Bible Explorer

Bincika › Jigogi › Furen bi-rana da ciyawa

Halitta

Furen bi-rana da ciyawa a cikin Littafi Mai Tsarki

Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (35), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.

Furen bi-rana

  • Kawunan ginshiƙan shirayin haikali suna da siffar furen bi-rana1Sar 7:19, 1Sar 7:22
    Ayoyin
    1Sar 7:19Dajiyoyin da suke a bisa ginshiƙan a shirayi suna da fasalin furen bi-rana, tsayinsu kamu huɗu-huɗu ne.
    1Sar 7:22Dajiyoyin da suke a bisa suna da fasalin bi-rana ne. Ta haka aka gama aiki a kan ginshiƙan.
  • Leɓen Tekun tagulla yana kamar bi-ranar da ta buɗe1Sar 7:26, 2Tar 4:5
    Ayoyin
    1Sar 7:26Kaurin kwanon ya kai tafin hannu, kuma da’iransa ya yi kamar da’iran kwaf, kamar bi-ranar da ta buɗe. Wannan kwanon da aka kira Teku yakan ci garwa dubu biyu.
    2Tar 4:5Kaurin ya kai tafin hannu, kuma da’iransa ya yi kama da’irar kwaf, kama furen da ya tohu. Ya riƙe randuna dubu uku.
  • “Ku dubi yadda furannin jeji suke girma mana. Ba sa aiki ko saƙa”Mat 6:28, Luk 12:27
    Ayoyin
    Mat 6:28“Me ya sa kuke damuwa a kan riguna? Ku dubi yadda furannin jeji suke girma mana. Ba sa aiki ko saƙa.
    Luk 12:27“Ku dubi yadda furanni suke girma. Ba sukan yi aiki, ko saƙa ba, duk da haka, ina faɗa muku cewa, ko Solomon cikin kyakkyawan darajarsa duka, bai yafa kayan ado da ya kai kamar na ko ɗaya a cikinsu ba.
  • Ko Solomon cikin dukan darajarsa bai yi ado kamar ɗayansu baMat 6:29
    Ayoyin
    Mat 6:29Duk da haka ina gaya muku ko Solomon cikin dukan darajarsa bai sa kayan adon da ya kai na ko ɗaya a cikinsu ba.
  • Makiyayi yakan yi kiwon garkensa a cikin furannin bi-ranaWW 2:16, WW 6:3
    Ayoyin
    WW 2:16Ƙaunataccena nawa ne ni kuma tasa ce; yana kiwon garkensa a cikin furannin bi-rana.
    WW 6:3Ni na ƙaunataccena ce, ƙaunataccena kuma nawa ne; yana kiwo a cikin furen bi-rana.
  • Ƙaunataccen ya gangara zuwa lambunsa don ya tattara furannin bi-ranaWW 6:2
    Ayoyin
    WW 6:2Ƙaunataccena ya gangara zuwa lambunsa, zuwa inda fangulan kayan yaji suke, don yă yi kiwo a cikin lambun don kuma yă tattara furen bi-rana.
  • “furen bi-rana na kwari … Kamar furen bi-rana a cikin ƙayayyuwa”WW 2:1–2
    Ayoyin
    WW 2:1–2Ni furen bi-rana ne na Sharon, furen bi-rana na kwari. Kamar furen bi-rana a cikin ƙayayyuwa haka ƙaunatacciyata take a cikin ’yan mata.
  • “Leɓunansa sun yi kamar furen bi-rana suna ɗiga da mur”WW 5:13
    Ayoyin
    WW 5:13Kumatunsa kamar lambun kayan yaji suna ba da turare. Leɓunansa sun yi kamar furen bi-rana suna ɗiga da mur.
  • Tagwayen ’yan bareyi suna kiwo a cikin furannin bi-ranaWW 4:5
    Ayoyin
    WW 4:5Nonanki biyu sun yi kamar bareyi biyu, kamar tagwayen barewa da suke kiwo a cikin furen bi-rana.

