Bible Explorer

Bincika › Jigogi › Naziri da wa’adinsa

Abubuwan ban mamaki

Naziri da wa’adinsa a cikin Littafi Mai Tsarki

Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (27), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.

A cikin Doka

  • Namiji ko mace yana iya yin wa’adi na musamman na NaziriƘid 6:2
    Ayoyin
    Ƙid 6:2“Yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘In mace, ko namiji yana so yă yi alkawari na musamman, alkawarin zaman keɓaɓɓe ga Ubangiji, a matsayin Banazare,
  • Ba ruwan inabi, abin sha mai sa maye, ruwan tsami, ruwan ’ya’yan inabi, inabi ko zabibiƘid 6:3
    Ayoyin
    Ƙid 6:3dole yă keɓe kansa daga ruwan inabi, ko daga waɗansu abubuwa sha masu sa maye, kada kuma yă sha ruwan tsamin da aka yi daga ruwan inabi, ko daga waɗansu abubuwa sha masu sa maye. Ba zai sha ruwan ’ya’yan inabi, ko yă ci ’ya’yan inabi ɗanye ko busasshe ba.
  • Ba kome daga kuringar inabi, ko ƙwayoyi ko ɓawo maƘid 6:4
    Ayoyin
    Ƙid 6:4Muddin yana Banazare, ba zai ci wani abin da ya fito daga ’ya’yan inabi ba, ko ƙwayar inabi, ko ɓawonsa ma.
  • Ba reza a kai: dole gashi ya yi tsawoƘid 6:5
    Ayoyin
    Ƙid 6:5“ ‘A dukan lokacin da yake a kan alkawarin keɓewarsa, reza ba zai taɓa kansa. Dole yă kasance da tsarki har ƙarshen keɓewarsa ga Ubangiji; tilas yă bar gashin kansa yă yi tsawo.
  • Ba kusantar gawa, ko ta mahaifi ko ta mahaifiya maƘid 6:6–7
    Ayoyin
    Ƙid 6:6–7A dukan kwanakin keɓewarsa ga Ubangiji, Banazarin ba zai yi kusa da gawa ba. Ko da ma gawar ta mahaifinsa ce, ko ta mahaifiyarsa, ko ta ɗan mahaifiyarsa, ko kuma ta ’yar’uwarsa ce, ba zai ƙazantar da kansa saboda su ba, domin alamar keɓewarsa ga Allah tana kansa.
  • In wani ya mutu farat ɗaya kusa da shi: ya aske kansa a rana ta bakwaiƘid 6:9
    Ayoyin
    Ƙid 6:9“ ‘In farat ɗaya wani ya mutu kusa da shi, to, keɓewarsa ta ƙazantu, dole yă aske kansa a ranar tsarkakewarsa, a rana ta bakwai.
  • A rana ta takwas: kurciyoyi biyu ko ’yan tattabarai biyuƘid 6:10
    Ayoyin
    Ƙid 6:10Sa’an nan a rana ta takwas, tilas yă kawo wa firist ’yan kurciyoyi biyu, ko kuma ’yan tattabarai biyu a bakin ƙofar Tentin Sujada.
  • Ba a ƙidaya kwanakin da suka wuce ba; wa’adin ya sāke farawaƘid 6:12
    Ayoyin
    Ƙid 6:12Dole yă keɓe kansa ga Ubangiji, har kwanakin keɓewarsa, kuma dole yă kawo ɗan rago bana ɗaya a matsayin hadayar laifi. Kwanakin baya ba sa cikin lissafi, domin ya ƙazantu a lokacin keɓewarsa.
  • A ƙarshe: ɗan rago namiji, ɗan rago mace, rago, da burodi marar yistiƘid 6:13–15
    Ayoyin
    Ƙid 6:13–15“ ‘To, ga doka saboda Banazare sa’ad da kwanakin keɓewarsa suka gama. Za a kawo shi a bakin ƙofar Tentin Sujada. A can zai miƙa hadayunsa ga Ubangiji. Hadayun kuwa su ne, ɗan rago, bana ɗaya marar lahani don hadaya ta ƙonawa, ’yar tunkiya, bana ɗaya marar lahani na hadaya don zunubi, rago marar lahani don hadaya ta salama, tare da hadayu na hatsi da hadayu na sha, da kuma kwando burodi marar yisti, ƙosai da aka yi da lallausan gari kwaɓaɓɓe da mai, da kuma wainan da aka barbaɗa da mai.
  • Naziri yakan aske kansa ya sa gashin a cikin wutaƘid 6:18
    Ayoyin
    Ƙid 6:18“ ‘Sa’an nan a ƙofar Tentin Sujada, dole Banazaren yă aske gashin da ya alamta keɓewarsa, yă kwashe gashin, yă zuba a cikin wutar da take ƙarƙashin hadaya ta salama.
  • Bayan haka, Naziri yana iya shan ruwan inabiƘid 6:20
    Ayoyin
    Ƙid 6:20Firist zai kaɗa su a gaban Ubangiji, hadaya ce ta kaɗawa; mai tsarki ne kuma, zai zama na firist, tare da ƙirjin da aka kaɗa da kuma cinyar da aka kawo. Bayan haka, Banazaren zai iya shan ruwan inabi.

