Gida › Bukukuwan shekarar coci › Kirsimeti
Bukukuwan shekarar coci
Kirsimeti
Haihuwar Yesu kamar yadda Matiyu da Luka suka faɗa, tare da annabcin Ishaya da farkon Bisharar Yohanna, gaba ɗaya. Cocin Yamma suna yin Kirsimeti a 25 ga Disamba; Cocin Orthodox na kalandar Julian a 7 ga Janairu.
Kwanaki
| Shekara | Cocin YammaKirsimeti | Cocin OrthodoxHaihuwar Kristi |
|---|---|---|
| 2026 | Disamba 25, 2026Juma’a | Janairu 7, 2027Alhamis |
| 2027 | Disamba 25, 2027Asabar | Janairu 7, 2028Juma’a |
| 2028 | Disamba 25, 2028Litinin | Janairu 7, 2029Lahadi |
| 2029 | Disamba 25, 2029Talata | Janairu 7, 2030Litinin |
| 2030 | Disamba 25, 2030Laraba | Janairu 7, 2031Talata |
Rana tana buɗe karatun ranar a kalandar Orthodox ko ta Katolika.
Kwanakin Orthodox bisa kalandar Julian, wadda Cocin Rasha, Sabiya da Jojiya da Dutsen Athos ke bi: bukukuwansu marasa canzawa suna faɗuwa kwana 13 daga baya a kalandar farar hula. Cocin kalandar sabuwa (Girka, Romania, Bulgaria da sauransu) suna yin Kirsimeti a 25 ga Disamba; ana lissafin Easter da kwanakin da suka dogara da ita iri ɗaya a kusan duk Cocin Orthodox.
Nassosin Littafi Mai Tsarki
Ishaya
2Mutanen da suke tafiya cikin duhu sun ga babban haske; a kan waɗanda suke zama a ƙasar inuwar mutuwa haske ya haskaka. 3Ka fadada al’umma ka kuma ƙara farin cikinsu; suna farin ciki a gabanka yadda mutane sukan yi murna a lokacin girbi, kamar yadda mutane sukan yi farin ciki sa’ad da suke raba ganima. 4Gama kamar yadda yake a kwanakin da aka ci Midiyan da yaƙi, kuka ji tsoro nauyin da ya nawaita musu, sandar da yake a kafaɗunsu, sandar masu zaluncinsu. 5Kowane takalmin jarumin da aka yi amfani da shi a yaƙi da kuma kowane rigar da ka naɗe cikin jini zai kasance an ƙone shi zai kuma zama abin hura wuta. 6Gama a gare mu an haifa mana yaro, a gare mu an ba da ɗa, gwamnati za tă kasance a kafaɗarsa. Za a ce da shi Mashawarci Mai Banmamaki, Allah Maɗaukaki Uban Madawwami, Sarkin Salama. 7Game da girmar gwamnatinsa da salama babu iyaka. Zai gāji sarki Dawuda, yă yi mulki a matsayinsa, zai kafa mulkinsa a kan adalci da gaskiya, tun daga yanzu har zuwa ƙarshen zamani. Ubangiji Maɗaukaki ne ya yi niyyar aikata wannan duka.
Mattiyu
18Ga yadda haihuwar Yesu Kiristi ta kasance. An yi alkawarin auren mahaifiyarsa Maryamu, ga Yusuf. Amma tun kafin su zama miji da mata, sai aka tarar Maryamu tana da ciki, ta wurin Ruhu Mai Tsarki. 19Yusuf mijinta, da yake shi mai adalci ne, bai so yă ba ta kunya, yă tone mata asiri a fili ba, sai ya yi tunani yă sake ta a ɓoye. 20Amma yana cikin wannan tunani, sai wani mala’ikan Ubangiji ya bayyana masa cikin mafarki ya ce, “Yusuf ɗan Dawuda, kada ka ji tsoron ɗaukan Maryamu zuwa gidanka a matsayin matarka, gama cikin nan nata, daga wurin Ruhu Mai Tsarki ne. 21Za tă haifi ɗa, za ka kuma sa masa suna Yesu, gama shi ne zai ceci mutanensa daga zunubansu.” 22Duk wannan ya faru ne, don a cika abin da Ubangiji ya faɗi ta bakin annabin cewa, 23“Ga shi budurwa za tă yi ciki, za tă haifi ɗa, kuma za a kira shi Immanuwel” (wanda yake nufin “Allah tare da mu”). 24Da Yusuf ya farka daga barci, sai ya bi umarnin mala’ikan Ubangiji, ya ɗauki Maryamu zuwa gida a matsayin matarsa. 25Amma bai kwana da ita ba, sai bayan da ta haifi ɗan. Ya kuwa sa masa suna Yesu.
Luka
1A waɗancan kwanaki, Kaisar Augustus ya ba da doka cewa ya kamata a yi ƙidaya a dukan masarautar Roma. 2(Wannan ce ƙidaya ta fari da aka yi a lokacin da Kwiriniyus yake gwamnar Suriya.) 3Sai kowa ya koma garinsa don a rubuta shi. 4Saboda haka Yusuf ma ya haura daga Nazaret a Galili zuwa Yahudiya, ya tafi Betlehem garin Dawuda, don shi daga gida da kuma zuriyar Dawuda ne. 5Ya tafi can don a rubuta shi tare da Maryamu, wadda aka yi masa alkawari zai aura, tana kuwa da ciki. 6Yayinda suke can, sai lokacin haihuwar jaririn ya yi, 7ta kuwa haifi ɗanta na fari. Ta nannaɗe shi a zane ta kuma kwantar da shi cikin wani kwami, don ba su sami ɗaki a masauƙi ba. 8Akwai makiyaya masu zama a fili kusa da wurin, suna tsaron garkunan tumakinsu da dare. 9Sai wani mala’ikan Ubangiji ya bayyana gare su, ɗaukakar Ubangiji kuma ta haskaka kewaye da su, suka kuwa tsorata ƙwarai. 10Amma mala’ikan ya ce musu, “Kada ku ji tsoro. Na kawo muku labari mai daɗi na farin ciki mai yawa ne wanda zai zama domin dukan mutane. 11Yau a birnin Dawuda an haifa muku Mai Ceto; shi ne Kiristi Ubangiji. 12Wannan zai zama alama a gare ku. Za ku tarar da jariri a nannaɗe a zane kwance a kwami.” 13Ba labari sai ga taron rundunar sama suka bayyana tare da mala’ikan, suna yabon Allah suna cewa, 14“Ɗaukaka ga Allah a can cikin sama, a duniya kuma salama ga mutane waɗanda tagomashinsa yake bisansu.” 15Da mala’ikun suka bar su, su suka koma sama, sai makiyayan suka ce wa juna, “Mu je Betlehem mu ga wannan abin da ya faru, wanda Ubangiji ya sanar mana.” 16Sai suka tafi da sauri, suka tarar da Maryamu da Yusuf, da kuma jaririn kwance a kwami. 17Sa’ad da suka gan shi, sai suka baza maganar da aka gaya musu game da yaron, 18duk kuwa waɗanda suka ji wannan, suka yi mamaki a kan abin da makiyayan suka faɗa. 19Amma Maryamu ta riƙe dukan waɗannan abubuwa ta kuma yi ta tunaninsu a zuciyarta. 20Makiyayan kuwa suka koma, suna ɗaukaka suna kuma yabon Allah saboda dukan abubuwan da suka ji, suka kuma gani, yadda aka gaya musu.
Mattiyu
1Bayan an haifi Yesu a Betlehem, a Yahudiya, a zamanin Sarki Hiridus, sai waɗansu Masana, daga gabas suka zo Urushalima 2suka yi tambaya suka ce, “Ina shi wanda aka haifa sarkin Yahudawa? Gama mun ga tauraronsa a gabas mun kuwa zo ne domin mu yi masa sujada.” 3Da Sarki Hiridus ya ji wannan, sai hankalinsa ya tashi haka ma na dukan Urushalima. 4Bayan ya kira dukan manyan firistoci da malaman dokoki na mutane wuri ɗaya, sai ya tambaye su inda za a haifi Kiristi. 5Suka amsa suka ce, “A Betlehem ne, cikin Yahudiya, gama haka annabin ya rubuta. 6“ ‘Amma ke Betlehem, a cikin ƙasar Yahuda, ba ke ce mafi ƙanƙanta a cikin masu mulki a Yahuda ba, gama daga cikinki mai mulki zai zo, wanda zai zama makiyayin mutanena Isra’ila.’” 7Sai Hiridus ya kira Masanan nan a ɓoye, yă gano daga wurinsu daidai lokacin da tauraron ya bayyana. 8Sai ya aike su Betlehem ya ce, “Ku je ku binciko a hankali game da yaron nan. Da kun same shi, sai ku kawo mini labari nan da nan, domin ni ma in je in yi masa sujada.” 9Bayan sun saurari sarki, sai suka kama hanyarsu, tauraron da suka gani a gabas kuwa yana tafe a gabansu, sai da ya kai inda yaron yake. 10Da suka ga tauraron, sai suka yi farin ciki ƙwarai. 11Suka shiga gidan, suka kuwa ga yaron tare da mahaifiyarsa Maryamu. Suka durƙusa har ƙasa, suka yi masa sujada. Sa’an nan suka kunce dukiyarsu, suka miƙa masa kyautai na zinariya da na turare da na mur. 12Bayan an gargaɗe su cikin mafarki kada su koma wurin Hiridus, sai suka koma ƙasarsu ta wata hanya dabam.
Yohanna
1Tun farar farawa akwai Kalma, Kalman kuwa yana nan tare da Allah, Kalman kuwa Allah ne. 2Yana nan tare da Allah tun farar farawa. 3Ta wurin Kalman ne aka halicci dukan abubuwa. In ba tare da shi ba, babu abin da aka yi wanda aka yi. 4A cikinsa rai ya kasance, wannan rai kuwa shi ne hasken mutane. 5Hasken yana haskakawa cikin duhu, amma duhun bai rinjaye shi ba. 6Akwai wani mutumin da aka aiko daga Allah; mai suna Yohanna. 7Ya zo a matsayin mai shaida domin yă ba da shaida game da wannan haske, don ta wurinsa dukan mutane su ba da gaskiya. 8Shi kansa ba shi ne hasken ba; sai dai ya zo a matsayin shaida ne kaɗai ga hasken. 9Haske na gaskiya da yake ba da haske ga kowane mutum mai shigowa duniya. 10Yana a duniya, kuma ko da yake an yi duniya ta wurinsa ne, duniya ba tă gane shi ba. 11Ya zo wurin abin da yake nasa, amma nasa ɗin ba su karɓe shi ba. 12Duk da haka dukan waɗanda suka karɓe shi, ga waɗanda suka gaskata a sunansa, ya ba su iko su zama ’ya’yan Allah 13’ya’yan da aka haifa ba bisa hanyar ’yan adam, ko shawarar mutum ko nufin namiji ba, sai dai haifaffu bisa ga nufin Allah. 14Kalman ya zama mutum, ya kuwa zauna a cikinmu. Muka ga ɗaukakarsa, ɗaukaka ta wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaici, wanda ya zo daga wurin Uba, cike da alheri da gaskiya.
A zane-zane
Sujadar MakiyayaGiorgione · 1505/1510
Sujadar MasanaFra Angelico da Fra Filippo Lippi · kusan 1440/1460
Tauraro Ya Jagoranci MasanaGustave Doré · 1866
Haihuwar YesuDürer · kusan 1502–3
Masana Suna Yi wa Yesu SujadaDürer · kusan 1501–1503
Haihuwar YesuDürer · 1504
Masana Suna Yi wa Yesu SujadaLucas van Leyden · 1513
Shafi Ɗaya da Aka Yanke daga Littafin Linjila: Haihuwar Yesu (gaba)Mai zane da ba a san sunansa ba, Helmarshausen · kusan 1190
Albishir ga Makiyaya (Ms. 125, fol. 7, daga Littafin Rubutun Hannu na Irmengard)Mai zane ɗan Jamus da ba a san sunansa ba · bayan 1053
Masu Hikima Suna Yi wa Jaririn Sujada (Ms. Ludwig VII 1, fol. 25v, daga Littafin Albarka)Mai zane da ba a san sunansa ba, Regensburg · kusan 1030–1040
Mala’ika Yana Bayyana ga MakiyayaRembrandt · 1634
Makiyaya Suna Yi wa Yesu Sujada: da FitilaRembrandt · kusan 1654
Wasu bukukuwa
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi