Bible Explorer

Littafi Mai Tsarki › Zabura › 56

SRK · Babi 56 / 150

Zabura 56

1Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da murya “Kurciya a Itatuwan Oak Mai Nisa.” Ta Dawuda. Wani miktam. Sa’ad da Filistiyawa suka kama shi a birnin Gat. Ka yi mini jinƙai, ya Allah, gama mutane sun tasar mini da zafi; dukan yini suna matsa harinsu.

2Masu ɓata sunana suna bina dukan yini; da yawa suna kai mini hari cikin fariyarsu.

3Sa’ad da nake tsoro, zan dogara gare ka.

4Ga Allah wanda maganarsa nake yabo ga Allah na dogara; ba zan ji tsoro ba. Me mutum mai mutuwa zai yi mini?

5Dukan yini sun yi ta juya maganata; kullum suna ƙulle-ƙulle su cuce ni.

6Sun haɗa baki, sun ɓoye, suna kallon takawata suna a shirye su ɗauki raina.

7Sam, kada ka bari su kuɓuce; cikin fushinka, ya Allah, ka saukar da al’ummai.

8Ka lissafta makokina; ka jera hawayena a littafinka, ba a rubuce suke a cikin littafinka ba?

9Ta haka abokan gābana za su juya da baya sa’ad da na nemi taimako. Ta haka zan san cewa Allah yana tare da ni.

10Ga Allah, wanda nake yabon maganarsa, ga Ubangiji, wanda nake yabon maganarsa,

11ga Allah na dogara; ba zan ji tsoro ba. Me mutum zai iya yi mini?

12Ina ƙarƙashin alkawari gare ka, ya Allah; zan miƙa hadayuna na godiya gare ka.

13Gama ka cece ni daga mutuwa da kuma ƙafafun daga tuntuɓe, don in yi tafiya a gaban Allah cikin hasken rai.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (SRK, 2020) · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. (ba a canja rubutu ba; an bar bayanan ƙasa da kanun labarai) · eBible.org