Gida › Bukukuwan shekarar coci › Fentakos
Bukukuwan shekarar coci
Fentakos
Kwana hamsin bayan Easter: saukowar Ruhu Mai Tsarki a kan almajirai a Urushalima, kamar yadda littafin Ayyukan Manzanni ya faɗa, tare da annabcin Yowel da Bitrus ya kawo da maganar Yesu a Bisharar Yohanna.
Kwanaki
| Shekara | Cocin YammaFentekos | Cocin OrthodoxFentekos |
|---|---|---|
| 2027 | Mayu 16, 2027Lahadi | Yuni 20, 2027Lahadi |
| 2028 | Yuni 4, 2028Lahadi | Yuni 4, 2028Lahadi |
| 2029 | Mayu 20, 2029Lahadi | Mayu 27, 2029Lahadi |
| 2030 | Yuni 9, 2030Lahadi | Yuni 16, 2030Lahadi |
| 2031 | Yuni 1, 2031Lahadi | Yuni 1, 2031Lahadi |
Rana tana buɗe karatun ranar a kalandar Orthodox ko ta Katolika.
Kwanakin Orthodox bisa kalandar Julian, wadda Cocin Rasha, Sabiya da Jojiya da Dutsen Athos ke bi: bukukuwansu marasa canzawa suna faɗuwa kwana 13 daga baya a kalandar farar hula. Cocin kalandar sabuwa (Girka, Romania, Bulgaria da sauransu) suna yin Kirsimeti a 25 ga Disamba; ana lissafin Easter da kwanakin da suka dogara da ita iri ɗaya a kusan duk Cocin Orthodox.
Nassosin Littafi Mai Tsarki
Ayyukan Manzanni
1Da ranar Fentekos ta yi, dukansu suna tare wuri ɗaya. 2Ba zato ba tsammani sai aka ji motsi kamar ta babbar iska tana hurowa daga sama ta kuma cika dukan gidan da suke zaune. 3Suka ga wani abin da ya yi kama da harsunan wuta, suka rarrabu suna kuma sassauka a kan kowannensu. 4Dukansu kuwa suka cika da Ruhu Mai Tsarki suka kuma fara magana da waɗansu harsuna yadda Ruhu ya sa suka iya. 5To, a Urushalima akwai Yahudawa masu tsoron Allah, daga kowace ƙasa a duniya. 6Da suka ji wannan motsi, taro ya haɗu wuri ɗaya a ruɗe, domin kowannensu ya ji suna magana da yarensa. 7Cike da mamaki, suka yi tambaya suna cewa, “Ashe, duk waɗannan mutane masu magana ba Galiliyawa ba ne? 8To, yaya kowannenmu yana ji suna yarensa? 9Fartiyawa, Medes da Elamawa; mazaunan Mesofotamiya, Yahudiya da Kaffadokiya, Fontus da Asiya, 10Firjiya da Famfiliya, Masar da sassa Libiya kusa da Sairin; baƙi daga Roma 11(Yahudawa da kuma waɗanda suka tuba suka shiga Yahudanci); Kiretawa da Larabawa, mun ji su suna shelar abubuwan banmamaki na Allah da yarenmu!” 12A ruɗe kuma cike da mamaki, suka tambayi junansu cewa, “Mene ne wannan yake nufi?” 13Duk da haka waɗansu suka yi musu ba’a suka ce, “Sun yi tatil da ruwan inabi ne.” 14Sai Bitrus ya miƙe tsaye tare da Sha Ɗayan nan, ya ɗaga muryarsa ya yi wa taron jawabi ya ce, “’Yan’uwana Yahudawa da dukanku da kuke zama cikin Urushalima, bari in bayyana muku wannan, ku saurara da kyau ga abin da zan faɗa. 15Waɗannan mutane ba su bugu ba, kamar yadda kuka ɗauka. Yanzu ƙarfe tara na safe ne kawai! 16A’a, ai, abin da aka yi magana ta bakin annabi Yowel ke nan cewa, 17“Allah ya ce, ‘A kwanakin ƙarshe, zan zubo Ruhuna bisa dukan mutane. ’Ya’yanku maza da mata za su yi annabci, samarinku za su ga wahayoyi, dattawanku kuma za su yi mafarkai. 18Kai, har ma a kan bayina, maza da mata, zan zubo Ruhuna a waɗancan kwanaki, za su kuwa yi annabci. 19Zan nuna abubuwan banmamaki a sararin sama da alamu a nan ƙasa, jini da wuta da kuma hauhawan hayaƙi. 20Za a mai da rana duhu, wata kuma ya zama jini, kafin zuwa rana mai girma da kuma ta ɗaukaka ta Ubangiji. 21Kuma duk wanda ya kira bisa sunan Ubangiji zai sami ceto.’
Yowel
28“Daga baya kuma, zan zuba Ruhuna a bisan dukan mutane. ’Ya’yanku maza da mata za su yi annabci, tsofaffinku za su yi mafarkai, matasanku za su ga wahayoyi. 29Har ma a bisan bayina, maza da mata, zan zuba Ruhuna a kwanakin nan. 30Zan nuna abubuwan banmamaki a cikin sammai da kuma a kan duniya, za a ga jini da wuta da murtukewar hayaƙi. 31Rana za tă duhunta wata kuma yă zama jini kafin isowar babbar ranan nan mai banrazana ta Ubangiji. 32Amma dukan waɗanda suka nemi Ubangiji za su tsira. Kamar yadda Ubangiji ya ce, gama a Dutsen Sihiyona da Urushalima akwai ceto, a cikin waɗannan da Ubangiji ya kira.
Yohanna
37A rana ta ƙarshe kuma mafi girma ta Bikin, Yesu ya tsaya ya yi magana da babbar murya ya ce, “Duk mai jin ƙishirwa, yă zo wurina yă sha. 38Duk wanda ya gaskata da ni, kamar yadda Nassi ya ce, kogunan ruwa masu rai za su gudana daga cikinsa.” 39Da wannan yana nufin Ruhu ke nan, wanda waɗanda suka gaskata da shi za su karɓa daga baya. Har yă zuwa wannan lokaci ba a ba da Ruhu ba tukuna, da yake ba a riga an ɗaukaka Yesu ba.
Yohanna
19Da Yamman ranar farko ta mako, sa’ad da almajiran suna tare, ƙofofi kuma suna a kulle saboda tsoron Yahudawa, sai ga Yesu ya zo ya tsaya a tsakiyarsu ya ce, “Salama tă kasance tare da ku!” 20Bayan ya faɗa haka, sai ya nuna musu hannuwansa da gefensa. Sai almajiran suka yi farin ciki ƙwarai da suka ga Ubangiji. 21Sai Yesu ya sāke ce musu, “Salama tă kasance tare da ku! Kamar yadda Uba ya aiko ni, haka ni ma ina aikan ku.” 22Da wannan sai ya hura musu numfashinsa ya ce, “Ku karɓi Ruhu Mai Tsarki. 23Duk wanda kuka gafarta wa zunubansa, an gafarta masa ke nan. Duk wanda ba ku gafarta wa ba kuwa, ba a gafarta masa ba ke nan.”
A zane-zane
FentekosDürer · kusan 1509/1510?
Saukowar Ruhu Mai TsarkiGustave Doré · 1866
Manzanni Suna Wa’aziGustave Doré · 1866
FentakosMai zane ɗan Jamus · tsakiyar ƙarni na 13
Yesu Yana Bayyana ga ManzanniRembrandt · 1656
Bayyanar Kiristi a Ɗakin Sama (Apparition du Christ au cénacle)James Tissot · 1886–1894
Wasu bukukuwa
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi