Bible Explorer

Bincika › Jigogi › Macizai

Halitta

Macizai a cikin Littafi Mai Tsarki

Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (28), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.

  • Farawa: maciji ya fi kowace dabbar jeji wayoFar 3:1
    Ayoyin
    Far 3:1To, maciji dai ya fi kowane a cikin namun jejin da Ubangiji Allah ya yi wayo. Ya ce wa macen, “Tabbatacce ne Allah ya ce, ‘Kada ku ci daga kowane itace a lambu’?”
  • Farawa: maciji zai yi tafiya da cikinsa ya kuma ci ƙuraFar 3:14
    Ayoyin
    Far 3:14Saboda haka Ubangiji Allah ya ce wa macijin, “Saboda ka yi haka, “Na la’anta ka cikin dukan dabbobi da kuma cikin dukan namun jeji! Daga yanzu rubda ciki za ka yi tafiya turɓaya kuma za ka ci dukan kwanakin rayuwarka.
  • “yadda maciji yake tafiya a kan dutse” — ɗaya daga cikin abubuwa huɗu masu ban mamakiK Mag 30:18–19
    Ayoyin
    K Mag 30:18–19“Akwai abubuwa uku da suke ba ni mamaki, abubuwa huɗu da ba na iya fahimtarsu, yadda gaggafa take firiya a sararin sama, yadda maciji yake tafiya a kan dutse, yadda jirgin ruwa yake tafiya a teku, da kuma sha’ani tsakanin namiji da ’ya mace.
  • Macizai a katanga: wanda ya huda ta ko ya jingina da ita zai iya sāran saM Had 10:8, Amos 5:19
    Ayoyin
    M Had 10:8Duk wanda ya haƙa rami shi ne zai fāɗa a ciki; duk wanda ya rushe katanga, shi maciji zai sara.
    Amos 5:19Za ku zama kamar mutanen da suka guje wa zaki sai suka fāɗa a hannun beyar, ko kuma kamar wanda ya shiga gida ya dāfa hannu a bango sai maciji ya sare shi.
  • Masu layar maciji: ba riba in maciji ya sāra kafin a yi masa layaM Had 10:11
    Ayoyin
    M Had 10:11In maciji ya sari mutum kafin a ba shi makarin gardi, ina amfanin maganin?
  • Gamsheƙa da ya toshe kunnuwansa ga waƙar mai layaZab 58:4–5
    Ayoyin
    Zab 58:4–5Dafinsu ya yi kamar dafin maciji, kamar na gamsheƙan da ya toshe kunnuwansa, da ba ya jin muryar gardi, kome dabarar gwanin mai waƙar zai zama.
  • Gamsheƙai da ba a iya yi musu layaIrm 8:17
    Ayoyin
    Irm 8:17“Duba, zan aika macizai masu dafi a cikinku, kāsā, waɗanda ba su da maƙari, za su kuwa sassare ku,” in ji Ubangiji.
  • Gamsheƙa a gefen hanya yakan sari diddigen doki, mahayinsa kuma ya fāɗiFar 49:17
    Ayoyin
    Far 49:17Dan zai zama maciji a gefen hanya, kububuwa a bakin hanya, da take saran ɗiɗɗigen doki domin mahayinsa yă fāɗi da baya.
  • Jejin yana da macizai masu dafi da kunamaiM Sh 8:15
    Ayoyin
    M Sh 8:15Ya bishe ku cikin hamada mai fāɗi, mai bantsoro, wannan busasshiyar ƙasa wadda ba ta da ruwa, ga macizai masu dafi da kuma kunamai. Ya ba ku ruwa daga dutsen ƙanƙara.
  • Negeb: ƙasar zaki, gamsheƙa da maciji mai tashi samaIsh 30:6
    Ayoyin
    Ish 30:6Allah ya faɗa game da dabbobin Negeb cewa, Ta cikin ƙasa mai wahala da mai hatsari inda zakoki da zakanya, inda macizai masu dafi da macizai masu tashi sama suke, jakadu na ɗaukan arzikinsu a kan jakuna, dukiyarsu a kan raƙuma, zuwa ƙasan nan marar riba,
  • Ka fasa ƙwan gamsheƙa, sai gamsheƙa ya ƙyanƙyasheIsh 59:5
    Ayoyin
    Ish 59:5Suna ƙyanƙyashe ƙwan kāsā su kuma saƙa yanar gizo-gizo. Duk wanda ya ci ƙwansu zai mutu, kuma sa’ad da ƙwan ya fashe, zai ƙyanƙyashe kububuwa.

A cikin labarai

  • Sandan Musa ya zama maciji; ya gudu daga gare shi, sa’an nan ya kama shi a wutsiyaFit 4:3–4
    Ayoyin
    Fit 4:3–4Sai Ubangiji ya ce, “Jefa shi ƙasa.” Musa ya jefa shi ƙasa, sai sandan ya zama maciji, Musa kuwa ya gudu daga gare shi. Sai Ubangiji ya ce masa, “Sa hannunka ka ɗauke shi ta wutsiya.” Sai Musa ya miƙa hannu, ya kama macijin, macijin kuwa ya dawo sanda a hannunsa.
  • Sandan Haruna ya zama maciji ya haɗiye sandunan bokayeFit 7:10–12
    Ayoyin
    Fit 7:10–12Sai Musa da Haruna suka tafi wurin Fir’auna, suka yi yadda Ubangiji ya umarce su. Haruna ya jefa sandansa ƙasa, a gaban Fir’auna da bayinsa, sai sandan ya zama maciji. Fir’auna kuwa ya kira masu hikima da masu sihiri, sai bokayen Masarawa ma suka yi irin abubuwan nan da bokancinsu. Kowannensu ya jefa sandansa ƙasa, ya kuwa zama maciji. Amma sandan Haruna ya haɗiye sandunansu.
  • Macizai masu dafi sun sari Isra’ilawa a jeji, da yawa kuma suka mutuƘid 21:6
    Ayoyin
    Ƙid 21:6Sai Ubangiji ya aiko da macizai masu dafin a cikinsu, suka sassari mutane, Isra’ilawa masu yawa kuwa suka mutu.
  • Musa ya yi macijin tagulla a kan sanda; waɗanda aka sāra da suka dube shi sun rayuƘid 21:8–9
    Ayoyin
    Ƙid 21:8–9Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ƙera siffar maciji ka rataye shi a bisa doguwar sanda; kowa da maciji ya sare shi, idan ya dubi macijin nan da ka rataye, zai rayu.” Saboda haka Musa ya ƙera macijin tagulla, ya kuma rataye shi bisa doguwar sanda. Sa’an nan duk wanda maciji ya sare shi, ya kuma dubi macijin tagullar, zai warke.
  • Hezekiya ya fasa macijin tagullan nan, Nehushtan, domin ana ƙona masa turare2Sar 18:4
    Ayoyin
    2Sar 18:4Ya kawar da masujadan kan tudu, ya farfasa keɓaɓɓun duwatsu, ya sassare ginshiƙan Ashera. Ya fashe macijin tagullan da Musa ya yi, gama har zuwa lokacin nan Isra’ilawa suna ƙona turare gare shi. (An ba shi suna Nehushtan.)
  • A Malta maciji, da zafin wuta ya fitar, ya dāfe a hannun BulusAyy M 28:3–4
    Ayoyin
    Ayy M 28:3–4Bulus ya tattara tarin itace, yayinda kuma yake sa itacen a wuta, sai maciji ya ɓullo saboda zafi, ya dāfe a hannunsa. Da mutanen tsibirin suka ga macijin yana lilo a hannunsa, sai suka ce wa juna “Lalle, wannan mutum mai kisankai ne; gama ko da yake ya tsira daga teku, Adalci bai bar shi ya rayu ba.”
  • Bulus ya karkaɗe shi; mazaunan tsibirin sun jira ya kumburaAyy M 28:5–6
    Ayoyin
    Ayy M 28:5–6Amma Bulus ya karkaɗe macijin a cikin wuta, bai kuwa ji wani ciwo ba. Mutanen kuma suka yi zato zai kumbura ko kuma nan da nan zai fāɗi matacce, amma da aka daɗe ba su ga wani abu ya faru da shi ba, sai suka sāke ra’ayi suka ce shi wani allah ne.
  • Yesu ya ba almajiransa iko su taka macizai da kunamaiLuk 10:17, Luk 10:19
    Ayoyin
    Luk 10:17Mutum saba’in da biyun nan suka dawo da murna, suka ce, “Ubangiji, har mun sha ƙarfin aljanu ma a cikin sunanka.”
    Luk 10:19Na ba ku iko da za ku tattaka macizai, da kunamai, ku kuma shawo kan dukan ikon abokin gāba, kuma ba wani lahani da zai same ku.

Maganganu

  • “ku zama masu wayo kamar macizai, kuma marasa ɓarna kamar kurciyoyi”Mat 10:16
    Ayoyin
    Mat 10:16“Ina aikan ku kamar tumaki a cikin kyarketai. Saboda haka ku zama masu wayo kamar macizai, kuma marasa ɓarna kamar kurciyoyi.
  • Wane uba ne zai ba ɗansa maciji in ya roƙi kifi?Mat 7:10, Luk 11:11
    Ayoyin
    Mat 7:10Ko kuwa in ya roƙe shi kifi, sai yă ba shi maciji?
    Luk 11:11“Wane mahaifi ne a cikinku, in ɗansa ya roƙe shi kifi, zai ba shi maciji a maimakon,
  • Ruwan inabi “yana sara kamar maciji da kuma dafi kamar gamsheƙa”K Mag 23:31–32
    Ayoyin
    K Mag 23:31–32Kada ka ƙyifce ido a ruwan inabi sa’ad da ya yi ja, sa’ad da yana da kyan gani a cikin ƙwarya, sa’ad da yana gangarawa sumul a maƙogwaro! A ƙarshe yana sara kamar maciji da kuma dafi kamar gamsheƙa.
  • “Suna sa harsunansu su yi kaifi kamar na maciji”Zab 140:3
    Ayoyin
    Zab 140:3Suna sa harsunansu su yi kaifi kamar na maciji; dafin gamsheƙa yana a leɓunansu. Sela
  • “Za su lashi ƙura kamar maciji”Mik 7:17
    Ayoyin
    Mik 7:17Za su lashi ƙura kamar maciji, kamar dabbobi masu rarrafe a ƙasa. Za su fito daga maɓuyarsu da rawan jiki, za su juya cikin tsoro ga Ubangiji Allahnmu su kuma ji tsoronku.
  • Masar “za tă yi huci kamar macijin da yake gudu”Irm 46:22
    Ayoyin
    Irm 46:22Masar za tă yi huci kamar macijin da yake gudu yayinda abokin gāba yana matsowa da ƙarfi; za su fāɗo mata gatura kamar mutanen da suke saran itatuwa.

Tushe

Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.