Bible Explorer

Bincika › Jigogi › Raɓar safiya

Halitta

Raɓar safiya a cikin Littafi Mai Tsarki

Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (22), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.

  • Raɓa takan sauka a kan sansani da dare, manna kuma tare da itaƘid 11:9
    Ayoyin
    Ƙid 11:9Sa’ad da raɓa tana saukowa da dad dare a kan sansani, Manna ma takan sauko.
  • Sa’ad da raɓar safiya ta ɗauke, ’yan ƙananan ɓawo sun kwanta a ƙasaFit 16:13–14
    Ayoyin
    Fit 16:13–14Da yamman wannan rana, sai makware suka rufe dukan sansani, da safe kuma sai ga raɓa ta kewaye sansani. Lokacin da raɓar ta watse, sai ga wani abu kamar tsaki, falle-falle kuma da laushi, fari, kamar hazo, a ƙasa.
  • Raɓa takan kwanta a kan rassa dukan dareAyu 29:19
    Ayoyin
    Ayu 29:19Jijiyoyina za su kai cikin ruwa, kuma raɓa za tă kwanta a rassana dukan dare.
  • Gizagizai sun ɗiga raɓaK Mag 3:20
    Ayoyin
    K Mag 3:20ta wurin sani aka rarraba zurfafa, gizagizai kuma suka zubo raɓa.
  • “Wa ya zama mahaifin raɓa?”Ayu 38:28
    Ayoyin
    Ayu 38:28Ruwan sama yana da mahaifi? Wa ya zama mahaifin raɓa?
  • Ƙaunataccen da dare: “Kaina ya jiƙe da raɓa”WW 5:2
    Ayoyin
    WW 5:2Na yi barci amma zuciyata tana a farke. Ku saurara! Ƙaunataccena yana ƙwanƙwasa ƙofa. “Buɗe mini, ’yar’uwata, ƙaunatacciyata, kurciyata, marar laifina. Kaina ya jiƙe da raɓa, gashina ya yi danshin ɗiɗɗigar dare.”
  • Raɓar sama ta jiƙa NebukadnezzarDan 4:33
    Ayoyin
    Dan 4:33Nan da nan abin da aka faɗa a kan Nebukadnezzar tabbatarsa ya cika. Aka kore shi daga cikin mutane ya kuma shiga cin ciyawa kamar shanu. Jikinsa ya jiƙe da raɓa, har gashinsa ya yi tsawo kamar fikafikan gaggafa, kumbarsa kuma suka yi tsawo kamar na tsuntsu.
  • Raɓar Hermon tana sauka a kan duwatsun SihiyonaZab 133:3
    Ayoyin
    Zab 133:3Yana kamar raɓar Hermon da take zubowa a kan Dutsen Sihiyona. Gama a can Ubangiji ya tabbatar da albarkarsa, har ma rai na har abada.

A cikin labarai

  • Gideyon ya matse kwano cike da ruwa daga ulunMah 6:37–38
    Ayoyin
    Mah 6:37–38to, zan shimfiɗa ulu a masussuka, inda safe akwai raɓa a kan ulun kaɗai, ƙasa kuwa a bushe, to, zan san cewa za ka ceci Isra’ila ta hannuna, yadda ka ce.” Abin da faru ke nan. Gideyon ya tashi da sassafe kashegari, ya matse ulun ya kakkaɓe raɓar, ruwan ya cika ƙwarya.
  • Kashegari ulun ya bushe raɓa kuma ta rufe ƙasaMah 6:39–40
    Ayoyin
    Mah 6:39–40Sa’an nan Gideyon ya ce wa Allah, “Kada ka yi fushi da ni. Bari in ƙara yin wani gwaji kuma da ulun. A wannan lokaci ka sa ulun yă bushe, ƙasar kuma ta rufu da raɓa.” A wannan dare Allah ya yi haka. Ulun ne kaɗai yake a bushe, amma dukan ƙasar ta jiƙe da raɓa.
  • Iliya ga Ahab: ba raɓa ko ruwan sama a waɗannan shekaru1Sar 17:1
    Ayoyin
    1Sar 17:1To, Iliya mutumin Tishbe, daga Tishbe a Gileyad, ya ce wa Ahab, “Muddin Ubangiji, Allah na Isra’ila wanda nake bauta wa yana a raye, ba za a yi raɓa ko ruwan sama a ’yan shekaru masu zuwa ba, sai ko na faɗa haka.”
  • Makokin Dawuda: “Ya duwatsun Gilbowa, kada a sāke yin ruwa ko raɓa a kanku”2Sam 1:21
    Ayoyin
    2Sam 1:21“Ya duwatsun Gilbowa, kada a sāke yin ruwa ko raɓa a kanku, balle gonakin da suke ba da hatsin hadaya su ƙara bayarwa. Gama a can ne garkuwoyin manyan sojoji suka kwanta, suka kwanta a wulaƙance. Garkuwar Shawulu kuwa, ba za a ƙara shafa mata mai ba.
  • Haggai: sammai sun ƙi saukar da raɓa, ƙasa kuma ta ƙi ba da amfaniHag 1:10
    Ayoyin
    Hag 1:10Shi ya sa, saboda ku sammai sun ƙi saukar da raɓa, ƙasa kuma ta ƙi ba da amfani.

