Bible Explorer

Bincika › Jigogi › Al’ul na Lebanon

Halitta

Al’ul na Lebanon a cikin Littafi Mai Tsarki

Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (32), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.

  • Solomon ya yi magana a kan itatuwa, daga al’ul na Lebanon zuwa hizzob da yake girma a bango1Sar 4:33
    Ayoyin
    1Sar 4:33Ya yi magana a kan rayuwar itatuwa, daga al’ul na Lebanon zuwa hizzob da yake girma a bangaye. Ya kuma yi koyarwa game da dabbobi, da tsuntsaye, da abubuwa masu rarrafe, da kuma kifi.
  • Zabura: itatuwan al’ul na Lebanon sun ƙoshiZab 104:16
    Ayoyin
    Zab 104:16Ana yi wa itatuwan Ubangiji banruwa sosai, al’ul na Lebanon da ya shuka.
  • A zamanin Solomon al’ul yana da yawa kamar itatuwan jumaiza a gindin tuddai1Sar 10:27, 2Tar 1:15
    Ayoyin
    1Sar 10:27Sarki ya mai da azurfa barkatai a cikin Urushalima kamar duwatsu, al’ul kuma da yawa kamar itatuwan fir na jumaiza a gindin tuddai.
    2Tar 1:15Sarki ya sa azurfa da zinariya suka zama barkatai a Urushalima kamar duwatsu, al’ul kuma kamar itatuwan fir a gindin tsaunuka.
  • Mutane za su maye gurbin itatuwan jumaiza da aka sare da al’ulIsh 9:10
    Ayoyin
    Ish 9:10“Tubalai sun zube a ƙasa, amma za mu sāke gina su da dutse; an sassare itatuwan ɓaure, amma za mu maya su da al’ul.”
  • Al’ul daga Lebanon ya zama jigon jirgin ruwa domin TayaEzk 27:5
    Ayoyin
    Ezk 27:5Sun yi dukan katakanki daga itatuwan fir daga Senir; sun kwaso itatuwan al’ul daga Lebanon don su yi miki jigon jirgin ruwa.
  • An yi amfani da itacen al’ul, hizzob da jan zare a ayyukan tsabtacewaFir 14:4, Ƙid 19:6
    Ayoyin
    Fir 14:4firist zai umarta a kawo tsuntsaye biyu masu rai, masu tsabta da itacen al’ul, jan ƙyalle da kuma hizzob saboda mutumin da za a tsabtacce.
    Ƙid 19:6Firist zai ɗauki itacen al’ul, da hizzob, da jan ulu, yă jefa su a kan karsanar da ake ƙonewa.

