Bible Explorer

Littafi Mai Tsarki › Zabura › 129

SRK · Babi 129 / 150

Zabura 129

1Waƙar haurawa. Sun yi mini danniya ƙwarai tun ina ƙarami, bari Isra’ila yă ce,

2sun yi mini danniya ƙwarai tun ina ƙarami, amma ba su yi nasara a kaina ba.

3Manoma sun nome bayana suka yi kunyoyinsu da tsayi.

4Amma Ubangiji mai adalci ne; ya ’yantar da ni daga igiyoyin mugaye.

5Bari dukan waɗanda suke ƙin Sihiyona a juye da su baya da kunya.

6Bari su zama kamar ciyawa a kan rufi, wadda takan bushe kafin tă yi girma;

7da ita mai girbi ba ya iya cika hannuwansa, balle wanda yake tarawa yă cika hannuwansa.

8Kada masu wuce su ce, “Albarkar Ubangiji ta kasance a kanku; muna sa muku albarka a cikin sunan Ubangiji.”

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (SRK, 2020) · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. (ba a canja rubutu ba; an bar bayanan ƙasa da kanun labarai) · eBible.org