Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Bukukuwan shekarar coci › Azumin Lent

Bukukuwan shekarar coci

Azumin Lent

Kwana arba’in na azumi kafin Easter: a cocin Yamma tun Laraba ta Toka, a Cocin Orthodox tun Litinin Mai Tsabta. Azumin Yesu a jeji da maganarsa game da sadaka, addu’a da azumi, gaba ɗaya.

Kwanaki

ShekaraCocin YammaLaraba ta TokaCocin OrthodoxLitinin Mai Tsabta
2027Faburairu 10, 2027LarabaMaris 15, 2027Litinin
2028Maris 1, 2028LarabaFaburairu 28, 2028Litinin
2029Faburairu 14, 2029LarabaFaburairu 19, 2029Litinin
2030Maris 6, 2030LarabaMaris 11, 2030Litinin
2031Faburairu 26, 2031LarabaFaburairu 24, 2031Litinin

Rana tana buɗe karatun ranar a kalandar Orthodox ko ta Katolika.

Kwanakin Orthodox bisa kalandar Julian, wadda Cocin Rasha, Sabiya da Jojiya da Dutsen Athos ke bi: bukukuwansu marasa canzawa suna faɗuwa kwana 13 daga baya a kalandar farar hula. Cocin kalandar sabuwa (Girka, Romania, Bulgaria da sauransu) suna yin Kirsimeti a 25 ga Disamba; ana lissafin Easter da kwanakin da suka dogara da ita iri ɗaya a kusan duk Cocin Orthodox.

Nassosin Littafi Mai Tsarki

Yowel

Yow 2:12–17

12“Ko yanzu”, in ji Ubangiji, “Ku juyo gare ni da dukan zuciyarku, da azumi da kuka da makoki.” 13Ku kyakkece zuciyarku ba rigunanku ba. Ku juyo ga Ubangiji Allahnku, gama shi mai alheri ne mai tausayi kuma mai jinkirin fushi da yawan ƙauna, yakan kuma janye daga aika da bala’i. 14Wa ya sani? Ko zai juya yă kuma ji tausayi yă sa mana albarka ta wurin hadaya ta gari da hadaya ta sha wa Ubangiji Allahnku. 15A busa ƙaho a Sihiyona, a yi shelar azumi mai tsarki, a kira tsarkakan taro. 16A tattara mutane; ku tsarkake taron; ku kawo dattawa wuri ɗaya; ku kuma tara yara, da waɗanda suke shan mama. Bari ango yă bar ɗakinsa amarya kuma lolokinta. 17Bari firistocin da suke yin hidima a gaban Ubangiji, su yi kuka tsakanin filin haikali da bagade. Bari su ce, “Ka cece mutanenka, ya Ubangiji. Kada ka bar gādonka yă zama abin dariya, da abin ba’a a cikin al’ummai. Me zai sa a ce a cikin mutane, ‘Ina Allahnsu yake?’ ”

Mattiyu

Mat 4:1–11

1Sa’an nan Ruhu ya kai Yesu cikin hamada don Iblis yă gwada shi. 2Bayan ya yi azumi yini arba’in da kuma dare arba’in, sai ya ji yunwa. 3Sai mai gwajin ya zo wurinsa ya ce, “In kai Ɗan Allah ne, ka ce wa duwatsun nan su zama burodi.” 4Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake cewa, ‘Ba da abinci kaɗai mutum yake rayuwa ba, sai dai da kowace kalmar da take fitowa daga bakin Allah.’ ” 5Sai Iblis ya kai shi birni mai tsarki, ya kai shi can wuri mafi tsayi duka na haikali. 6Ya ce, “In kai Ɗan Allah ne, yi tsalle ka sauka ƙasa. Gama a rubuce yake, “ ‘Zai umarci mala’ikunsa game da kai, za su tallafe ka da hannuwansu, don kada ka buga ƙafarka a kan dutse.’” 7Yesu ya amsa masa ya ce, “A rubuce yake kuma cewa, ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’ ” 8Har wa yau, Iblis ya kai shi bisa wani dutse mai tsawo sosai, ya nunnuna masa dukan mulkokin duniya da darajarsu. 9Ya ce, “Zan ba ka dukan wannan, in za ka durƙusa ka yi mini sujada.” 10Sai Yesu ya ce masa, “Rabu da ni, Shaiɗan! Gama a rubuce yake, ‘Yi wa Ubangiji Allahnka sujada, shi kaɗai kuma za ka bauta wa.’ ” 11Sa’an nan Iblis ya bar shi, mala’iku kuwa suka zo suka yi masa hidima.

Mattiyu

Mat 6:1–6, 16–21

1“Ku yi hankali kada ku nuna ‘ayyukanku na adalci’ a gaban mutane, don su gani. In kuka yi haka, ba za ku sami lada daga wurin Ubanku da yake cikin sama ba. 2“Saboda haka sa’ad da kake ba wa masu bukata taimako, kada ka yi shelarsa, yadda munafukai suke yi a majami’u da kuma kan tituna, don mutane su yabe su. Gaskiya nake gaya muku, sun riga sun sami ladarsu cikakke. 3Amma sa’ad da kake ba wa masu bukata taimako, kada ka yarda hannun hagunka yă ma san abin da hannun damarka yake yi, 4don bayarwarka ta zama a ɓoye. Ubanka kuwa mai ganin abin da ake yi a ɓoye, zai sāka maka. 5“Sa’ad da kuma kuke addu’a, kada ku zama kamar munafukai, gama sun cika son yin addu’a a tsaye a cikin majami’u da kuma a bakin titi, don mutane su gan su. Gaskiya nake gaya muku, sun riga sun sami ladarsu cikakke. 6Amma sa’ad da kake addu’a, sai ka shiga ɗakinka, ka rufe ƙofa, ka yi addu’a ga Ubanka wanda ba a gani. Ubanka kuwa mai ganin abin da ake yi a ɓoye, zai sāka maka. 16“Sa’ad da kuma kuna azumi, kada ku ɓata fuska, yadda munafukai suke yi. Sukan ɓata fuskokinsu domin su nuna wa mutane cewa suna azumi. Gaskiya nake gaya muku, sun riga sun sami ladarsu cikakke. 17Amma sa’ad da kana azumi, ka shafa wa kanka mai, ka wanke fuskarka, 18domin kada mutane su ga alama cewa kana azumi, sai dai Ubanka kaɗai wanda ba a gani; Ubanka kuwa mai ganin abin da ake yi a ɓoye, zai sāka maka. 19“Kada ku yi wa kanku ajiyar dukiya a duniya, inda asu da tsatsa suke ɓatawa, inda kuma ɓarayi sukan fasa, su yi sata. 20Amma ku yi wa kanku ajiyar dukiya a sama, inda ba tsatsa da asu da za su ɓata su, inda kuma ba ɓarayin da za su fasa, su yi sata. 21Gama inda dukiyarka take, a nan ne fa zuciyarka za tă kasance.

A zane-zane

Duk ayyuka

Wasu bukukuwa

Bukukuwan shekarar coci

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi