Gida › Bukukuwan shekarar coci › Makon Mai Tsarki da Easter
Bukukuwan shekarar coci
Makon Mai Tsarki da Easter
Makon Mai Tsarki daga Lahadin Ganyen Dabino zuwa Easter: shigowa Urushalima, Jibin Ƙarshe, Shan wahala da Tashin matattu da kalmomin Bisharu da kansu, abubuwan da suka faru a makon sa’a bayan sa’a, da kwanakin Easter ta Yamma da ta Orthodox na shekaru masu zuwa.
Kwanaki
| Shekara | Cocin YammaLahadin Ista | Cocin OrthodoxIsta |
|---|---|---|
| 2027 | Maris 28, 2027LahadiLahadin Dabino: Maris 21, 2027Juma’a Mai Tsarki: Maris 26, 2027 | Mayu 2, 2027LahadiLahadin Dabino: Afirilu 25, 2027Babbar Juma’a: Afirilu 30, 2027 |
| 2028 | Afirilu 16, 2028LahadiLahadin Dabino: Afirilu 9, 2028Juma’a Mai Tsarki: Afirilu 14, 2028 | Afirilu 16, 2028LahadiLahadin Dabino: Afirilu 9, 2028Babbar Juma’a: Afirilu 14, 2028 |
| 2029 | Afirilu 1, 2029LahadiLahadin Dabino: Maris 25, 2029Juma’a Mai Tsarki: Maris 30, 2029 | Afirilu 8, 2029LahadiLahadin Dabino: Afirilu 1, 2029Babbar Juma’a: Afirilu 6, 2029 |
| 2030 | Afirilu 21, 2030LahadiLahadin Dabino: Afirilu 14, 2030Juma’a Mai Tsarki: Afirilu 19, 2030 | Afirilu 28, 2030LahadiLahadin Dabino: Afirilu 21, 2030Babbar Juma’a: Afirilu 26, 2030 |
| 2031 | Afirilu 13, 2031LahadiLahadin Dabino: Afirilu 6, 2031Juma’a Mai Tsarki: Afirilu 11, 2031 | Afirilu 13, 2031LahadiLahadin Dabino: Afirilu 6, 2031Babbar Juma’a: Afirilu 11, 2031 |
Rana tana buɗe karatun ranar a kalandar Orthodox ko ta Katolika.
Kwanakin Orthodox bisa kalandar Julian, wadda Cocin Rasha, Sabiya da Jojiya da Dutsen Athos ke bi: bukukuwansu marasa canzawa suna faɗuwa kwana 13 daga baya a kalandar farar hula. Cocin kalandar sabuwa (Girka, Romania, Bulgaria da sauransu) suna yin Kirsimeti a 25 ga Disamba; ana lissafin Easter da kwanakin da suka dogara da ita iri ɗaya a kusan duk Cocin Orthodox.
Nassosin Littafi Mai Tsarki
Mattiyu
1Da suka yi kusa da Urushalima suka kuma kai Betfaji da yake kan Dutsen Zaitun, sai Yesu ya aiki almajirai biyu, 2yana ce musu, “Ku je ƙauyen da yake gabanku, nan take za ku ga wata jaka a daure tare da ɗanta kusa da ita, a can. Ku kunce su ku kawo mini. 3In wani ya yi muku wata magana, ku ce masa Ubangiji yana bukatarsu, zai kuwa mai da su nan da nan.” 4Wannan ya faru ne don a cika abin da aka faɗa ta bakin annabin cewa, 5“Ku ce wa Diyar Sihiyona, ‘Duba, sarkinki yana zuwa gare ki, mai tawali’u yana a kan jaki, a kan aholaki, ɗan jaki.’ ” 6Almajiran suka tafi suka yi kamar yadda Yesu ya umarce su. 7Suka kawo jakar da ɗanta, suka shimfiɗa mayafansu a kansu, Yesu kuma ya zauna a kansu. 8Wani babban taron mutane suka shimfiɗa mayafansu a kan hanya, yayinda waɗansu suka sassari rassan itatuwa suka shisshimfiɗa a kan hanya. 9Taron mutanen da suke gabansa da kuma waɗanda suke binsa a baya suka yi ihu suna cewa, “Hosanna ga Ɗan Dawuda!” “Mai albarka ne wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji!” “Hosanna a cikin sama!” 10Sa’ad da Yesu ya shiga Urushalima, dukan birnin ya ruɗe, ana ta tambaya, “Wane ne wannan?” 11Taron mutane suka amsa, “Wannan shi ne Yesu, annabin nan daga Nazaret a Galili.”
Yohanna
1Ana gab da Bikin Ƙetarewa. Yesu kuwa ya san cewa lokaci ya yi da zai bar wannan duniya, yă koma wurin Uba. Da yake ya ƙaunaci waɗanda suke nasa a duniya, yanzu kuwa ya nuna musu cikakkiyar ƙaunarsa. 2Ana cikin cin abincin yamma, Iblis kuwa ya riga ya zuga Yahuda Iskariyot, ɗan Siman yă bashe Yesu. 3Yesu kuwa ya san cewa, Uba ya sa dukan abubuwa a ƙarƙashin ikonsa, ya kuma san cewa daga Allah ya zo, zai kuma koma wurin Allah; 4saboda haka ya tashi daga cin abincin, ya tuɓe rigarsa ta waje, ya ɗaura tawul a ƙugunsa. 5Bayan haka, sai ya zuba ruwa a cikin kwano, sa’an nan ya fara wanke ƙafafun almajiransa, yana sharewa da tawul wanda ya ɗaura. 6Ya zo kan Siman Bitrus, wanda ya ce masa, “Ubangiji, kai za ka wanke ƙafafuna?” 7Yesu ya amsa ya ce, “Yanzu ba ka fahimci abin da nake yi ba, amma nan gaba za ka gane.” 8Sai Bitrus ya ce, “Faufau, ba za ka taɓa wanke ƙafafuna ba.” Yesu ya amsa ya ce, “Sai na wanke ka, in ba haka ba, ba ka da rabo a gare ni.” 9Sai Siman Bitrus ya ce, “To, Ubangiji, ba ƙafafuna kaɗai ba har ma da hannuwana da kaina kuma!” 10Yesu ya amsa ya ce, “Wanda ya riga ya yi wanka yana bukata yă wanke ƙafafunsa ne kawai; dukan jikinsa yana da tsabta. Ku kuwa kuna da tsabta, ko da yake ba kowannenku ba.” 11Gama ya san wanda zai bashe shi, shi ya sa ya ce, “Ba kowa ba ne yake da tsabta.” 12Da ya gama wanke ƙafafunsu, sai ya sa tufafinsa ya koma wurin zamansa. Ya tambaye su ya ce, “Kun fahimci abin da na yi muku? 13Kuna ce da ni ‘Malam’ da kuma ‘Ubangiji,’ daidai ne kuwa, gama haka nake. 14Da yake ni da nake Ubangijinku da kuma Malaminku, na wanke ƙafafunku, haka ku ma ya kamata ku wanke ƙafafun juna. 15Na ba ku misali domin ku yi yadda na yi muku.
Mattiyu
17A rana ta fari ta Bikin Burodi Marar Yisti, sai almajiran suka zo wurin Yesu suka yi tambaya suka ce, “Ina kake so mu je mu shirya maka wurin da za ka ci Bikin Ƙetarewa?” 18Ya amsa ya ce, “Ku shiga gari wurin wāne, ku ce masa, ‘Malam ya ce, lokacina ya yi kusa. Zan ci Bikin Ƙetarewa tare da almajiraina a gidanka.’ ” 19Saboda haka almajiran suka yi yadda Yesu ya umarce su, suka kuwa shirya Bikin Ƙetarewa. 20Da yamma ta yi, sai Yesu ya zauna don cin abinci tare da Sha Biyun. 21Yayinda suke cin abinci, sai ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, ɗayanku zai bashe ni.” 22Suka yi baƙin ciki ƙwarai, suka fara ce masa da ɗaya-ɗaya, “Gaskiya nake gaya muku, ɗayanku zai bashe ni.” 23Yesu ya amsa ya ce, “Wanda ya sa hannunsa a kwano tare da ni ne, zai bashe ni. 24Ɗan Mutum zai tafi kamar yadda aka rubuta game da shi. Amma kaiton mutumin da zai bashe Ɗan Mutum! Da ma ba a haifi mutumin nan ba, da ya fi masa.” 25Sa’an nan Yahuda, wanda zai bashe shi ya ce, “Tabbatacce ba ni ba ne, ko, Rabbi?” Yesu ya amsa ya ce, “I, kai ma ka fada.” 26Yayinda suke cikin cin abinci, Yesu ya ɗauki burodi, ya yi godiya ya kuma kakkarya, ya ba wa almajiransa yana cewa, “Ku karɓa ku ci; wannan jikina ne.” 27Sa’an nan ya ɗauki kwaf, ya yi godiya, ya kuma ba su, yana cewa, “Ku shassha daga cikinsa, dukanku. 28Wannan jinina ne na sabon alkawari, wanda aka zubar saboda mutane da yawa, don gafarar zunubai. 29Ina gaya muku, ba zan ƙara shan ruwan inabin nan ba har sai ranar da zan sha shi sabo tare da ku a mulkin Ubana.” 30Da suka rera waƙa, sai suka fita, suka tafi Dutsen Zaitun.
Yohanna
1Da ya gama addu’a, sai Yesu ya fita tare da almajiransa suka haye Kwarin Kidron. A wancan ƙetaren kuwa akwai lambun zaitun, da shi da almajiransa suka shiga ciki. 2To, Yahuda, wanda ya bashe shi, ya san wurin, domin Yesu ya sha zuwa wurin da almajiransa. 3Saboda haka Yahuda ya zo cikin lambun, yana jagoranta ƙungiyar sojoji da waɗansu ma’aikata daga wurin manyan firistoci da Farisiyawa. Suna riƙe da toci, fitilu da kuma makamai. 4Yesu kuwa, sane da duk abin da zai same shi, ya fito ya tambaye, su ya ce, “Wa kuke nema?” 5Suka amsa suka ce, “Yesu Banazare.” Yesu ya ce, “Ni ne shi.” (Yahuda kuwa wanda ya bashe shi yana nan tsaye tare da su.) 6Da Yesu ya ce, “Ni ne shi,” sai suka ja da baya suka fāɗi a ƙasa. 7Sai ya sāke tambayar su ya ce, “Wa kuke nema?” Suka ce, “Yesu Banazare.” 8Yesu ya amsa ya ce, “Ai, na gaya muku ni ne shi. In kuma ni ne kuke nema, to, sai ku bar waɗannan su tafi.” 9Wannan ya faru ne don a cika kalmomin da ya yi cewa, “Ban yar da ko ɗaya daga cikin waɗanda ka ba ni ba.” 10Sai Siman Bitrus, wanda yake da takobi, ya zāre, ya kai wa bawan babban firist sara, ya ɗauke masa kunnensa na dama (Sunan bawan kuwa Malkus ne.) 11Sai Yesu ya umarce Bitrus ya ce, “Mai da takobinka kube! Ba zan sha kwaf da Uba ya ba ni ba?” 12Sai ƙungiyar soja tare da shugaban sojanta da kuma ma’aikatan Yahudawa suka kama Yesu. Suka daure shi 13sa’an nan suka kawo shi da farko wurin Annas, wanda yake surukin Kayifas, babban firist a shekaran nan. 14Kayifas ne wanda ya shawarci Yahudawa cewa zai fi kyau mutum ɗaya yă mutu saboda mutane. 15Siman Bitrus da kuma wani almajiri suna bin Yesu. Domin almajirin nan sananne ne ga babban firist, sai ya shiga tare da Yesu a filin gidan babban firist ɗin, 16Bitrus kuwa ya dakata a waje a bakin ƙofa. Almajirin nan da yake sananne ga babban firist, ya dawo ya yi magana da yarinyar mai aiki a can, ya kuma shigo da Bitrus. 17Yarinyar da take bakin ƙofar ta ce wa Bitrus, “Kai ba ɗaya ne daga cikin almajiran mutumin nan ba ne?” Bitrus ya amsa ya ce, “A’a, ba na ciki.” 18To, ana sanyi, bayi da ma’aikatan suna tsattsaye kewaye da wutar da suka hura don su ji ɗumi. Bitrus ma yana tsaye tare da su, yana jin ɗumi. 19Ana cikin haka, sai babban firist ya tuhumi Yesu game da almajiransa da kuma koyarwarsa. 20Yesu ya amsa ya ce, “Ai, na yi wa duniya magana a fili. Na kuma sha yin koyarwa a majami’u ko kuma a haikali inda Yahudawa duka sukan taru. Ban taɓa faɗin kome a ɓoye ba. 21Don me kake tuhumata? Ka tambayi waɗanda suka ji ni. Ba shakka, sun san abin da na faɗa.” 22Da Yesu ya faɗa haka, sai ɗaya daga cikin ma’aikatan da yake tsaye kusa ya mare shi a fuska ya ce, “Haka za ka amsa wa babban firist?” 23Yesu ya amsa ya ce, “In na faɗi abin da ba daidai ba, ka nuna abin da ba daidai ba. Amma in gaskiya na faɗa, don me ka mare ni?” 24Sai Annas ya aika da shi, a daure, wurin Kayifas babban firist. 25Da Siman Bitrus yana nan tsaye yana jin ɗumin wuta, sai aka tambaye shi, “Kai, kai ma ba ɗaya daga cikin almajiransa ba ne?” Sai ya yi mūsu, yana cewa, “Sam, ba na ciki.” 26Sai wani daga cikin bayin babban firist dangin wanda Bitrus ya sare wa kunne, ya tambaya shi ya ce, “Kana tsammani ban gan ka tare da shi a gonar zaitun ba?” 27Bitrus ya sāke yin mūsu, nan take kuwa zakara ya yi cara. 28Sa’an nan Yahudawa suka fitar da Yesu daga wurin Kayifas zuwa fadar gwamnar Roma. A yanzu dai, safiya ta yi, don gudu kada su ƙazantar da kansu Yahudawa ba su shiga cikin fadar ba; sun so su iya ci Bikin Ƙetarewa. 29Saboda haka Bilatus ya fito wajensu ya ce, “Wace ƙara kuke kawowa game da mutumin nan?” 30Suka amsa suka ce, “Da a ce shi ba mai laifi ba ne, ai, da ba mu bashe shi gare ka ba.” 31Bilatus ya ce, “Ku tafi da shi da kanku mana, ku hukunta shi bisa ga dokarku.” Sai Yahudawa suka ƙi suka ce, “Ba mu da ikon yanke wa wani hukuncin kisa.” 32Wannan kuwa ya faru ne don a cika kalmomin da Yesu ya yi da suka nuna irin mutuwar da zai yi. 33Sai Bilatus ya koma cikin fada, ya kira Yesu ya tambaye shi, “Shin, kai ne sarkin Yahudawa?” 34Yesu ya yi tambaya ya ce, “Wannan ra’ayin kanka ne, ko waɗansu ne suka yi maka magana game da ni?” 35Bilatus ya amsa ya ce, “Ni mutumin Yahuda ne? Ai, mutanenka ne da kuma manyan firistoci suka bashe ka gare ni. Me ka yi?” 36Yesu ya ce, “Mulkina ba na duniyan nan ba ne. Da na duniyan nan ne da bayina sun yi yaƙi su hana Yahudawa kama ni. Amma fa mulkina daga wani waje ne.” 37Sai Bilatus ya ce, “To, wato, kai sarki ne!” Yesu ya amsa ya ce, “Haka yake, ni sarki ne yadda ka faɗa. Tabbatacce, saboda wannan dalili ne aka haife ni, kuma don wannan ne na zo duniya, domin in shaidi gaskiya. Duk wanda yake gefen gaskiya yakan saurare ni.” 38Bilatus ya tambaye shi ya ce, “Mece ce gaskiya?” Da ya faɗi haka, sai ya sāke fitowa wurin Yahudawa ya ce, “Ni fa ban sami wani abin zargi game da shi ba. 39Amma fa kuna da wata al’ada in lokacin Bikin Ƙetarewa ya yi, nakan sakar muku da ɗan kurkuku ɗaya. To, kuna so in sakar muku ‘sarkin Yahudawa’?” 40Sai suka ɗau kururuwa suna cewa, “Kai, ba shi ba! A ba mu Barabbas!” To, Barabbas ɗin nan yana da hannu dumu-dumu a wani tawaye. 19:1Sa’an nan Bilatus ya tafi da Yesu ya kuma sa aka yi masa bulala. 2Sai sojojin suka tuƙa rawanin ƙaya suka sa masa a kā, suka kuma yafa masa wata riga mai ruwan shunayya. 3Suka yi ta zuwa wurinsa suna cewa, “Ranka yă daɗe, sarkin Yahudawa!” Suna ta marinsa a fuska. 4Bilatus kuwa ya sāke fitowa ya ce wa Yahudawa, “Ga shi, zan fito muku da shi don ku san cewa ban same shi da wani abin zargi ba.” 5Sa’ad da Yesu ya fito sanye da rawanin ƙayar da kuma riga mai ruwan shunayya, sai Bilatus ya ce musu, “Ga mutumin!” 6Nan da nan da manyan firistoci da ma’aikatansu suka gan shi, sai suka yi ihu suka ce, “A gicciye! A gicciye!” Amma Bilatus ya amsa ya ce, “Ku, ku ɗauke shi ku gicciye. Ni dai ban same shi da wani abin zargi ba.” 7Yahudawa dai suka nace suna cewa, “Mu fa muna da doka, kuma bisa ga dokar dole yă mutu domin ya mai da kansa Ɗan Allah.” 8Da Bilatus ya ji haka, sai tsoro ya ƙara kama shi, 9sai ya sāke koma cikin fada. Ya tambayi Yesu, “Daga ina ka fito?” Amma Yesu bai amsa masa ba. 10Bilatus ya ce, “Ba za ka yi mini magana ba? Ba ka san cewa ina da ikon sakinka, ko gicciye ka ba?” 11Yesu ya amsa ya ce, “Ba ka da wani iko a kaina, in ba a ba ka daga sama ba. Saboda haka wanda ya bashe ni gare ka, ya fi na zunubi.” 12Daga nan fa, Bilatus ya yi nemi yă saki Yesu, sai dai Yahudawa suka yi ta ihu suna cewa, “In ka saki wannan mutum, kai ba abokin Kaisar ba ne. Duk wanda ya ɗauka kansa a matsayin sarki, ai, yana gāba da Kaisar ne.” 13Da Bilatus ya ji haka, sai ya fito da Yesu, ya kuma zauna a kujerar shari’ar da ake ce da shi Daɓen Dutse (wanda a harshen Arameyik ana ce da shi Gabbata). 14Ranar Shirye-shiryen Makon Bikin Ƙetarewa ce kuwa, wajen sa’a ta shida. Sai Bilatus ya ce wa Yahudawa, “Ga sarkinku.” 15Amma suka yi ihu suka ce, “A yi da shi! A yi da shi! A gicciye shi!” Bilatus ya ce, “A! In gicciye sarkinku?” Sai manyan firistoci suka amsa suka ce, “Mu dai, ba mu da wani sarki sai Kaisar.” 16A ƙarshe Bilatus ya ba da shi gare su a gicciye shi. Saboda haka sojoji suka tafi da Yesu. 17Ɗauke da gicciyensa, ya kuwa fita zuwa wurin Ƙoƙon Kai (wanda a harshen Arameya ana ce da shi Golgota). 18Nan suka gicciye shi tare da waɗansu mutum biyu, ɗaya a kowane gefe da Yesu a tsakiya. 19Bilatus ya sa aka rubuta wata sanarwa aka kafa a kan gicciyen. Abin da aka rubuta kuwa shi ne, Yesu Banazare, Sarkin Yahudawa. 20Yahudawa da yawa suka karanta wannan sanarwa, gama inda aka gicciye Yesu yana kusa da birni. An kuwa rubuta sanarwar da Arameyanci, Romanci da kuma Girik. 21Sai manyan firistocin Yahudawa suka ce, “A’a! Kada ka rubuta, ‘Sarkin Yahudawa,’ ka dai rubuta, wannan mutum ya ce shi sarkin Yahudawa ne.” 22Bilatus ya amsa ya ce, “Abin da na rubuta, na rubuta.” 23Da sojojin suka gicciye Yesu, sai suka ɗibi tufafinsa suka kasa kashi huɗu, kowanne ya ɗauki kashi ɗaya. Suka kuma ɗauki taguwarsa, taguwar kuwa ba ɗinki, saƙa ɗaya ce gudanta daga sama har ƙasa. 24Sai suka ce wa juna, “Kada mu yage ta, sai dai mu jefa ƙuri’a a kanta mu ga wanda zai ci.” Wannan ya faru ne don a cika nassin da ya ce, “Suka rarraba tufafina a junansu, suka kuma jefa ƙuri’a a kan rigata.” Abin da sojojin suka yi ke nan. 25To, tsaye kusa da gicciyen Yesu kuwa akwai mahaifiyarsa, tare da ’yar’uwar mahaifiyarsa, Maryamu matar Kilofas, da kuma Maryamu Magdalin. 26Sa’ad da Yesu ya ga mahaifiyarsa a can, da kuma almajirin nan da yake ƙauna tsaye kusa, sai ya ce wa mahaifiyarsa, “Mace, ga ɗanki,” 27ga almajirin kuwa ya ce, “Ga mahaifiyarka.” Tun daga wannan lokaci fa almajirin nan ya kai ta gidansa. 28Bayan haka, sanin cewa an cika kome, kuma domin a cika Nassi, sai Yesu ya ce, “Ina jin ƙishirwa.” 29To, akwai wani tulun ruwan tsami ajiye a can, saboda haka suka jiƙa soso da shi, suka soka soson a sandan itacen hizzob, suka kai bakin Yesu. 30Da ya tsotsi abin sha ɗin, sai Yesu ya ce, “An gama.” Da wannan fa, ya sunkuyar da kansa ya saki ruhunsa. 31To, ranan nan fa, ranar Shirye-shirye ce, kashegari kuma muhimmin Asabbaci ne. Domin Yahudawa ba sa so a bar jikunan a kan gicciyoyi a Asabbaci, sai suka roƙi Bilatus a kakkarye ƙafafunsu kuma sauko da jikunan. 32Sai sojoji suka zo suka karya ƙafafun mutum na farko da aka gicciye tare da Yesu, da kuma na ɗayan. 33Amma sa’ad da suka zo kan Yesu suka tarar ya riga ya mutu, ba su karya ƙafafunsa ba. 34A maimako, sai ɗaya daga cikin sojojin ya soki Yesu a gefe da māshi, nan take jini da ruwa suka fito. 35Mutumin da ya gani ɗin shi ya ba da shaida, shaidarsa kuwa gaskiya ce. Ya san gaskiya yake faɗa, yana kuma ba da shaidar domin ku ma ku gaskata. 36Waɗannan abubuwa sun faru don a cika Nassi ne cewa, “Ba ko ɗaya daga cikin ƙasusuwansa da za a karya,” 37kuma kamar yadda wani Nassi ya ce, “Za su dubi wanda suka soka.” 38Bayan haka, Yusuf mutumin Arimateya ya roƙi Bilatus a ba shi jikin Yesu. Yusuf dai almajirin Yesu ne, amma a ɓoye domin yana tsoron Yahudawa. Da izinin Bilatus, ya zo ya ɗauki jikin. 39Yana tare da Nikodimus, wannan da ya taɓa zuwa wurin Yesu da dare. Nikodimus ya zo da mur da aloyes a gauraye, wajen awo ɗari. 40Da ɗaukowar jikin Yesu, sai su biyun suka nannaɗe shi tare da kayan ƙanshi a cikin ƙyallayen lilin bisa ga al’adar Yahudawa ta jana’iza. 41A inda aka gicciye Yesu, akwai wani lambu, a cikin lambun kuwa akwai sabon kabari, wanda ba a taɓa sa kowa ba. 42Da yake ranan nan, ranar Shirye-shirye ce ta Yahudawa, kabarin kuma yana kusa, sai suka binne Yesu a can.
Mattiyu
1Bayan ranar Asabbaci, da sassafe, a ranar farko ta mako, Maryamu Magdalin tare da ɗaya Maryamun, suka je don su ga kabarin. 2Sai aka yi wata babbar girgizar ƙasa. Don wani mala’ikan Ubangiji ya sauka daga sama, ya je kabarin, ya gungurar da dutsen, ya kuma zauna a kai. 3Kamanninsa yana kama da walƙiya, tufafinsa kuma fari fat kamar dusan ƙanƙara. 4Masu gadin kabarin kuma suka ji tsoro ƙwarai, suka yi rawan jiki, suka zama kamar matattu. 5Mala’ikan ya ce wa matan, “Kada ku ji tsoro, domin na san cewa kuna neman Yesu wanda aka gicciye ne. 6Ai, ba ya nan, ya tashi kamar yadda ya faɗa. Ku zo ku ga inda ya kwanta. 7Sai ku tafi da sauri ku gaya wa almajiransa cewa, ‘Ya tashi daga matattu, ya kuma ya sha gabanku zuwa Galili. Can za ku gan shi.’ Ga shi na faɗa muku.” 8Sai matan suka bar kabarin da hanzari, da tsoro, sai dai cike da farin ciki, suka tafi a guje don su gaya wa almajiransa. 9Kwaram, sai ga Yesu ya gamu da su ya ce, “Gaisuwa.” Sai suka zo kusa da shi, suka rungumi ƙafafunsa, suka yi masa sujada. 10Sai Yesu ya ce musu, “Kada ku ji tsoro, ku tafi ku gaya wa ’yan’uwana, su tafi Galili. A can za su gan ni.”
Markus
1Da Asabbaci ya wuce, sai Maryamu Magdalin, Maryamu mahaifiyar Yaƙub, da kuma Salome suka sayi kayan ƙanshi domin su je su shafa wa jikin Yesu. 2A ranar farko ta mako, da sassafe, bayan fitowar rana, suna kan hanyarsu zuwa kabarin ke nan, 3sai suka tambaye juna suka ce, “Wane ne zai gungura mana dutsen daga bakin kabarin?” 4Amma da suka ɗaga kai, sai suka ga cewa, an riga an gungura dutsen. Dutsen kuwa babba ne. 5Da suna shiga cikin kabarin, sai suka ga wani saurayi sanye da farar riga, yana zaune a hannun dama, sai suka firgita. 6Ya ce, “Kada ku firgita. Kuna neman Yesu Banazare wanda aka gicciye ne. Ya tashi! Ba ya nan. Ku dubi inda aka kwantar da shi. 7Amma ku tafi ku gaya wa almajiransa da kuma Bitrus cewa, ‘Ya sha gabanku zuwa Galili. Can za ku gan shi, kamar yadda ya faɗa muku.’ ” 8Da rawan jiki da kuma ruɗewa, matan suka fita a guje daga kabarin. Ba su kuwa gaya wa kowa ba, don suna tsoro.
Luka
1Da sassafe a ranar farko ta mako, matan suka je kabarin, da kayan ƙanshin da suka shirya. 2Suka iske an riga an gungurar da dutsen daga bakin kabarin. 3Amma da suka shiga ciki, ba su iske jikin Ubangiji Yesu ba. 4Yayinda suna cikin tunani a kan wannan, nan take, ga waɗansu mutum biyu tsaye kusa da su, sanye da kaya masu ƙyalli, kamar walƙiya. 5A cikin tsoro, matan suka fāɗi da fuskokinsu a ƙasa, amma mutanen suka ce musu, “Me ya sa kuke neman mai rai a cikin matattu? 6Ba ya nan, ya tashi! Ku tuna yadda ya gaya muku tun yana tare da ku a Galili cewa, 7‘Dole a ba da Ɗan Mutum ga hannun masu zunubi, a kuma gicciye shi, a rana ta uku kuma a tashe shi.’ ” 8Sai suka tuna da maganarsa. 9Da suka dawo daga kabarin, sai suka faɗa wa Sha Ɗayan nan da sauransu, dukan waɗannan abubuwa. 10Matan da suka gaya wa manzannin waɗannan abubuwa su ne, Maryamu Magdalin, da Yowanna, da Maryamu uwar Yaƙub, da waɗansu da suke tare da su. 11Amma ba su gaskata matan ba, domin sun ɗauki kalmominsu wani zancen banza ne. 12Duk da haka, Bitrus ya tashi a guje zuwa kabarin. Da ya sunkuya, sai ya ga ƙyallayen lilin kaɗai a kwance. Sai ya koma yana tunani a ransa, a kan abin da ya faru.
Yohanna
1Da sassafe a ranar farko ta mako, tun da sauran duhu, Maryamu Magdalin ta tafi kabarin ta kuwa tarar an kawar da dutsen daga bakin kabarin. 2Sai ta zo da gudu wajen Siman Bitrus da ɗayan almajirin, wanda Yesu yake ƙauna, ta ce, “Sun ɗauke Ubangiji daga kabarin, ba mu kuma san inda suka sa shi ba!” 3Sai Bitrus da almajirin nan suka nufi kabarin. 4Dukansu biyu suna gudu, amma ɗayan almajirin ya tsere wa Bitrus ya kuma fara kai kabarin. 5Ya sunkuya ya duba ciki ya ga ƙyallayen lilin ne kwance a can amma bai shiga ba. 6Sa’an nan Siman Bitrus, wanda yake bayansa, ya iso ya kuwa wuce cikin kabarin. Ya ga ƙyallayen lilin kwance a can, 7haka ma zanen binnewar da aka naɗe kan Yesu da shi. Zanen a naɗe yake shi kaɗai, a keɓe da lilin ɗin. 8A ƙarshe sai almajirin nan, wanda ya kai kabarin da farko, shi ma ya shiga. Ya gani ya kuma gaskata. 9(Har yanzu ba su fahimci Nassin nan da ya ce lalle ne Yesu yă tashi daga matattu ba.) 10Sai almajiran suka koma zuwa inda suke zama. 11Maryamu kuwa ta tsaya a bakin kabarin daga waje tana kuka. Da tana cikin kuka, sai ta sunkuya ta leƙa cikin kabarin, 12sai ta ga waɗansu mala’iku biyu saye da fararen tufafi, zaune a inda dā gawar Yesu take, ɗaya wajen kai ɗayan kuma wajen ƙafafu. 13Suka tambaye ta cewa, “Mace, don me kike kuka?” Ta ce, “Sun ɗauke Ubangijina, ban kuma san inda suka ajiye shi ba.” 14Da ta faɗin haka, sai ta juya ta ga Yesu tsaye, sai dai ba tă gane cewa Yesu ne ba. 15Sai ya ce, “Mace, don me kike kuka? Wa kike nema?” Ta yi tsammani shi ne mai aikin lambun, sai ta ce, “Ranka yă daɗe, in kai ne ka ɗauke shi, gaya mini inda ka ajiye shi, in je in ɗauke shi.” 16Yesu ya ce mata, “Maryamu.” Sai ta juya wajensa ta ɗaga murya ta ce da Arameyanci, “ Rabboni!” (Wanda yake nufin “Malam”). 17Yesu ya ce, “Kada ki riƙe ni, gama ban riga na koma wajen Uba tukuna ba. A maimako, ki tafi wajen ’yan’uwana ki gaya musu, ‘Ina komawa wajen Ubana da Ubanku, wajen Allahna da kuma Allahnku.’ ” 18Sai Maryamu Magdalin ta wajen almajiran da labari cewa, “Na ga Ubangiji!” Ta kuma gaya musu cewa ya faɗa mata waɗannan abubuwa.