Albarka

  • Albarkar Ishaku: raɓar sama da wadatar ƙasaFar 27:28
    Ayoyin
    Far 27:28Allah yă ba ka daga raɓar sama da kuma yalwar ƙasa, yalwar hatsi da sabon ruwan inabi.
  • Isuwa zai zauna nesa da raɓar samaFar 27:39
    Ayoyin
    Far 27:39Mahaifinsa Ishaku ya amsa masa ya ce, “Ga shi, ni’imar ƙasar za tă nisanci mazauninka. Raɓar samaniya can ƙwanƙoli za tă nisance ka.
  • Musa: ƙasar Yusuf ta sami albarkar raɓa mai daraja daga samaM Sh 33:13
    Ayoyin
    M Sh 33:13Game da Yusuf ya ce, “Bari Ubangiji yă albarkaci ƙasarsa da raɓa mai daraja daga sama a bisa da kuma zurfin ruwan da suke kwance a ƙarƙashi;
  • Ƙasar hatsi da sabon ruwan inabi, inda sammai suke ɗiga raɓaM Sh 33:28
    Ayoyin
    M Sh 33:28Haka Isra’ila zai zauna lafiya shi kaɗai; zuriyar Yaƙub a tsare a ƙasar hatsi da sabon ruwan inabi, inda sammai za su zuba raɓa.

Maganganu

  • “kamar raɓar safen da yakan kakkaɓe”Hos 6:4, Hos 13:3
    Ayoyin
    Hos 6:4“Me zan yi da kai Efraim? Me zan yi da kai Yahuda? Ƙaunarku tana kamar hazon safiya, kamar raɓar safiya da takan ɓace.
    Hos 13:3Saboda haka za su zama kamar hazon safiya, kamar raɓar safen da yakan kakkaɓe, kamar ƙaiƙayin da ake tankaɗe daga masussuka, kamar hayaƙin da yake fita daga taga.
  • Tagomashin sarki “yana kama da raba a kan ciyawa”K Mag 19:12
    Ayoyin
    K Mag 19:12Fushin sarki yana kama da rurin zaki, amma tagomashinsa yana kama da raba a kan ciyawa.
  • “za mu fāɗa masa kamar yadda raɓa takan fāɗo a bisa ƙasa”2Sam 17:12
    Ayoyin
    2Sam 17:12Sa’an nan za mu fāɗa masa duk inda yake, za mu fāɗa masa kamar yadda raɓa takan fāɗo a bisa ƙasa. Da shi da mutanensa babu ko ɗaya da za a bari da rai.
  • “kamar girgijen raba a lokacin girbi”Ish 18:4
    Ayoyin
    Ish 18:4Ga abin da Ubangiji ya faɗa mini, “Zan yi shiru in kuma duba a hankali daga mazaunina, kamar ƙuna mai zafi a hasken rana, kamar girgijen raba a lokacin girbi.”

Tushe

Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.