Bible Explorer

Bincika › Jigogi › Bareyi da gadaje

Halitta

Bareyi da gadaje a cikin Littafi Mai Tsarki

Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (19), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.

  • Ana iya cin gada da barewa, mai tsarki da marar tsarki dukaM Sh 12:15, M Sh 14:5
    Ayoyin
    M Sh 12:15Amma kwa iya yanka nama ku ci a garuruwanku, a duk lokacin da ranku yake so, kamar yadda ake yi da gada ko barewa, bisa ga albarkar da Ubangiji Allahnku yake sa muku. Marar tsarki da mai tsarki, duka za ku iya ci.
    M Sh 14:5mariri, barewa, mariya, makwarna, mazo, gada da kuma tunkiyar dutse.
  • An tanada ƙishimai, bareyi da batsiyoyi domin teburin Solomon1Sar 4:22–23
    Ayoyin
    1Sar 4:22–23Tanajin Solomon na kowace rana su ne, garwa talatin na garin abinci, shanun da aka yi kiwo a gida guda goma, shanu ashirin da suka ƙoshi daga kiwo, tumaki da awaki ɗari; ban da ƙishimai, bareyi, batsiyoyi, da kaji masu ƙiba.
  • Ayuba: batsiya takan kwanta ta haifi ’ya’yanta; ’ya’yan sukan yi girma a jejiAyu 39:1–4
    Ayoyin
    Ayu 39:1–4“Ka san lokacin da awakin kan dutse suke haihuwa? Ko ka taɓa lura da yadda batsiya take haihuwa? Kana ƙirga watanni nawa suke yi kafin su haihu? Ka san lokacin da suke haihuwa? Suna kwanciya su haifi ’ya’yansu; naƙudarsu ta ƙare bayan sun haihu. ’Ya’yansu suna girma kuma suna girma cikin ƙarfi a jeji; sukan tafi ba su dawowa.
  • A lokacin fari barewa takan bar sabon ɗanta domin babu ciyawaIrm 14:5
    Ayoyin
    Irm 14:5Har barewa a kurmi ma ta gudu ta bar ’ya’yan da ta haihu sababbi saboda babu ciyawa.
  • “Kamar yadda barewa take marmarin ruwan rafuffuka”Zab 42:1
    Ayoyin
    Zab 42:1Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Maskil ne na ’Ya’yan Kora maza. Kamar yadda barewa take marmarin ruwan rafuffuka, haka raina yake marmarinka, ya Allah.
  • Bareyin da ba su sami wurin kiwo ba ba su da ƙarfin guje wa mai farautaMako 1:6
    Ayoyin
    Mako 1:6Diyar Sihiyona ba ta da sauran daraja. ’Ya’yan sarakunanta sun zama kamar bareyi waɗanda suka rasa wurin kiwo; cikin rashin ƙarfi suka guje wa masu fafararsu.
  • Barewa takan ’yantar da kanta daga hannun mai farautaK Mag 6:5
    Ayoyin
    K Mag 6:5Ka ’yantar da kanka, kamar barewa daga hannun mai farauta, kamar tsuntsu daga tarkon mai kafa tarko.

Maganganu

  • Asahel mai gudu ne kamar barewa2Sam 2:18
    Ayoyin
    2Sam 2:18’Ya’yan Zeruhiya, maza uku sun kasance a can. Su ne, Yowab, Abishai da Asahel. To, Asahel mai gudu ne kamar barewa.
  • Jarumawan Gad suna da sauri kamar bareyi a kan duwatsu1Tar 12:8
    Ayoyin
    1Tar 12:8Sai waɗansu mutanen Gad suka koma suna goyon bayan Dawuda suka kuma haɗa kai da shi a kagararsa a hamada. Su ƙwararrun mayaƙa ne, a shirye don yaƙi, kuma suna iya riƙe garkuwa da māshi. Fuskokinsu kamar fuskoki zakoki, kuma suna da sauri kamar bareyi a kan duwatsu.
  • “Ya sa ƙafafuna kamar ƙafafun barewa” a kan ƙwanƙoli2Sam 22:34, Zab 18:33, Hab 3:19
    Ayoyin
    2Sam 22:34Ya sa ƙafafuna kamar ƙafafun barewa; ya sa na iya tsayawa a kan duwatsu.
    Zab 18:33Ya sa ƙafafuna kamar ƙafafun barewa; ya sa na iya tsaya a kan ƙwanƙoli.
    Hab 3:19Ubangiji Mai Iko Duka shi ne ƙarfina; yakan mai da ƙafafuna kamar na barewa, yakan sa in yi tafiya a wurare masu tsayi. Domin mai bi da kaɗe-kaɗe. A kan kayan kiɗi masu tsirkiyata.
  • “Ƙaunatacciyar mariri, barewa mai kyan gani”K Mag 5:19
    Ayoyin
    K Mag 5:19Ƙaunatacciyar mariri, barewa mai kyan gani, bari mamanta su ishe ka kullum, bari ƙaunarta ta ɗauke hankalinka kullum.
  • Ƙaunataccen, kamar barewa ko sagarin ƙishimi a kan duwatsuWW 2:9, WW 2:17, WW 8:14
    Ayoyin
    WW 2:9Ƙaunataccena yana kama da barewa ko sagarin ƙishimi Duba! Ga shi can tsaye a bayan katangarmu, yana leƙe ta tagogi, yana kallo ta cikin asabari.
    WW 2:17Sai gari ya waye inuwa kuma ta watse, ka juye, ƙaunataccena, ka zama kamar barewa ko kamar sagarin ƙishimi a kan tuddai masu ciyawa.
    WW 8:14Ka zo, ƙaunataccena, ka zama kamar barewa ko kuwa kamar ’yar batsiya a kan dutsen da kayan yaji suke a shimfiɗe.
  • “ku yi mini alkawari da bareyi da ƙishimai na jeji”WW 2:7
    Ayoyin
    WW 2:7’Yan matan Urushalima, ku yi mini alkawari da bareyi da ƙishimai na jeji. Ba za ku tā da ko ku farka ƙauna ba sai haka ya zama lalle.
  • “Naftali sakakkiyar barewa ce”Far 49:21
    Ayoyin
    Far 49:21“Naftali sakakkiyar barewa ce da take haihuwar kyawawan ’ya’ya.

Tushe

Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.