Bible Explorer

Bincika › Jigogi › Gaggafa

Halitta

Gaggafa a cikin Littafi Mai Tsarki

Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (20), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.

  • Gaggafa tana cikin tsuntsayen da Isra’ila ba za su ci baFir 11:13, M Sh 14:12
    Ayoyin
    Fir 11:13“ ‘Waɗannan su ne tsuntsayen da za ku yi ƙyamarsu, ba za ku ci su ba domin sun zama abin ƙyama. Tsuntsayen kuwa su ne, gaggafa, ungulu, baƙin ungulu,
    M Sh 14:12Amma waɗannan ba za ku ci ba, gaggafa, ungulu, ungulun kwakwa,
  • Shaho yakan yi sheƙarsa can sama, yă zauna a kan dutseAyu 39:27–28
    Ayoyin
    Ayu 39:27–28Ko da umarninka ne shaho yake firiya ya kuma yi sheƙarsa a can sama? Yana zama a kan dutse yă zauna a wurin da dare; cikin duwatsu ne wurin zamansa.
  • Daga can yake neman abincinsa; idanunsa suna gani daga nesaAyu 39:29
    Ayoyin
    Ayu 39:29Daga can yake neman abincinsa; idanunsa suna gani daga nesa.
  • ’Ya’yansa suna shan jini; inda kisassu suke, a can yakeAyu 39:30
    Ayoyin
    Ayu 39:30’Ya’yansa suna shan jini, inda akwai waɗanda aka kashe nan za a same shi.”
  • Gaggafa takan tā da sheƙarta ta kuma yi shawagi bisa ’ya’yantaM Sh 32:11
    Ayoyin
    M Sh 32:11kamar gaggafar da take yawo a kan sheƙarta tana rufe ’ya’yanta, ta buɗe fikafikanta don tă kwashe su tă ɗauke su a kafaɗunta.
  • Gaggafa takan sauko da sauri a kan abin da za ta kamaAyu 9:26, Irm 49:22
    Ayoyin
    Ayu 9:26Suna wucewa kamar jirgin ruwan da aka yi da kyauro, kamar jahurma da ta kai wa namanta cafka.
    Irm 49:22Duba! Gaggafa tana firiya tana kuma saukowa, tana buɗe fikafikanta a bisa Bozra. A wannan rana zukatan jarumawan Edom za su zama kamar macen da take naƙuda.
  • “yadda gaggafa take firiya a sararin sama” — ɗaya daga cikin abubuwa huɗu masu ban mamakiK Mag 30:18–19
    Ayoyin
    K Mag 30:18–19“Akwai abubuwa uku da suke ba ni mamaki, abubuwa huɗu da ba na iya fahimtarsu, yadda gaggafa take firiya a sararin sama, yadda maciji yake tafiya a kan dutse, yadda jirgin ruwa yake tafiya a teku, da kuma sha’ani tsakanin namiji da ’ya mace.

Maganganu

  • Sun fi gaggafa sauri: Shawulu da Yonatan, masu fafarawa, dawakai2Sam 1:23, Mako 4:19, Irm 4:13
    Ayoyin
    2Sam 1:23Shawulu da Yonatan, a raye ƙaunatattu ne da kuma bansha’awa, a mace kuma ba su rabu ba. Sun fi gaggafa sauri, sun fi zaki ƙarfi.
    Mako 4:19Masu fafarar mu sun fi gaggafa mai firiya a sararin sama sauri; sun fafare mu a kan duwatsu suna fakon mu a jeji.
    Irm 4:13Duba! Yana zuwa kamar gizagizai, kekunan yaƙinsa suna zuwa kamar guguwa, dawakansa sun fi gaggafa sauri. Kaiton mu! Mun shiga uku!
  • A Sinai: “na ɗauko ku a kan fikafikan gaggafa”Fit 19:4
    Ayoyin
    Fit 19:4‘Ku da kanku kun ga abin da na yi wa Masar, da yadda na ɗauko ku a kan fikafikan gaggafa na kawo ku wurina.
  • Al’umma daga nesa da take sauko da sauri kamar gaggafaM Sh 28:49
    Ayoyin
    M Sh 28:49Ubangiji zai kawo al’umma daga nesa, daga iyakar duniya, ta sauko a kanku kamar gaggafa, al’ummar da ba ku san yarenta ba,
  • A makoki: “ku yi wa kanku ƙwalƙwal kamar ungulu”Mik 1:16
    Ayoyin
    Mik 1:16Ku aske kanku ƙwal don makoki, ku yi wa kanku ƙwalƙwal kamar ungulu. Gama za a ja ’ya’yan da kuke farin ciki a kai su bauta.
  • Wadata “sukan yi fikafikai sukan tashi sama kamar gaggafa”K Mag 23:5
    Ayoyin
    K Mag 23:5Da ƙyiftawar ido a kan wadata ta ɓace, gama tabbatacce sukan yi fikafikai sukan tashi sama kamar gaggafa.
  • “a sabunta ƙuruciyarka kamar na gaggafa”Zab 103:5
    Ayoyin
    Zab 103:5Wanda ya ƙosar da kai da abubuwa masu kyau domin a sabunta ƙuruciyarka kamar na gaggafa.
  • “Za su yi firiya da fikafikai kamar gaggafa”Ish 40:31
    Ayoyin
    Ish 40:31amma waɗanda suka dogara ga Ubangiji za su sabunta ƙarfinsu. Za su yi firiya da fikafikai kamar gaggafa; za su kuma yi gudu ba kuwa za su gaji ba, za su yi tafiya ba kuwa za su kasala ba.
  • “Ko da yake ka gina wa kanka sheƙa can bisa kamar na gaggafa”Irm 49:16, Oba 1:4
    Ayoyin
    Irm 49:16Tsoron da ka sa ake ji da kuma girman kan zuciyarka ya ruɗe ka, kai da kake zama a kogon dutse, kai da kake kan tudu. Ko da yake ka gina wa kanka sheƙa can bisa kamar na gaggafa, daga can zan sauko da kai ƙasa,” in ji Ubangiji.
    Oba 1:4Ko da yake kina firiya kamar gaggafa kin kuma yi sheƙarki a can cikin taurari, daga can zan saukar da ke,” in ji Ubangiji.

Tushe

Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.