Bible Explorer

Bincika › Jigogi › Tumaki

Halitta

Tumaki a cikin Littafi Mai Tsarki

Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (38), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.

  • Habila makiyayin tumaki neFar 4:2
    Ayoyin
    Far 4:2Daga baya ta haifi ɗan’uwansa, ta kuma ba shi suna Habila. Sa’ad da suka yi girma sai Habila ya zama makiyayin tumaki, Kayinu kuwa ya zama manomi.
  • Habila ya kawo ’ya’yan fari na garkensaFar 4:4
    Ayoyin
    Far 4:4Amma Habila ya kawo mafi kyau daga ’ya’yan fari na garkensa. Ubangiji ya yi farin ciki da sadakar da Habila ya kawo,
  • Ibrahim ya sami rago da ƙahoninsa suka sarƙe a kurmiFar 22:13
    Ayoyin
    Far 22:13Ibrahim ya ɗaga ido, ya duba, sai ya ga rago da ƙahoninsa a kafe a wani ɗan kurmi. Sai Ibrahim ya tafi ya kamo ragon ya miƙa shi hadaya ta ƙonawa a maimakon ɗansa.
  • Makiyaya sukan mirgine dutse daga bakin rijiya su ba garkuna ruwaFar 29:2–3
    Ayoyin
    Far 29:2–3A can ya ga rijiya a jeji da garkuna uku na tumaki kwance kusa da ita, gama a wannan rijiya ce ake shayar da garkuna. Dutsen da ake rufe bakin rijiyar mai girma ne. Sa’ad da dukan garkuna suka taru a can, sai makiyayan su gungurar da dutsen daga bakin rijiyar su shayar da tumaki. Sa’an nan su mai da dutsen a wurinsa a bakin rijiya.
  • Rahila makiyayiya ce; Yaƙub ya ba tumakin mahaifinta ruwaFar 29:9–10
    Ayoyin
    Far 29:9–10Tun yana cikin magana da su, sai ga Rahila ta zo da tumakin mahaifinta, gama ita makiyayyiya ce. Sa’ad da Yaƙub ya ga Rahila ’yar Laban, ɗan’uwan mahaifiyarsa, da tumakin Laban, sai ya tafi ya gungurar da dutsen daga bakin rijiyar, ya kuma shayar da tumakin kawunsa.
  • ’Yan mata bakwai na Yetro sun ba garken ruwa, Musa kuma ya taimake suFit 2:16–17
    Ayoyin
    Fit 2:16–17To, fa, akwai wani firist na Midiyan, yana da ’ya’ya mata bakwai, suka zo su shayar da dabbobin mahaifinsu. Sai waɗansu makiyaya suka zo suka kore su, amma Musa ya tashi ya taimake su ya shayar da dabbobinsu.
  • Musa yana kiwon garken Yetro sa’ad da ya iso HorebFit 3:1
    Ayoyin
    Fit 3:1Ana nan wata rana Musa yana kiwon tumakin Yetro surukinsa, firist na Midiyan, sai ya bi da tumaki zuwa gefe mai nisa a cikin hamada, har ya zo Horeb, dutsen Allah.
  • Dawuda, ɗan autan, yana waje yana kiwon tumaki1Sam 16:11
    Ayoyin
    1Sam 16:11Don haka ya tambayi Yesse ya ce, “Su ke nan ’ya’yan maza da kake da su?” Yesse ya ce, “Har yanzu akwai ɗan autan, amma yana kiwon tumaki.” Sama’ila ya ce, “Ka aika yă zo, ba za mu zauna ba sai ya iso.”
  • Yaƙub a matsayin makiyayi: zafi da rana, sanyi da dare, asara ga namun jejiFar 31:38–40
    Ayoyin
    Far 31:38–40“Na kasance tare da kai shekaru ashirin. Tumakinka da awakinka ba su yi ɓarin ciki ba, ban kuwa ci raguna daga garkunanka ba. Ban kawo dabbobinka da namun jeji suka yayyaga; na kuma ɗauki hasarar ba? Ka nemi in biya dukan abin da aka sace da rana ko da dare. Yanayin da na kasance ke nan, da rana na sha zafin rana da dare kuma na sha sanyi, ga rashin barci.
  • Hakkin aikin Yaƙub: dabbobi masu ɗigo-ɗigo, masu tabo-tabo da masu baƙin launiFar 30:32
    Ayoyin
    Far 30:32Bari in ratsa cikin dukan garkunanka yau in fid da masu dabbare-dabbare da tumaki babare-babare, da kowane ɗan rago baƙi, da dabbare-dabbare da babare-babare na awaki daga ciki, waɗannan ne za su zama ladana.
  • Sandunansa da ya ɓare a wuraren shan ruwa da ’ya’ya masu dabbare-dabbareFar 30:37–39
    Ayoyin
    Far 30:37–39Yaƙub ya samo ɗanyen reshen itatuwan aduruku, da na katambiri, da na durumi, ya ɓare ya bar fararen cikin katakon rassan. Sa’an nan ya zuba ɓararre rassan cikin dukan kwamame na banruwa saboda su kasance a gaban garkunan sa’ad da suka zo shan ruwa. A sa’ad da garkunan suke barbara suka kuma zo shan ruwa, sai su yi barbara a gaban rassan. Sai kuwa su haifi ƙanana masu zāne dabbare-dabbare, ko babare-babare ko masu zāne-zāne.
  • Makiyaya suna tsaron garkunansu da dareLuk 2:8
    Ayoyin
    Luk 2:8Akwai makiyaya masu zama a fili kusa da wurin, suna tsaron garkunan tumakinsu da dare.
  • Tumaki sun san muryar makiyayi; yakan kira su da sunansuYoh 10:3–4
    Ayoyin
    Yoh 10:3–4Mai gadin yakan buɗe wa makiyayin ƙofa, tumakin kuma sukan saurari muryarsa. Yakan kira tumakinsa da suna, yă kuma fid da su waje. Sa’ad da ya fitar da dukan nasa waje, sai ya ja gabansu, tumakinsa kuma sukan bi shi domin sun san muryarsa.

Ulu, madara da sausaya

  • Madara daga garke, kitsen ’yan raguna da raguna daga BashanM Sh 32:14
    Ayoyin
    M Sh 32:14da kindirmo da madara daga shanu da tumaki da ƙibabbun tumaki da awaki, da zaɓaɓɓun ragunan Bashan da kuma ƙwayoyin alkama mafi kyau. Ka sha ruwan inabi ja wur mai kumfa.
  • Laban ya tafi sausayar tumakinsa sa’ad da Rahila ta ɗauki gumakanFar 31:19
    Ayoyin
    Far 31:19Sa’ad da Laban ya tafi don askin tumakinsa, sai Rahila ta sace gumakan gidan mahaifinta.
  • Yahuda ya haura wajen masu yin masa sausayar tumaki a TimnaFar 38:12–13
    Ayoyin
    Far 38:12–13Bayan an daɗe sai matar Yahuda, ’yar Shuwa ta rasu. Sa’ad da Yahuda ya gama makoki, sai ya haura zuwa Timna, zuwa wurin mutanen da suke askin tumakinsa, abokinsa Hira mutumin Adullam kuwa ya tafi tare da shi. Sa’ad da aka faɗa wa Tamar cewa, “Surukinki yana kan hanyarsa zuwa Timna don askin tumakinsa,”
  • Nabal yana da tumaki 3,000 da awaki 1,000, yana sausayarsu a Karmel1Sam 25:2
    Ayoyin
    1Sam 25:2A Mawon, akwai wani mutum wanda yake da dukiya a Karmel, mutumin mai arziki ne ƙwarai. Yana da awaki dubu ɗaya, da tumaki dubu uku waɗanda yake wa aski a Karmel.
  • Lokacin sausaya lokacin biki ne: na Nabal da na Absalom1Sam 25:11, 1Sam 25:36, 2Sam 13:23–24
    Ayoyin
    1Sam 25:11Don me zan ɗauki burodina da ruwana, da kuma naman da na yanka saboda masu yin wa tumakina aski in ba mutanen da ban ma san inda suka fito ba?”
    1Sam 25:36Da Abigiyel ta kai gida sai ta sami Nabal cikin gida yana ta fama biki iri na sarakuna. Yana ji wa ransa daɗi, ya kuma bugu tilis, saboda haka ba tă ce masa kome ba sai da gari ya waye.
    2Sam 13:23–24Bayan shekaru biyu, sa’ad da masu askin tumakin Absalom suna Ba’al-Hazor, kusa da iyakar Efraim, sai ya gayyaci dukan ’ya’yan sarki maza a can. Sai Absalom ya je wurin sarki ya ce, “Bawanka ya sa masu askin tumaki sun zo. Ko sarki da fadawansa za su zo tare da ni?”
  • Ulun farko da aka sausaya daga garke na firistoci neM Sh 18:3–4
    Ayoyin
    M Sh 18:3–4To, ga rabon da jama’a za su ba firistoci daga hadayun da suka miƙa ta bijimi ne, ko ta tunkiya ce; sai su ba firistoci kafaɗar, kumatun, da kuma kayan cikin. Za ku ba su nunan fari na hatsinku, da sabon ruwan inabinku, da manku, da kuma gashi na fari daga askin da kuka yi na tumakinku.
  • Ayuba ya ji wa matalauta ɗumi da ulun tumakinsaAyu 31:20
    Ayoyin
    Ayu 31:20kuma zuciyarsa ba tă gode mini ba don na yi masa sutura da gashin tumakina,

