Bible Explorer

Bincika › Jigogi › Zakoki

Halitta

Zakoki a cikin Littafi Mai Tsarki

Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (31), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.

  • Zaki yakan yi ruri a kan abin da ya kama; ɗan zaki yakan yi gurnani a kogonsaAmos 3:4
    Ayoyin
    Amos 3:4Zaki yakan yi ruri a jeji in bai sami kama nama ba? Zai yi gurnani a cikin kogonsa in bai kama kome ba?
  • Zakanya da ’yan zakoki sukan labe a kogunansu su yi kwanto a cikin sarƙaƙiyaAyu 38:39–40
    Ayoyin
    Ayu 38:39–40“Za ka iya farauto wa zakanya nama, ka kuma kawar wa zakoki yunwarsu. Lokacin da suka kwanta cikin kogunansu, ko kuma lokacin da suke a wurin ɓuyansu?
  • Zaki ya yayyaga abin farauta domin ’ya’yansa ya cika kogunansa da abin da ya kasheNah 2:11–12
    Ayoyin
    Nah 2:11–12Ina kogon zakokin nan yake yanzu, inda suka ciyar da ’ya’yansu, inda zaki da zakanya sukan shiga, da ’ya’yansu, ba mai damunsu Zaki ya kashe abin da ya ishe ’ya’yansa ya kuma murɗe wuyan dabbobi ya cika wurin zamansa da abin da ya kama ya cika kogwanninsa da abin da ya kashe.
  • Tsohon zaki yakan mutu don rashin abin farauta; ’ya’yan zakanya sukan watseAyu 4:10–11
    Ayoyin
    Ayu 4:10–11Zakoki suna ruri suna gurnani; duk da haka an karya haƙoran manyan zakoki. Zakoki suna mutuwa domin ba dabbar da za su kashe su ci, ’ya’yan zakanya kuma sun watse.
  • Mai ƙarfi cikin namun jeji, ba ya ja da baya a gaban komeK Mag 30:30
    Ayoyin
    K Mag 30:30zaki mai ƙarfi a cikin namun jeji, wanda ba ya ratse wa kowa;
  • Zakoki suna zaune a kurmin UrdunIrm 49:19, Irm 50:44, Zak 11:3
    Ayoyin
    Irm 49:19“Kamar zaki mai haurawa daga kurmin Urdun zuwa wurin kiwo mai kyau, zan kori Edom daga ƙasarta nan da nan. Wane ne zaɓaɓɓen da zan naɗa don wannan? Wane ne yake kama da ni kuma wa zai kalubalance ni? Kuma wane makiyayi ne zai yi gāba da ni?”
    Irm 50:44Kamar zaki mai haurawa daga kurmin Urdun zuwa wurin kiwo mai dausayi, zan fafare Babilon daga ƙasan nan da nan. Wane ne zaɓaɓɓen da zan naɗa domin wannan? Wane ne kamar ni da zai kalubalance ni? Kuma wanda makiyayi zai iya tsaya gāba da ni?”
    Zak 11:3Ku ji kukan makiyaya; an ɓata musu wuraren kiwonsu masu ciyayi! Ku ji rurin zakoki; an lalatar da jejin Urdun!
  • Makiyayi yakan ƙwace ƙafafu biyu kawai ko gutsuren kunne daga bakin zakiAmos 3:12
    Ayoyin
    Amos 3:12Ga abin da Ubangiji ya ce, “Kamar yadda makiyayi yakan ceci daga bakin zaki ƙasusuwa ƙafafu biyu kawai ko kunne ɗaya, haka za a ceci Isra’ilawa, masu zama a Samariya da kan gado kawai da kuma a ɗan ƙyalle a kan dogayen kujerunsu.”
  • Ihun ƙungiyar makiyaya ba ya tsorata zaki ya bar abin da ya kamaIsh 31:4
    Ayoyin
    Ish 31:4Ga abin da Ubangiji ya faɗa mini, “Kamar yadda zaki kan yi ruri babban zaki a kan abin da ya yi farauta, kuma ko da yake dukan ƙungiyar makiyaya sun taru wuri ɗaya a kansa, ba zai jijjigu ta wurin ihunsu ba ko ya damu da kiraye-kirayensu, ta haka Ubangiji Maɗaukaki zai sauko don yă yi yaƙi a kan Dutsen Sihiyona da kuma a kan ƙwanƙolinsa.