Gini da al’ul

  • Hiram na Taya ya aika wa Dawuda gungumen al’ul, masassaƙa da masu fasa duwatsu domin fādarsa2Sam 5:11
    Ayoyin
    2Sam 5:11To, Hiram sarkin Taya ya aiki manzanni wurin Dawuda tare da gumaguman itacen al’ul, da kafintoci, da kuma maginan duwatsu, suka kuwa gina wa Dawuda fada.
  • Dawuda: “ina zama a fadar da aka yi da al’ul, yayinda akwatin alkawarin Ubangiji yana a ƙarƙashin tenti”1Tar 17:1
    Ayoyin
    1Tar 17:1Bayan Dawuda ya zauna a fadansa, sai ya ce wa annabi Natan, “Ga ni, ina zama a fadar da aka yi da al’ul, yayinda akwatin alkawarin Ubangiji yana a ƙarƙashin tenti.”
  • Solomon ya roƙi Hiram al’ul; ba wanda ya iya saran itace kamar Sidoniyawa1Sar 5:6
    Ayoyin
    1Sar 5:6“Don haka, ka ba da umarni a yanka mini itatuwan al’ul na ƙasar Lebanon. Ma’aikatana za su haɗa hannu da ma’aikatanka, ni kuwa zan biya ka albashin ma’aikatanka kamar yadda ka faɗa. Gama ka san cewa babu wani a cikinmu da ya iya yanka itacen katako kamar Sidoniyawa.”
  • An jawo gungumen zuwa teku aka kuma ɗaure su suka yi iyo a kan ruwa1Sar 5:8–9, 2Tar 2:16
    Ayoyin
    1Sar 5:8–9Sai Hiram ya aike wa Solomon da kalmomin nan, “Na sami saƙon da ka aika mini, zan kuma yi duk abin da kake so ta wurin tanada katakan al’ul da na fir. Ma’aikatana za su gangara da su daga Lebanon zuwa bakin teku. Zan sa a ɗaɗɗaura su su bi ruwan teku daga Lebanon zuwa bakin Bahar Rum da za ka nuna mini. A can zan kunce maka su, sa’an nan ka kwashe. Kai kuma za ka biya bukatata ta wurin tanadin abinci wa gidana.”
    2Tar 2:16za mu kuwa yanka dukan gumagumai daga Lebanon da kake bukata za mu kuwa yi fitonsu ta teku, su gangara zuwa Yaffa. Za ka iya kwashe su daga can ka haura zuwa Urushalima.”
  • An biya masu saran itace na Hiram da alkama, sha’ir, ruwan inabi da man zaitun2Tar 2:10
    Ayoyin
    2Tar 2:10Zan ba wa bayinka masu yankan katakai waɗanda suka yanka katako, garwa niƙaƙƙen alkama dubu ashirin, garwan sha’ir dubu ashirin da randunan ruwan inabi dubu ashirin da kuma randunan man zaitun dubu ashirin.”
  • Isra’ilawa 30,000 sun yi aiki a Lebanon bi da bi, 10,000 kowane wata1Sar 5:13–14
    Ayoyin
    1Sar 5:13–14Sarki Solomon ya ɗebi ma’aikata daga dukan Isra’ila, su dubu talatin. Ya riƙa aika su dubu goma-goma zuwa Lebanon kowane wata, saboda su yi wata ɗaya a Lebanon, watanni biyu kuma a gida. Adoniram ne ya lura da aikin gandun.
  • Solomon ya ba Hiram garuruwa ashirin a Galili saboda al’ul da fir1Sar 9:11
    Ayoyin
    1Sar 9:11sai Sarki Solomon ya ba wa Hiram sarkin Taya garuruwa ashirin a yankin Galili, gama Hiram ya tanada masa da dukan katakai al’ul da na fir, da kuma zinariyar da ya bukaci domin aiki.
  • An rufe haikali da katakan al’ul da alluna1Sar 6:9–10
    Ayoyin
    1Sar 6:9–10A haka ya gina haikalin ya kuma gama shi, ya jinƙe shi da manyan katakai da kuma katakan al’ul. Ya kuma gina ɗakunan gefe duka a gefen haikalin. Tsayin kowanne, kamu biyar ne, aka haɗa su da haikalin da manyan katakan al’ul.
  • A ciki, al’ul da aka sassaƙa da siffar gora da furanni; ba a ga ko dutse ɗaya ba1Sar 6:15, 1Sar 6:18
    Ayoyin
    1Sar 6:15Ya rufe bangon ciki da katakan itacen al’ul tun daga ƙasa har zuwa sama, ya kuma rufe daɓen da katakan itacen fir.
    1Sar 6:18An yi wa katakan itacen al’ul na cikin haikalin zāne mai fasalin gora da na buɗaɗɗun furanni. An rufe bangon ciki duka da itacen al’ul, har ba a ganin duwatsun ginin.
  • Fili na ciki: jeri uku na sassaƙaƙƙun duwatsu da jeri ɗaya na katakan al’ul1Sar 6:36
    Ayoyin
    1Sar 6:36Ya kuma gina filin ciki da sassaƙaƙƙun duwatsu, jeri uku, da jeri ɗaya na katakan itacen al’ul.
  • Fādar Kurmin Lebanon tana tsaye a kan jeri huɗu na ginshiƙan al’ul1Sar 7:2–3
    Ayoyin
    1Sar 7:2–3Ya gina fadarsa mai suna Kurmin Lebanon, tsawonsa kamu ɗari, fāɗinsa kamu hamsin, tsayinsa kuma kamu talatin, a bisa jeri huɗu na ginshiƙan itacen al’ul, aka shimfiɗa katakan itacen al’ul a bisa ginshiƙan. Aka yi rufin da al’ul bisa ginshiƙan da suke bisa ginshiƙai arba’in da biyar, goma sha biya a kowane jeri.
  • Waɗanda suka dawo daga bauta sun yi jigilar gungumen al’ul daga Lebanon zuwa YoffaEzr 3:7
    Ayoyin
    Ezr 3:7Sai suka ba wa magina da kafintoci kuɗi, suka ba wa mutanen Sidon da na Taya abinci, da abin sha, da mai, don su kawo itatuwan al’ul a Yaffa daga Lebanon ta teku, yadda Sairus sarkin Farisa ya ba da umarni.
  • Wani sarki ya yi wa fādarsa jerin al’ul ya kuma shafe ta da jan fentiIrm 22:14
    Ayoyin
    Irm 22:14Yana cewa, ‘Zan gina wa kaina babban fada da manyan ɗakuna.’ Ta haka sai ya yi musu manyan tagogi ya manne musu al’ul ya yi musu ado kuma da ruwan ja.
  • “Al’ul su ne ginshiƙan gidanmu”WW 1:17
    Ayoyin
    WW 1:17Al’ul su ne ginshiƙan gidanmu; fir su ne katakan rufin gidanmu.

Maganganu da tatsuniyoyi

  • Tatsuniyar Yehowash: sarƙaƙiya ta nemi ’yar itacen al’ul aure2Sar 14:9
    Ayoyin
    2Sar 14:9Amma Yehowash sarkin Isra’ila ya mai da martani wa Amaziya sarkin Yahuda ya ce, “Wata ’yar ƙaya a kurmin Lebanon ta aika da saƙo wurin itacen al’ul a Lebanon cewa, ‘Ka ba ɗana ’yarka aure.’ Amma wani naman jeji ya zo ya tattake ƙayar.
  • Tatsuniyar Yotam: wuta daga ƙaya ta cinye itatuwan al’ulMah 9:15
    Ayoyin
    Mah 9:15“Itacen ƙaya ya ce wa itatuwan, ‘In da gaske ne kuke so ku naɗa ni sarkinku, ku zo ku sha inuwana; in ba haka ba, bari wuta ta fito daga itacen ƙaya ta cinye itacen al’ul na Lebanon!’
  • Ba’amore, mai tsayi kamar al’ul da ƙarfi kamar oakAmos 2:9
    Ayoyin
    Amos 2:9“Na hallaka mutumin Amoriyawa a gabansu, ko da yake ya yi dogo kamar itacen al’ul kuma mai ƙarfi kamar itacen oak. Na hallaka ’ya’yan itatuwansa daga sama, da kuma jijiyoyinsa daga ƙasa.
  • Zabura: “za su yi girma kama al’ul na Lebanon”Zab 92:12
    Ayoyin
    Zab 92:12Adalai za su haɓaka kamar itacen dabino, za su yi girma kama al’ul na Lebanon;
  • “Muryar Ubangiji ta kakkarya itatuwan al’ul”Zab 29:5
    Ayoyin
    Zab 29:5Muryar Ubangiji ta kakkarya itatuwan al’ul na Lebanon. Ubangiji ya kakkarya itatuwan al’ul na Lebanon kucu-kucu.
  • “mafi kyau kamar itacen al’ul”WW 5:15
    Ayoyin
    WW 5:15Ƙafafunsa sun yi kamar ginshiƙan dutsen alabastar da aka kafa su a cikin rammukar zinariya. Kamanninsa ya yi kamar Lebanon, mafi kyau kamar itacen al’ul nasa.
  • Itatuwan al’ul suna murna: “babu wani mai yankan katakon da ya zo yă yanka mu”Ish 14:8
    Ayoyin
    Ish 14:8Har itatuwan fir ma da kuma al’ul na Lebanon suna murna a kanka suna cewa, “Yanzu da aka ƙasƙantar da kai, babu wani mai yankan katakon da ya zo yă yanka mu.”
  • “Yi kuka, ya itacen fir, gama itacen al’ul ya fāɗi”Zak 11:2
    Ayoyin
    Zak 11:2Yi kuka, ya itacen fir, gama itacen al’ul ya fāɗi; itatuwa masu daraja sun lalace! Ku yi kuka, ku itatuwan oak na Bashan; an sassare itatuwan babban kurmi!

Tushe

Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.