Bible Explorer

Bincika › Jigogi › Dawakai

Halitta

Dawakai a cikin Littafi Mai Tsarki

Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (37), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.

  • Ayuba: doki yakan tone ƙasa a kwari, ya yi farin ciki da ƙarfinsa, ya kutsa cikin yaƙiAyu 39:19–21
    Ayoyin
    Ayu 39:19–21“Ko kai ne kake ba doki ƙarfinsa kai kake rufe wuyansa da geza mai yawa? Ko kai kake sa shi yă yi tsalle kamar fāra, ba ya jin tsoro sai dai a ji tsoronsa. Yana takawa da ƙarfi yana jin daɗin ƙarfinsa yana shiga filin yaƙi gabagadi.
  • Yakan yi wa tsoro dariya ba ya kuma juya baya daga takobiAyu 39:22–23
    Ayoyin
    Ayu 39:22–23Yana yi wa tsoro dariya ba ya jin tsoron kome; ba ya guje wa takobi. Kwari a baka yana lilo a gabansa kibiya da māshi suna wuce kansa.
  • Da busar ƙaho ba ya iya tsayawa wuri ɗaya; yakan ji ƙanshin yaƙiAyu 39:24–25
    Ayoyin
    Ayu 39:24–25Yana kartar ƙasa da ƙarfi; ba ya iya tsayawa tsab sa’ad da ya ji busar ƙaho. Da jin ƙarar ƙaho sai ya ce, ‘Yauwa!’ Ya ji ƙanshin yaƙi daga nesa, da ihun shugabannin yaƙi.
  • Ana jin fyuɗewa da haniniyar dawakan yaƙi daga nesaIrm 8:16
    Ayoyin
    Irm 8:16Daga Dan ana jin tirjin dawakan abokin gāba; da jin haniniyar ingarmunsu dukan ƙasar ta girgiza. Sun zo su cinye ƙasar da kome da yake cikinta, birni da dukan mazaunanta.
  • Linzami a bakinsu yakan sa mahayi ya juya dukan dabbarYaƙ 3:3
    Ayoyin
    Yaƙ 3:3Sa’ad da muka sa linzamai a bakunan dawakai don mu sa su yi mana biyayya, mukan iya bin da dabbar gaba ɗaya.
  • Dole a riƙe dawakai da alfadarai da linzami da ragamaZab 32:9
    Ayoyin
    Zab 32:9Kada ka zama kamar doki ko doki, wanda ba su da azanci wanda dole sai an bi da su da linzami da ragama in ba haka ba, ba za su zo wurinka ba.
  • Ana kawo sha’ir da ciyawa domin dawakan kekunan yaƙi1Sar 4:28
    Ayoyin
    1Sar 4:28Kowa a cikinsu, bisa ga lokacin da aka ba shi, yakan kai hatsin sha’ir da ciyawa domin dawakan-kekunan yaƙi, da sauran dawakai a inda aka ajiye su.
  • Ƙafafun amalanke da dawakai sukan bi kan hatsi ba tare da sun murƙushe shi baIsh 28:28
    Ayoyin
    Ish 28:28Dole a niƙa hatsi don a yi burodi; saboda haka mutum ba zai yi ta bugun alkama, har yă ɓata tsabar ba. Ya san yadda zai sussuke alkamarsa, ba tare da ya ɓata tsabarta ba.