Gamuwa

  • Samson ya yayyaga ɗan zaki da hannunsa kawaiMah 14:5–6
    Ayoyin
    Mah 14:5–6Sai Samson ya gangara zuwa Timna tare da mahaifinsa da kuma mahaifiyarsa. Da suka yi kusa da gonar inabin Timna, nan da nan sai ga ɗan zaki ya taso ya nufe shi yana ruri. Ruhun Ubangiji kuwa ya sauko masa da ƙarfi, ya sa ya yaga zakin kashi biyu da hannu kamar yadda akan yayyage ɗan akuya. Sai dai bai gaya wa iyayensa abin da ya yi ba.
  • Daga baya ya sami ƙudan zuma da zuma a cikin gawar zakinMah 14:8–9
    Ayoyin
    Mah 14:8–9Daga baya, da ya koma don yă aure ta, sai ya ratse don yă ga gawar zakin. Sai ga taron ƙudan zuma da zuma a ciki, wanda ya sa hannu ya ɗebo yana tafiya yana sha. Sa’ad da ya iso wurin iyayensa, ya ba su zuman, su ma suka sha. Sai dai bai gaya musu cewa ya ɗebo zuman daga gawar zaki ba.
  • Kacici-kacicinsa: “Daga mai ci, abinci ya fito”Mah 14:14, Mah 14:18
    Ayoyin
    Mah 14:14Sai ya ce, “Daga mai ci, abinci ya fito; daga mai ƙarfi, abu mai zaki ya fito.” Har kwana uku ba su iya ba da amsa ba.
    Mah 14:18Kafin rana ta fāɗi a rana ta bakwai mutane garin suka ce masa, “Me ya fi zuma zaki? Me ya fi zaki ƙarfi?” Samson ya ce musu, “Da ba don kun haɗa baki da matata ba, da ba za ku san amsar kacici-kacici ba.”
  • Dawuda, yaro makiyayi, ya kashe zakoki da beyar da suke ɗaukar ’yan raguna1Sam 17:34–36
    Ayoyin
    1Sam 17:34–36Amma Dawuda ya ce wa Shawulu, “Bawanka yana kiwon tumakin mahaifinsa. Sa’ad da zaki ko beyar ta zo ta kama tunkiya, ta tafi da ita. Nakan bi ta a baya in buga ta in kuma ƙwato tunkiyar daga bakinta. In kuma ta taso mini, nakan cafke ta a gashinta in buga ta in kashe. Bawanka ya kashe zaki da beyar, wannan Bafilistin marar kaciya zai zama kamar ɗaya daga cikinsu, domin ya rena rundunar Allah mai rai.
  • Benahiya ya shiga rami a ranar da ake ƙanƙara ya kashe zaki2Sam 23:20
    Ayoyin
    2Sam 23:20Benahiya, ɗan Yehohiyada mutumin Kabzeyel shi ma jarumi ne sosai, ya yi nasarori masu yawa. Ya bugi ƙwararrun jarumawan Mowab guda biyu. Ya kuma shiga rami wata ranar da ake ƙanƙara, ya kashe zaki.
  • Zaki ya kashe mutumin Allah amma bai cinye shi ba, bai kuma taɓa jakinsa ba1Sar 13:24–28
    Ayoyin
    1Sar 13:24–28Yayinda yake kan hanyarsa, sai wani zaki ya sadu da shi ya kashe shi, aka kuma jefar da jikinsa a kan hanya, jakin da zakin suka tsaya kusa da gawar. Waɗansu mutane masu wucewa suka ga an yar da gawar a can, zaki yana tsaye kusa da gawar, sai suka tafi suka ba da labarin a birni inda tsohon annabin nan yake zama. Sa’ad da annabin da ya dawo da mutumin Allah ya ji, sai ya ce, “Mutumin Allah ne, wanda ya ƙazantar da maganar Ubangiji. Ubangiji ya bashe shi ga zaki, wanda ya yayyage shi ya kuma kashe shi, kamar yadda maganar Ubangiji ta gargaɗe shi.” Sai annabin ya ce wa ’ya’yansa, “Ku yi wa jakina shimfiɗa.” Sai suka yi. Sai ya fita ya sami an jefar da gawar a hanya, jakin da zakin suna tsaye kusa da shi. Zakin bai ci gawar ko yă yayyage jakin ba.
  • Zaki ya kashe mutumin da ya ƙi ya bugi annabin1Sar 20:35–36
    Ayoyin
    1Sar 20:35–36Ta wurin maganar Ubangiji, ɗaya daga cikin ’ya’ya maza na annabawa ya ce wa abokinsa, “Ka buge ni da makaminka,” amma mutumin ya ƙi. Sai annabin ya ce, “Domin ba ka yi biyayya da Ubangiji ba, da zarar ka bar ni zaki zai kashe ka.” Daga baya mutumin ya tafi, zaki ya same shi, ya kuma kashe shi.
  • Zakoki sun kashe waɗansu daga cikin mazaunan da aka kawo garuruwan Samariya2Sar 17:25–26
    Ayoyin
    2Sar 17:25–26Sa’ad da suka fara zama a can, ba su bauta wa Ubangiji ba; saboda haka ya aika da zakoki a tsakaninsu suka karkashe waɗansu mutane. Sai aka faɗa wa sarkin Assuriya cewa, “Mutanen da ka kwashe ka zaunar a garuruwan Samariya fa ba su san abin da allahn ƙasar yake bukata ba. Saboda haka allahn ƙasar ya tura zakoki a cikinsu, waɗanda suke karkashe su, domin mutanen ba su san abin da yake bukata ba.”
  • An jefa Daniyel cikin kogon zakoki, aka hatimce shi da dutse da zoben sarkiDan 6:16–17
    Ayoyin
    Dan 6:16–17Saboda haka sai sarki ya ba da umarni suka kuma kawo Daniyel suka jefa shi cikin ramin zakoki. Sarki ya ce wa Daniyel, “Bari Allahn nan wanda kake bauta masa kullum, yă cece ka!” Aka kawo dutsen aka rufe bakin ramin, sa’an nan sarki ya hatimce shi da zobensa da kuma zoban manyan mutanensa, don kada wani yă canja yanayin Daniyel.
  • Da wayewar gari aka fitar da Daniyel ba rauni ko kaɗanDan 6:19–23
    Ayoyin
    Dan 6:19–23Gari yana wayewa, sai sarki ya tashi ya hanzarta zuwa ramin zakoki. Da ya yi kusa da ramin zakokin, sai ya kira Daniyel da muryar mai cike da damuwa ya ce, “Daniyel bawan Allah mai rai, ko Allahn nan naka wanda kake bauta wa kullum, ya iya cetonka daga zakoki?” Sai Daniyel ya amsa ya ce, “Ran sarki, yă daɗe! Allahna ya aiko da mala’ikansa, ya kuwa rufe bakunan zakoki. Ba su yi mini rauni ba, gama an same ni marar laifi ne a gabansa. Ban kuwa taɓa yin wani abu marar kyau a gabanka ba, ya sarki.” Sai sarki ya cika da murna ƙwarai, ya kuma yi umarni a ciro Daniyel daga ramin zakoki. Kuma da aka fito da Daniyel daga ramin, ba a sami wani rauni a jikinsa ba, domin ya dogara ga Allahnsa.
  • An jefa masu zarginsa ciki, zakoki kuma suka rinjaye su kafin su kai ƙasaDan 6:24
    Ayoyin
    Dan 6:24Sai sarki ya umarta, a kawo mutanen nan da suka yi wa Daniyel maƙarƙashiya, a tura su, da ’ya’yansu, da matansu cikin ramin zakoki. Kafin ma su kai ƙurewar ramin, sai zakoki suka hallaka su suka yayyage su, suka yi kaca-kaca da su.