Garkuna a lambobi

  • Mesha sarkin Mowab ya biya ’yan raguna 100,000 da ulun raguna 100,0002Sar 3:4
    Ayoyin
    2Sar 3:4Mesha, sarkin Mowab yana kiwon tumaki, ya kuma zama tilas yă biya haraji ga sarkin Isra’ila. Saboda haka yakan ba da ’yan tumaki dubu ɗari, da kuma gashin raguna dubu ɗari.
  • Larabawa sun kawo wa Yehoshafat raguna 7,700 da awaki 7,7002Tar 17:11
    Ayoyin
    2Tar 17:11Waɗansu Filistiyawa suka kawo wa Yehoshafat kyautai da azurfa a matsayin haraji, Larabawa kuwa suka kawo masa garkuna, raguna dubu bakwai da ɗari bakwai da kuma awaki dubu bakwai da ɗari bakwai.
  • An ƙwace tumaki 250,000 daga Hagirawa1Tar 5:21
    Ayoyin
    1Tar 5:21Suka ƙwace dabbobin Hagirawa, raƙuma dubu hamsin, tumaki dubu ɗari biyu da hamsin da kuma jakuna dubu biyu. Suka kuma kame mutane dubu ɗari ɗaya,
  • Ayuba yana da tumaki 7,000, daga baya kuma 14,000Ayu 1:3, Ayu 42:12
    Ayoyin
    Ayu 1:3yana da tumaki dubu bakwai, raƙuma dubu uku, shanu ɗari biyar, da jakuna ɗari biyar, yana kuma da masu yi masa aiki da yawa. A ƙasar Gabas ba wani kamar sa.
    Ayu 42:12Ubangiji ya albarkaci ƙarshen Ayuba fiye da farkonsa. Yana da tumaki guda dubu goma sha huɗu, raƙuma guda dubu shida; shanun noma guda dubu da jakuna guda dubu.
  • Kedar sun yi cinikin ’yan raguna, raguna da awaki da TayaEzk 27:21
    Ayoyin
    Ezk 27:21“ ‘Mutanen Arabiya da dukan sarakunan Kedar abokan cinikinki ne; sun yi ciniki da ke suka sayi kayanki da ’yan raguna, da raguna, da awaki.
  • Solomon ya miƙa tumaki 120,000 a keɓewar haikali1Sar 8:63
    Ayoyin
    1Sar 8:63Solomon ya miƙa hadaya ta salama ga Ubangiji, shanu dubu ashirin da biyu, tumaki da awaki dubu ɗari da dubu ashirin. Ta haka sarki da dukan Isra’ilawa suka keɓe haikalin Ubangiji.

A cikin Doka

  • Tunkiyar da aka sace aka yanka ko aka sayar: a biya tumaki huɗuFit 22:1
    Ayoyin
    Fit 22:1“In mutum ya saci saniya ko tunkiya ya yanka, ko ya sayar, zai biya shanu biyar, a maimakon saniyar da ya sata, ko kuma tumaki huɗu, maimakon tunkiyar da ya sata.
  • Tunkiyar da namun jeji suka yayyaga: a kawo gawar shaidaFit 22:10, Fit 22:13
    Ayoyin
    Fit 22:10“In mutum ya ba da jaki, ko saniya, ko tunkiya, ko kowace dabba wa maƙwabcinsa ajiya, sai abin ya mutu, ko ya ji rauni, ko an ɗauke shi, in ba shaida,
    Fit 22:13In naman jeji ne ya kashe ta, zai nuna gawar don shaida, ba za a kuwa sa maƙwabcin yă biya abin da naman jeji ya kashe ba.

A Urushalima

  • Firistoci sun sāke gina Ƙofar TumakiNeh 3:1
    Ayoyin
    Neh 3:1Eliyashib babban firist da ’yan’uwansa firistoci suka tashi suka sāke gina Ƙofar Tumaki. Suka tsarkake ta, suka sa ƙofofinta a wurarensu, suka yi ginin har Hasumiyar Ɗari, wadda suka tsarkake, da kuma Hasumiyar Hananel.
  • Tafkin Betesda yana kusa da Ƙofar TumakiYoh 5:2
    Ayoyin
    Yoh 5:2To, a Urushalima akwai wani tafki kusa da Ƙofar Tumaki, wanda a yaren Arameyik ake kira Betesda an kuma kewaye shi da shirayi biyar.

Maganganu

  • Haƙora “kamar garken tumakin da ba a daɗe da yin musu sausaya ba, da suke haurawa daga inda aka yi musu wanka”WW 4:2
    Ayoyin
    WW 4:2Haƙoranki sun yi kamar garken tumakin da ba a daɗe da yin musu sausaya ba, da suke haurawa daga inda aka yi musu wanka. Kowanne yana tare da ɗan’uwansa; babu waninsu da yake shi kaɗai.
  • “Ka tabbata ka san lafiyar garken tumakinka”K Mag 27:23
    Ayoyin
    K Mag 27:23Ka tabbata ka san lafiyar garken tumakinka, ka mai da hankali ga garken shanunka;
  • “gashin raguna za su tanada maka tufafi”K Mag 27:26
    Ayoyin
    K Mag 27:26gashin raguna za su tanada maka tufafi, za ka iya sayi gonaki masu kyau da kuɗin awaki.
  • “kamar tunkiya a gaban masu askinta tana shiru”Ish 53:7
    Ayoyin
    Ish 53:7Aka wulaƙanta shi aka kuma yi masa azaba, duk da haka bai buɗe bakinsa ba; aka kai shi kamar ɗan rago zuwa wurin yanka, kuma kamar tunkiya a gaban masu askinta tana shiru, haka bai buɗe bakinsa ba.

Tushe

Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.