Bible Explorer

Bincika › Jigogi › Iskoki

Halitta

Iskoki a cikin Littafi Mai Tsarki

Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (32), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.

Iskar gabas

  • Mafarkin Fir’auna: zangarkun hatsi da iskar gabas ta ƙonaFar 41:6, Far 41:23
    Ayoyin
    Far 41:6Bayansu, sai ga waɗansu kawuna bakwai na dawa, suka fito sirara waɗanda iskar gabas ta sa suka yanƙwane.
    Far 41:23Bayansu, sai ga waɗansu kawuna bakwai suka fito, yanƙwananne sirara waɗanda iskar gabas ta yanƙwane.
  • Iskar gabas ta hura yini da dare ta kawo fāraFit 10:13
    Ayoyin
    Fit 10:13Saboda haka Musa ya miƙa sandansa bisa Masar, Ubangiji kuwa ya sa iskar gabas ta hura a kan ƙasar dukan dare da kuma dukan yini. Da safe kuwa iskar ta kawo fāra;
  • Iskar gabas mai ƙarfi ta kori teku dukan dareFit 14:21
    Ayoyin
    Fit 14:21Da Musa ya miƙa hannunsa a bisa teku, sai Ubangiji ya tura teku baya da iskar gabas mai ƙarfi duk dare, ya maishe shi busasshiyar ƙasa. Ruwa ya rabu,
  • Iskar gabas mai zafi da rana sun sa Yunana sumaYun 4:8
    Ayoyin
    Yun 4:8Sa’ad da rana ta yi sama, sai Allah ya sa iskar gabas mai zafi ta huro, zafin ranar kuma ya buga kan Yunana, har ya ji sai ka ce zai suma. Ya so a ce ya mutu ma, sai ya ce, “Gara in mutu da a ce ina zaune da rai.”
  • Iskar gabas takan farfasa jiragen ruwa a tekuZab 48:7, Ezk 27:26
    Ayoyin
    Zab 48:7Ka hallaka su kamar jiragen ruwan Tarshish da iskar gabas ta wargaje.
    Ezk 27:26Matuƙan jiragenki sun kai ki can cikin manyan tekuna. Amma iskar gabas za tă farfasa ki kucu-kucu a tsakiyar teku.

Waɗansu iskoki

  • Iska mai ƙarfi ta yamma ta kora fāra cikin Jan TekuFit 10:19
    Ayoyin
    Fit 10:19Sai Ubangiji ya canja iska zuwa iska mai ƙarfi ta yamma wadda ta ɗibi fārar zuwa Jan Teku. Babu fāran da suka rage a wani wuri a Masar.
  • “iskar arewa kan kawo ruwan sama”K Mag 25:23
    Ayoyin
    K Mag 25:23Kamar yadda iskar arewa kan kawo ruwan sama, haka jita-jita kan kawo fushi.
  • Sanyi yakan zo daga iska mai sanyiAyu 37:9
    Ayoyin
    Ayu 37:9Guguwa tana fitowa daga inda take, sanyi kuma daga iska mai sanyi.
  • Tufafi sukan yi zafi sa’ad da ƙasa ta yi shiru a ƙarƙashin iskar kuduAyu 37:17
    Ayoyin
    Ayu 37:17Kai mai sa kaya don ka ji ɗumi lokacin da iska mai sanyi take hurawa,
  • “Sa’ad da kuma iska ta taso daga kudu, kukan ce, ‘Za a yi zafi’”Luk 12:55
    Ayoyin
    Luk 12:55Sa’ad da kuma iska ta taso daga kudu, kukan ce, ‘Za a yi zafi,’ sai kuwa a yi.
  • Bayan iska ta share sararin sama, ba mai iya kallon ranaAyu 37:21
    Ayoyin
    Ayu 37:21Yanzu ba wanda zai iya kallon rana, yadda take da haske a sararin sama bayan iska ta share ta.

A cikin labarai

  • Iska ta hura a kan duniya, ruwan rigyawa kuma ya fara janyewaFar 8:1
    Ayoyin
    Far 8:1Amma Allah ya tuna da Nuhu da dukan namun jeji da dabbobin da suke tare da shi a cikin jirgi, ya kuma aika da wata iska ta hura dukan duniya, ruwan kuwa ya janye.
  • Iska ta kawo makwarwa daga tekuƘid 11:31
    Ayoyin
    Ƙid 11:31Ana nan, sai Ubangiji ya kawo wata iska mai tsanani ta koro makware daga teku. Ta bar su birjik kewaye da sansani, tsayinsu daga ƙasa ya kai kamu biyu, misalin tafiyar nisan yini guda ta kowace fuska.
  • Iskar hamada ta bugi kusurwoyi huɗu na gidan ’ya’yan AyubaAyu 1:18–19
    Ayoyin
    Ayu 1:18–19Yana cikin magana, sai ga wani ɗan aika ya zo ya ce, “’Ya’yanka maza da mata suna biki, suna ci suna sha a gidan babban ɗanka, sai wata iska mai ƙarfi daga hamada ta auka ta rushe gidan, gidan kuwa ya fāɗi a kan ’ya’yanka ya kashe su, ni kaɗai na tsira na zo in gaya maka!”
  • A Horeb babbar iska ta farfashe duwatsu, sa’an nan girgizar ƙasa ta zo1Sar 19:11
    Ayoyin
    1Sar 19:11Sai Ubangiji ya ce, “Fita ka tsaya a kan dutse a gaban Ubangiji, gama Ubangiji yana shirin wucewa.” Sai ga babbar iska mai ƙarfi ta tsage duwatsu, ta kuma ragargaza duwatsu a gaban Ubangiji, amma Ubangiji ba ya cikin iskar. Bayan iskar sai aka yi girgizar ƙasa, amma Ubangiji ba ya cikin girgizar ƙasa.
  • Babbar iska a teku ta kusan farfashe jirgin ruwan YunanaYun 1:4
    Ayoyin
    Yun 1:4Sai Ubangiji ya aika da babban iska a bisan teku, hadiri ya tsananta ƙwarai har jirgin ya yi barazanar farfashewa.
  • Yesu ya tsawata wa iska da teku, sai wuri ya yi tsitMat 8:24–27
    Ayoyin
    Mat 8:24–27Ba zato ba tsammani, sai wani babban hadari ya taso a tafkin, har raƙuman ruwan suka sha kan jirgin. Amma Yesu yana barci. Almajiran suka je suka tashe shi, suna cewa, “Ubangiji, ka cece mu! Za mu nutse!” Ya amsa ya ce, “Ku masu ƙarancin bangaskiya, me ya sa kuke tsoro haka?” Sa’an nan ya tashi ya tsawata wa iskar da kuma raƙuman ruwan, sai wuri ya yi tsit gaba ɗaya. Mutanen suka yi mamaki suka ce, “Wane irin mutum ne wannan? Har iska da raƙuman ruwa suna masa biyayya!”
  • Almajirai sun sha wahalar tuƙi, domin iska tana gāba da suMar 6:48, Mat 14:24, Yoh 6:18
    Ayoyin
    Mar 6:48Ya ga almajiran suna fama da tuƙi saboda iska tana gāba da su. Wajen tsara ta huɗu na dare, sai ya tafi wurinsu, yana takawa a kan tafkin. Ya yi kamar zai wuce su,
    Mat 14:24jirgin ruwan kuwa ya riga ya yi nesa da gaci, yana fama da raƙuman ruwa domin iska tana gāba da shi.
    Yoh 6:18Iska mai ƙarfi kuwa tana bugowa, ruwaye kuma suka fara hauka.
  • Iskar kudu a hankali, sa’an nan guguwar da ake kira ’Yar arewa maso gabasAyy M 27:13–15
    Ayoyin
    Ayy M 27:13–15Da iska ta fara busowa daga kudu a hankali, sai suka yi tsammani sun sami abin da suke nema; saboda haka suka janye ƙugiyar jirgin ruwa suka bi ta gefen tsibirin Kirit. Ba a jima ba, sai ga wata guguwar iska mai ƙarfin da ake kira “’Yar arewa maso gabas,” ta buga daga tsibirin. Iskar ta ci ƙarfin jirgin ruwan har ya kāsa fuskantar iskar; saboda haka muka sallamar mata tă yi ta tura mu.
  • Da iskar kudu jirgin ruwan Bulus ya tafi daga Regiyum zuwa Futeyoli cikin kwana biyuAyy M 28:13
    Ayoyin
    Ayy M 28:13Daga can muka tashi muka isa Regiyum. Kashegari iskar kudu ta taso, kashegari kuma muka kai Futeyoli.

Maganganu

  • “Iska takan hura zuwa kudu ta kuma juya zuwa arewa; tă yi ta kewayewa”M Had 1:6
    Ayoyin
    M Had 1:6Iska takan hura zuwa kudu ta kuma juya zuwa arewa; tă yi ta kewayewa, tă yi ta koma inda take fitowa.
  • “Duk mai la’akari da iska, ba zai yi shuka ba”M Had 11:4
    Ayoyin
    M Had 11:4Duk mai la’akari da iska, ba zai yi shuka ba, mai la’akari da gizagizai kuma, ba zai yi girbi ba.
  • “ba ka san hanyar iska ba”M Had 11:5
    Ayoyin
    M Had 11:5Kamar yadda ba ka san hanyar iska ba, ko yadda aka siffanta jiki a cikin mahaifiya, haka ba za ka fahimci aikin Allah Mahaliccin dukan abubuwa ba.
  • “Iska takan hura zuwa inda take so. Kai kakan ji motsinta”Yoh 3:8
    Ayoyin
    Yoh 3:8Iska takan hura zuwa inda take so. Kai kakan ji motsinta, sai dai ba ka iya sanin inda take fitowa ko kuwa inda za ta. Haka yake ga duk wanda aka haifa ta wurin Ruhu.”
  • Kamar ƙaiƙayin da iska take kwashewaZab 1:4
    Ayoyin
    Zab 1:4Ba haka yake da mugaye ba! Su kamar yayi ne da iska take kwashewa.
  • “Ciyawar da iska take kaɗawa ne?”Mat 11:7
    Ayoyin
    Mat 11:7Sa’ad da almajiran Yohanna suke barin wurin, sai Yesu ya fara yi wa taron magana game da Yohanna. “Me kuka je kallo a hamada? Ciyawar da iska take kaɗawa ne?
  • Manyan jiragen ruwa da iskoki masu ƙarfi suke kora ana juya su da ƙaramin abin tuƙiYaƙ 3:4
    Ayoyin
    Yaƙ 3:4Ko kuwa misali, mu dubi jiragen ruwa, mana. Ko da yake suna da girma ƙwarai kuma iska mai ƙarfi ce take tura su, ana tuƙa su da ɗan ƙaramin sandan ƙarfe ne zuwa duk inda mai tuƙin jirgin yake so.
  • “raƙumar ruwan tekun da iska take kori”Yaƙ 1:6
    Ayoyin
    Yaƙ 1:6Amma sa’ad da ya roƙa, dole yă gaskata, ba tare da shakka ba, domin shi mai shakka, yana kama da raƙumar ruwan tekun da iska take kori tana kuma ɓuɓɓugowa.

Tushe

Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.