Nazirawan da aka ambata sunansu

  • Kada mahaifiyar Samson ta sha ruwan inabi ko ta ci wani abu marar tsarkiMah 13:4, Mah 13:7, Mah 13:14
    Ayoyin
    Mah 13:4To, sai ki lura kada ki sha ruwan inabi ko wani abu mai sa maye, kada kuma ki ci wani abu marar tsarki,
    Mah 13:7Sai dai ya ce mini, ‘Za ki yi ciki, ki kuma haifi ɗa. To, fa, kada ki sha ruwan inabi ko abu mai sa maye kada kuma ki ci abin da yake marar tsarki, gama ɗan zai zama Banazare na Allah tun daga haihuwa har ranar mutuwarsa.’ ”
    Mah 13:14Kada tă ci kowane iri abin da ya fito daga inabi, ba kuwa za tă sha ruwan inabi, ko abu mai sa maye ko ta ci abu marar tsarki ba. Dole tă kiyaye duk abin da na umarce mata.”
  • Samson zai zama Naziri tun daga cikin mahaifiya; ba reza a kansaMah 13:5
    Ayoyin
    Mah 13:5gama za ki yi ciki, ki haifi ɗa. Aska ba za tă taɓa kansa ba, domin yaron zai zama Banazare, keɓaɓɓe ga Allah tun daga haihuwa, shi ne kuwa zai soma ceton Isra’ilawa daga hannuwan Filistiyawa.”
  • Samson: “Ba a taɓa sa reza a kaina ba”Mah 16:17
    Ayoyin
    Mah 16:17Saboda haka sai ya faɗa mata kome ya ce, “Ba a taɓa sa reza a kaina ba, domin ni Naziri ne keɓaɓɓe ga Allah tun haihuwa. In kuwa an aske kaina, ƙarfina zai rabu da ni, sai in zama kamar kowa.”
  • Delila ta sa aka aske gashin kansaMah 16:19
    Ayoyin
    Mah 16:19Bayan ta sa shi ya yi barci a cinyarta, sai ta kira wani ya zo ya aske kitso guda bakwai nan a kansa, aka fara rinjayensa. Ƙarfinsa kuwa ya rabu da shi.
  • Hannatu ta yi wa’adi cewa reza ba za ta taɓa kan ɗanta ba1Sam 1:11
    Ayoyin
    1Sam 1:11Ta yi ta cewa, “Ya Ubangiji Maɗaukaki. In har ka dubi baƙin cikin baiwarka, ka tuna da ni, ba ka kuma manta da baiwarka ba, amma ka ba ta ɗa, ni ma zan miƙa shi ga Ubangiji dukan rayuwarsa, aska kuwa ba za tă taɓa kansa ba.”
  • Kada Yohanna Mai Baftisma ya taɓa shan ruwan inabi ko abin sha mai sa mayeLuk 1:15, Luk 7:33
    Ayoyin
    Luk 1:15gama zai zama mai girma a gaban Ubangiji. Ba kuwa zai taɓa shan ruwan inabi ko wani abu mai sa maye ba. Zai cika da Ruhu Mai Tsarki tun haihuwa.
    Luk 7:33Gama Yohanna Mai Baftisma ya zo, ba ya cin burodi, ba ya shan ruwan inabi, sai kuka ce, ‘Ai, yana da aljani.’
  • Amos: an tā da Nazirawa daga samarinku, amma kuka sa su sha ruwan inabiAmos 2:11–12
    Ayoyin
    Amos 2:11–12“Na kuma tā da annabawa daga cikin ’ya’yanku maza waɗansu kuma su zama keɓaɓɓu daga cikin samarinku. Ba haka ba ne, mutanen Isra’ila?” In ji Ubangiji. “Amma kuka sa keɓaɓɓun suka sha ruwan inabi kuka kuma umarci annabawa kada su yi annabci.

Wa’adai a cikin Ayyukan Manzanni

  • Bulus ya aske kansa a Kenkireya saboda wa’adiAyy M 18:18
    Ayoyin
    Ayy M 18:18Bulus kuwa ya ci gaba da zama a Korint na ’yan kwanaki. Sa’an nan ya bar ’yan’uwa ya shiga jirgin ruwa zuwa Suriya tare da Firiskila da Akwila. Kafin ya tashi, ya aske kansa a Kenkireya saboda alkawarin da ya yi.
  • Bulus ya biya kuɗin mutum huɗu da suke ƙarƙashin wa’adi don su aske kawunansuAyy M 21:23–24, Ayy M 21:26
    Ayoyin
    Ayy M 21:23–24saboda haka, ka yi abin da muka faɗa maka. Akwai mutum huɗu tare da mu da suka yi alkawari. Ka ɗauki waɗannan mutane, ka tafi da su ku tsarkaka gaba ɗaya, ka kuma biya musu kome don su samu su yi aski. Ta haka kowa zai sani babu gaskiya a waɗannan rahotanni game da kai, za a kuma ga cewa kai kanka kana kiyaye dokar.
    Ayy M 21:26Kashegari, sai Bulus ya ɗauki mutanen ya kuma tsarkake kansa tare da su. Sa’an nan ya tafi haikali domin yă sanar da ranar cikar tsarkakewarsu da kuma ranar da za a ba da sadaka domin kowannensu.

Rekabawa

  • Rekabawa ba sa shan ruwan inabi, kamar yadda kakansu Yehonadab ya umartaIrm 35:6, Irm 35:14
    Ayoyin
    Irm 35:6Amma sai suka amsa suka ce, “Ba ma shan ruwan inabi, domin kakanmu Yehonadab ɗan Rekab ya umarce mu cewa, ‘Ko ku, ko zuriyarku kada ku sha ruwan inabi.
    Irm 35:14‘Yehonadab ɗan Rekab ya umarci ’ya’yansa maza kada su sha ruwan inabi sun kuma kiyaye wannan umarni. Har yă zuwa yau ba sa shan ruwan inabi, domin sun yi biyayya da umarnin kakansu. Amma na yi muku magana sau da sau, duk da haka ba ku yi biyayya ba.
  • Ba su gina gidaje ba, ba su yi shuka ba, suna kuma zama a tentunaIrm 35:7
    Ayoyin
    Irm 35:7Haka kuma ba za ku gina gidaje, ku dasa iri ko ku nome gonakin inabi ba; kada ku kasance da wani daga cikin waɗannan abubuwa, amma dole kullum ku zauna a tentuna. Ta haka za ku yi dogon rai a cikin ƙasar baƙuncinku.’

Tushe

Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.