Ciyawa

  • Ciyawa takan yi girma domin dabbobi da kuma a kan tuddaiZab 104:14, Zab 147:8, M Sh 11:15
    Ayoyin
    Zab 104:14Yana sa ciyawa tă yi girma saboda shanu, tsire-tsire domin mutum ya nome, suna fid da abinci daga ƙasa,
    Zab 147:8Ya rufe sararin sama da gizagizai; yana tanada wa duniya ruwan sama yana kuma sa ciyawa tă yi girma a kan tuddai.
    M Sh 11:15Zan tanadar da ciyawa a filaye don shanunku, za ku ci, ku kuma ƙoshi.
  • Ruwan sama a kan ciyawar da aka yankaZab 72:6
    Ayoyin
    Zab 72:6Zai zama kamar ruwan sama mai fāɗuwa a filin ciyayin da aka yanka, kamar yayyafi mai ba wa duniya ruwa.
  • Ciyawa a kan rufin gidaje takan yi yaushi kafin ta yi girmaZab 129:6–7, 2Sar 19:26
    Ayoyin
    Zab 129:6–7Bari su zama kamar ciyawa a kan rufi, wadda takan bushe kafin tă yi girma; da ita mai girbi ba ya iya cika hannuwansa, balle wanda yake tarawa yă cika hannuwansa.
    2Sar 19:26Ƙarfin mutanensu ya tsiyaye, suka razana aka kuma kunyata su. Suna kama da tsirai a gona, kamar sabon toho kamar ciyawa mai tohuwa bisa rufin ɗaki wanda ya bushe saboda zafi, kafin yă yi girma.
  • Ciyawar jeji: tana nan yau, gobe a jefa ta cikin wutaMat 6:30, Luk 12:28
    Ayoyin
    Mat 6:30In haka Allah yake yi wa ciyawar jeji sutura, wadda yau tana nan, gobe kuwa a jefa a cikin wuta, ba zai ma fi yi muku sutura ba, ya ku masu ƙarancin bangaskiya?
    Luk 12:28In haka ne Allah yake yi wa ciyayin jeji sutura, wadda yau suna nan, sa’an nan gobe kuma a jefa cikin wuta, Allah ba zai yi muku sutura fiye da ciyayin jeji ba, ya ku masu ƙarancin bangaskiya!
  • Sa’ad da aka kwashe ciyawa, sabon tsiro yakan bayyanaK Mag 27:25
    Ayoyin
    K Mag 27:25Sa’ad da aka yanki ingirci sabon toho kuma ya bayyana aka kuma tattara ciyawa daga tuddai,
  • Zafin rana yakan bushe tsiro, furensa kuma ya kakkaɓeYaƙ 1:11
    Ayoyin
    Yaƙ 1:11Gama in rana ta fito ta yi zafi mai tsanani sai ta sa tsiro yă yanƙwane tsiro; furensa yă kakkaɓe, kyansa kuma yă lalace. Haka ma mai arziki zai shuɗe yayinda yake cikin harkarsa.
  • Lokacin fari Ahab ya bincika kowace maɓuɓɓuga da kwari don ciyawa domin dawakai1Sar 18:5
    Ayoyin
    1Sar 18:5Ahab ya ce wa Obadiya, “Ka ratsa ƙasar zuwa dukan maɓulɓulai da fadamu. Mai yiwuwa ka sami ciyawa mu ba dawakai da alfadarai don su rayu, don kada mu kashe dabbobinmu.”
  • Ruwan Nimrim ya ƙafe ciyawa kuma ta yi yaushiIsh 15:6
    Ayoyin
    Ish 15:6Ruwayen Nimrim sun ƙafe ciyayin kuma sun bushe; tsire-tsire duk sun ɓace babu sauran ɗanyen abu.
  • Dorina takan ci ciyawa kamar saAyu 40:15
    Ayoyin
    Ayu 40:15“Dubi dorina, wadda na halicce ku tare kuma ciyawa take ci kamar sa.
  • Nebukadnezzar ya ci ciyawa kamar saDan 4:33
    Ayoyin
    Dan 4:33Nan da nan abin da aka faɗa a kan Nebukadnezzar tabbatarsa ya cika. Aka kore shi daga cikin mutane ya kuma shiga cin ciyawa kamar shanu. Jikinsa ya jiƙe da raɓa, har gashinsa ya yi tsawo kamar fikafikan gaggafa, kumbarsa kuma suka yi tsawo kamar na tsuntsu.
  • “Jaki yakan yi kuka sa’ad da ya sami ciyawar ci”Ayu 6:5
    Ayoyin
    Ayu 6:5Jaki yakan yi kuka sa’ad da ya sami ciyawar ci, ko saniya takan yi kuka in ta sami abincinta?
  • Mutum dubu biyar sun zauna a kan ɗanyar ciyawaYoh 6:10, Mar 6:39
    Ayoyin
    Yoh 6:10Yesu ya ce, “Ku sa mutanen su zauna.” Wurin kuwa akwai ciyawa da sosai, sai maza suka zazzauna, sun kai wajen dubu biyar.
    Mar 6:39Sa’an nan Yesu ya umarce su su sa dukan mutanen su zazzauna ƙungiya-ƙungiya a kan ɗanyar ciyawa.

Maganganu

  • “Dukan mutane kamar ciyawa suke … ciyawa takan yanƙwane furannin kuma su kakkaɓe”Ish 40:6–8, 1Bit 1:24
    Ayoyin
    Ish 40:6–8Muryar tana cewa, “Ka yi shela.” Na kuwa ce, “Me zan yi shelar?” “Dukan mutane kamar ciyawa suke, kuma dukan ɗaukakarsu kamar furannin jeji ne. Ciyawa takan yanƙwane, furanni kuma su yi yaushi, domin Ubangiji ya hura iska a kansu. Tabbatacce mutane ciyawa ne. Hakika ciyawa takan yanƙwane, furanni kuma su yi yaushi, amma maganar Allahnmu tana nan daram har abada.”
    1Bit 1:24Gama, “Dukan mutane kamar ciyawa suke, darajarsu kuma kamar furannin jeji ne; ciyawa takan yanƙwane furannin kuma su kakkaɓe,
  • Sabuwar ciyawa takan toho da safe ta yi yaushi da yammaZab 90:5–6
    Ayoyin
    Zab 90:5–6Ka share mutane cikin barcin mutuwa; suna kama da sabuwa ciyawar safiya, ko da yake da safe takan yi sabuwar huda da yamma sai ta bushe ta kuma yanƙwane.
  • Kwanakin mutum kamar ciyawa ne; iska takan wuce sai ta ɓaceZab 103:15–16
    Ayoyin
    Zab 103:15–16Game da mutum dai, kwanakinsa suna kamar ciyawa da suke haɓaka kamar fure a gona; iska kan hura a kansa sai ya ɓace ba a kuwa sāke tuna da inda dā yake.
  • Magana mai sauka kamar raɓa, kamar ruwan sama a hankali a kan sabuwar ciyawaM Sh 32:2
    Ayoyin
    M Sh 32:2Bari koyarwata tă zubo kamar ruwan sama kalmomina kuma su sauko kamar raɓa, kamar yayyafi a kan sabuwar ciyawa, kamar ruwan sama mai yawa a kan tsirai marasa ƙarfi.

Tushe

Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.