A cikin yaƙi

  • Dawakai da kekunan yaƙin Fir’auna sun fafari Isra’ila har zuwa tekuFit 14:9, Fit 15:19
    Ayoyin
    Fit 14:9Masarawa, dukan dawakan Fir’auna da kekunan yaƙi da mahaya da sojoji, suka bi Isra’ilawa suka cin musu yayinda suke a sansani kusa da teku kurkusa da Fi Hahirot, wanda ya fuskanci Ba’al-Zafon.
    Fit 15:19Sa’ad da dawakai, kekunan yaƙi da mahayan dawakan Fir’auna suka shiga cikin teku, Ubangiji ya mayar da ruwan teku a kansu, amma Isra’ilawa suka wuce a cikin teku a busasshiyar ƙasa.
  • Yoshuwa ya yanke agaran dawakan abokan gāba ya kuma ƙone kekunan yaƙinsuYosh 11:6, Yosh 11:9
    Ayoyin
    Yosh 11:6Ubangiji ya ce wa Yoshuwa, “Kada ka ji tsoronsu, domin war haka gobe zan ba da dukansu a hannun Isra’ilawa, za su kuwa karkashe su. Za ku gurgunta dawakansu, ku kuma ƙone keken yaƙinsu.”
    Yosh 11:9Yoshuwa ya yi musu yadda Ubangiji ya umarta, ya gurgunta dawakansu, ya kuma ƙone keken yaƙinsu.
  • Dawuda ya yanke agaran dukan dawakan kekunan yaƙi sai ɗari kaɗai2Sam 8:4
    Ayoyin
    2Sam 8:4Dawuda ya kame keken yaƙinsa guda dubu, mahayan keken yaƙinsa dubu bakwai, da sojojin ƙasa dubu ashirin. Ya yayyanke agaran dawakan duka amma ya bar dawakai kekunan yaƙi ɗari.
  • Sarki Yehoshafat ga Ahab: “dawakaina kamar dawakanka”1Sar 22:4
    Ayoyin
    1Sar 22:4Saboda haka ya tambayi Yehoshafat, ya ce, “Za ka tafi tare da ni don in yi yaƙi da Ramot Gileyad?” Yehoshafat ya amsa wa sarkin Isra’ila, ya ce, “Ni ma kamar ka ne, mutanena kuwa kamar mutanenka, dawakaina kamar dawakanka.”
  • Ba’ar Assuriyawa: dawakai dubu biyu, in za ka sami mahayansu2Sar 18:23
    Ayoyin
    2Sar 18:23“ ‘Yanzu, ka zo ku shirya da shugabana, sarkin Assuriya. Zan ba ka dawakai dubu biyu, in za ka sami mahayansu!
  • ’Yan leƙen asiri a Samariya sun ɗauki kekunan yaƙi biyu da dawakai don su bi Arameyawa2Sar 7:13–14
    Ayoyin
    2Sar 7:13–14Ɗaya daga cikin fadawan sarki ya ce, “A sa waɗansu mutane su ɗauki dawakai biyar da suka ragu cikin birni, idan ba su tsira ba, za su zama kamar sauran Isra’ilawan da suka riga suka mutu ne. Bari mu aika, mu gani.” Saboda haka suka zaɓi kekunan yaƙi biyu tare da dawakansu, sarki kuwa ya aike su su bi bayan sojojin Arameyawa. Ya umarci masu tuƙinsu ya ce, “Ku je ku bincika abin da ya faru.”
  • “Ku shirya dawakai, ku sa musu sirdi! Ku tsaya a wurarenku saye da hulunan kwano a kai!”Irm 46:4
    Ayoyin
    Irm 46:4Ku shirya dawakai, ku sa musu sirdi! Ku tsaya a wurarenku saye da hulunan kwano a kai! Ku wasa māsunku, ku yafa kayan yaƙinku!
  • Kofatan ingarmun dawakai masu gudu da hayaniyar kekunan yaƙiIrm 47:3
    Ayoyin
    Irm 47:3da jin motsin takawar kofatan dawakai, da jin surutun kekunan yaƙin abokin gāba da motsin ƙafafunsu. Ubanni ba za su juye don su taimaki ’ya’yansu ba; hannuwansu za su yi laƙwas.