Zakoki a sassaƙa

  • Kujerar sarautar Solomon: zaki kusa da kowane wurin sa hannu, zakoki goma sha biyu a matakai shida1Sar 10:19–20
    Ayoyin
    1Sar 10:19–20Kujera sarautar ta kasance da matakai shida, kuma bayanta tana da bisa mai kamannin gammo. A kowane gefen kujerar akwai wurin sa hannu, da kuma zaki tsaye kusa da kowannensu. Zakoki goma sha biyu suna tsaye a matakai shida, ɗaya a kowane gefen ƙarshen mataki. Babu ƙasar da an taɓa gina irin wannan kujerar mulki.
  • Zakoki, bijimai da kerubobi sun yi wa dakalan tagulla na haikali ado1Sar 7:29, 1Sar 7:36
    Ayoyin
    1Sar 7:29A bisa sassan tsakanin mahaɗan, akwai siffofin zakoki, bijimai da kuma kerubobi, suna a kan mahaɗan su ma. A sama da kuma ƙasan siffofin zakokin da na bijiman kuwa akwai hotunan furanni.
    1Sar 7:36Ya zāna siffofin kerubobi, zakoki da itatuwan dabino a saman abubuwan riƙewa da kuma a kan ɓangarorin, a kowane abin da ya ga akwai ɗan fili, ya zāna furanni.

Maganganu

  • “gara rayayyen kare da mataccen zaki!”M Had 9:4
    Ayoyin
    M Had 9:4Duk wanda yake da rai a wannan duniya ta rayayyu, yana sa zuciya, gara rayayyen kare da mataccen zaki!
  • Rago yakan ce, “Akwai zaki a waje!”K Mag 22:13, K Mag 26:13
    Ayoyin
    K Mag 22:13Rago kan ce, “Akwai zaki a waje!” Ko kuma “Za a kashe ni a tituna!”
    K Mag 26:13Rago yakan ce, “Akwai zaki a kan hanya, zaki mai faɗa yana yawo a tituna!”
  • “Fushin sarki yana kama da rurin zaki”K Mag 20:2
    Ayoyin
    K Mag 20:2Fushin sarki yana kama da rurin zaki; duk wanda ya sa shi fushi zai rasa ransa.
  • Shawulu da Yonatan: “Sun fi gaggafa sauri, sun fi zaki ƙarfi”2Sam 1:23
    Ayoyin
    2Sam 1:23Shawulu da Yonatan, a raye ƙaunatattu ne da kuma bansha’awa, a mace kuma ba su rabu ba. Sun fi gaggafa sauri, sun fi zaki ƙarfi.
  • Jarumawan Gad suna da fuskoki kamar na zakoki, suna kuma da sauri kamar bareyi1Tar 12:8
    Ayoyin
    1Tar 12:8Sai waɗansu mutanen Gad suka koma suna goyon bayan Dawuda suka kuma haɗa kai da shi a kagararsa a hamada. Su ƙwararrun mayaƙa ne, a shirye don yaƙi, kuma suna iya riƙe garkuwa da māshi. Fuskokinsu kamar fuskoki zakoki, kuma suna da sauri kamar bareyi a kan duwatsu.

Tushe

Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.