Sarakuna da ciniki

  • Doka: kada sarki ya tara wa kansa dawakai masu yawaM Sh 17:16
    Ayoyin
    M Sh 17:16Sarkin, ba zai nemi dawakai da yawa wa kansa ba, ko yă sa mutane su koma Masar don su sami ƙarin dawakai ba, gama Ubangiji ya faɗa muku, “Ba za ku ƙara koma wancan hanya kuma ba.”
  • Rumfunan Solomon domin dawakan kekunan yaƙinsa, da mahayan dawakansa1Sar 4:26, 2Tar 9:25
    Ayoyin
    1Sar 4:26Solomon yana da rumfunan dawakai masu jan kekunan yaƙi, dubu huɗu, da kuma dawakai dubu goma sha biyu
    2Tar 9:25Solomon ya kasance da wuraren ajiye dawakai dubu huɗu don dawakai da kekunan yaƙi, yana da dawakai dubu goma sha biyu waɗanda ya ajiye a biranen kekunan yaƙi da kuma tare da shi a Urushalima.
  • Doki daga Masar ya kai shekel 150 na azurfa, keken yaƙi kuma 6001Sar 10:28–29
    Ayoyin
    1Sar 10:28–29An yi jigilar dawakan Solomon daga Masar da kuma daga Kuye, ’yan kasuwan fadan sarki sun sayo su daga Kuye. Suka yi jigilar kekunan yaƙi daga Masar a bakin shekel ɗari shida na azurfa, doki ɗaya kuma a kan ɗari da hamsin. Sun kuma yi jigilarsu suna sayarwa ga dukan sarakunan Hittiyawa da na Arameyawa.
  • Dawakan Solomon sun zo daga Masar, Kuye da waɗansu ƙasashe1Sar 10:28, 2Tar 9:28
    Ayoyin
    1Sar 10:28An yi jigilar dawakan Solomon daga Masar da kuma daga Kuye, ’yan kasuwan fadan sarki sun sayo su daga Kuye.
    2Tar 9:28An sayo dawakan Solomon daga Masar da kuma daga dukan sauran ƙasashe.
  • Bet Togarma sun yi cinikin dawakai, dawakan yaƙi da alfadarai da TayaEzk 27:14
    Ayoyin
    Ezk 27:14“ ‘Mutanen Bet Togarma sun sayi kayan cinikinki da dawakai, dawakan yaƙi da alfadarai.
  • Waɗanda suka dawo daga Babilon suna da dawakai 736 da alfadarai 245Ezr 2:66
    Ayoyin
    Ezr 2:66Suna da dawakai guda 736, alfadarai 245,
  • Waɗansu a Yahuda sun tafi Masar don su dogara ga dawakanta da kekunan yaƙintaIsh 31:1
    Ayoyin
    Ish 31:1Kaiton waɗanda suka gangara zuwa Masar don neman taimako, waɗanda suke dogara ga dawakai, waɗanda suke dogara ga yawan kekunan yaƙinsu da kuma a girman ƙarfin mahayan dawakansu, amma ba sa dogara ga Mai Tsarkin nan na Isra’ila, ko ya nemi taimako daga Ubangiji.
  • Yosiya ya kawar da dawakan da sarakunan Yahuda suka keɓe wa rana2Sar 23:11
    Ayoyin
    2Sar 23:11Ya kawar da dawakan nan da sarakunan Yahuda suka keɓe wa gumakan nan na rana daga mashigin haikalin Ubangiji. Waɗannan dawakan suna kusa da ɗakin Natan Melek, ɗaya daga cikin dattawan sarki. Yosiya ya kuma ƙone kekunan yaƙi a yin sujada ga gumakan nan rana.
  • An zagaya da Mordekai cikin birni a kan dokin sarki kansaEsta 6:8–11
    Ayoyin
    Esta 6:8–11bari a kawo rigar sarautar da sarki ya taɓa sawa, da kuma dokin da sarki ya taɓa hawa, wanda aka sa kambin sarauta a kai. Sa’an nan, bari a ba da rigar da kuma dokin wa ɗaya daga cikin manyan sarakuna mafi kirki na sarki. Bari shi kuma yă sa wannan riga wa mutumin da sarki yake jin daɗi yă girmama, a kuma bi da shi a bisan doki ko’ina a titunan birni, ana shela a gabansa ana cewa, ‘Wannan shi ne abin da ake yin wa mutumin da sarki yake jin daɗi yă girmama!’ ” Sarki ya umarci Haman ya ce, “Tafi yanzu ka karɓi rigar da dokin, ka kuma yi yadda ka shawarta wa Mordekai, mutumin Yahudan nan, wanda yake zama a bakin ƙofar sarki. Kada ka kāsa yin kome daga cikin abin da ka faɗa.” Saboda haka, Haman ya karɓo rigar da dokin. Ya sa wa Mordekai rigar, ya kuma bi da shi a kan doki ko’ina a titunan birnin, yana shela a gabansa yana cewa, “Wannan shi ne abin da ake yi wa mutumin da sarki yake jin daɗi yă girmama!”
  • Keken yaƙi na wuta da dawakai na wuta sun raba Iliya da Elisha2Sar 2:11
    Ayoyin
    2Sar 2:11Yayinda suke tafiya suna magana, sai kwatsam, keken yaƙin wuta da dawakan wuta suka ratse tsakaninsu, sai Iliya ya tafi sama a cikin guguwa.

Maganganu

  • “dawakansa sun fi gaggafa sauri”Irm 4:13
    Ayoyin
    Irm 4:13Duba! Yana zuwa kamar gizagizai, kekunan yaƙinsa suna zuwa kamar guguwa, dawakansa sun fi gaggafa sauri. Kaiton mu! Mun shiga uku!
  • “Dawakansu sun fi damisoshi sauri, sun fi kyarketan yamma zafin rai”Hab 1:8
    Ayoyin
    Hab 1:8Dawakansu sun fi damisoshi sauri, sun fi kyarketan yamma zafin rai. Mahayansu suna zuwa a guje; mahayansu daga nesa suka fito. Suna firiya kamar ungulu mai sauka da gaggawa don yă ci mushe;
  • “Akan shirya doki domin ranar yaƙi”K Mag 21:31
    Ayoyin
    K Mag 21:31Akan shirya doki domin ranar yaƙi, amma nasara tana ga Ubangiji ne.
  • Zabura: ko babban ƙarfin doki ba ya iya cetoZab 33:17
    Ayoyin
    Zab 33:17Dogara a kan doki don ceto banza ne; duk da yawan ƙarfinsa ba ya ceto.
  • “Bulala don doki, linzami don jaki”K Mag 26:3
    Ayoyin
    K Mag 26:3Bulala don doki, linzami don jaki, sanda kuma don bayan wawaye!
  • “Dawakai sukan yi gudu a kan duwatsu?”Amos 6:12
    Ayoyin
    Amos 6:12Dawakai sukan yi gudu a kan duwatsu? Wani yana iya yin noma a teku da shanun noma? Amma ga shi kun mai da gaskiya ta zama dafi amfanin adalci kuma ya zama ɗaci,
  • “In ka yi tsere da mutane a ƙafa … yaya za ka yi gasa da dawakai?”Irm 12:5
    Ayoyin
    Irm 12:5“In ka yi tsere da mutane a ƙafa suka kuma gajiyar da kai, yaya za ka yi gasa da dawakai? In ka yi tuntuɓe a lafiyayyiyar ƙasa, ƙaƙa za ka yi a kurmin Urdun?

Tushe

Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.