Mako Mai Tsarki
Ku bi abubuwan da suka faru sa’a bayan sa’a, yadda Littattafan Bishara suka faɗa.
Lahadin Dabino
- a cikin yiniranar da al’ada ta saShiga Urushalima
Yesu ya shiga birnin a kan jaki; taron mutane suka tarbe shi da rassan dabino.
Litinin na Mako Mai Tsarki · Babbar Litinin
- a cikin yinilokacin da rubutun ya ambataTsabtace haikali
Yesu ya kori ’yan kasuwa daga haikali. A Markus wannan ya faru kashegarin shigarsa.
Talata na Mako Mai Tsarki · Babbar Talata
- a cikin yinilokacin da rubutun ya ambataKoyarwa a haikali
Muhawara da malaman dokoki da Farisiyawa, misalai, da jawabin da ya yi a Dutsen Zaitun game da ƙarshen zamani.
Laraba na Mako Mai Tsarki · Babbar Laraba
- a cikin yinilokacin da rubutun ya ambataShafawa a Betani
Wata mace ta zuba turare mai ƙanshi a kan Yesu; Yahuda ya yarda ya bashe shi. Markus ya sa wannan kwana biyu kafin Bikin Ƙetarewa.
Alhamis Mai Tsarki · Babbar Alhamis
- 19:00–21:30lokacin da rubutun ya ambataJibin Ƙarshe
Da yamma Yesu ya ci abincin Bikin Ƙetarewa tare da Sha Biyun, ya wanke musu ƙafafu, ya kuma gutsuttsura burodi.
- 21:30–23:00lokacin da rubutun ya ambataJawabin bankwana
Kalmomin ƙarshe na Yesu ga almajiransa da addu’arsa dominsu.
- 23:00–00:30lokacin da rubutun ya ambataGetsemane
Da dare Yesu ya yi addu’a a cikin lambu, almajiran kuwa suna barci.
Juma’a Mai Tsarki · Babbar Juma’a
- 00:30–01:30lokacin da rubutun ya ambataKama Yesu
Yahuda ya zo tare da masu gadi, aka kuma tafi da Yesu.
- 01:30–05:30lokacin da rubutun ya ambataA gaban babban firist
Shari’a da dare. Bitrus ya yi mūsun saninsa sau uku, zakara kuma ya yi cara.
- 05:30–06:30lokacin da rubutun ya ambataMajalisa da safe
Da wayewar gari dattawa suka yanke shawara su miƙa Yesu ga Bilatus.
- 06:30–09:00lokacin da rubutun ya ambataA gaban Bilatus
Bilatus da Hiridus sun yi wa Yesu tambayoyi. Taron mutane suka zaɓi Barabbas, aka kuma yi wa Yesu bulala.
- 09:00–12:00 · Sa’a ta ukulokacin da rubutun ya ambataGicciyewa
Wajen ƙarfe 9 na safe (Markus 15:25). A Yohanna, shari’ar tana ci gaba har wajen sa’a ta shida (Yohanna 19:14); masu fassarar Littafi suna bayyana wannan ta hanyoyi dabam-dabam.
- 12:00–15:00 · Sa’a ta shidalokacin da rubutun ya ambataDuhu bisa ƙasar
Daga sa’a ta shida har zuwa ta tara, wato kusan daga ƙarfe 12 na rana zuwa ƙarfe 3 na yamma, duhu ya rufe ƙasar.
- 15:00–17:00 · Sa’a ta taralokacin da rubutun ya ambataMutuwa a kan gicciye
Wajen ƙarfe 3 na yamma Yesu ya yi kira da murya mai ƙarfi, ya ja numfashinsa na ƙarshe.
- 17:00–19:00lokacin da rubutun ya ambataBinnewa
Da yamma, kafin Asabbaci ya fara, Yusuf daga Arimateya ya sa jikin a cikin kabari.
Asabar Mai Tsarki · Babbar Asabar
- a cikin yinilokacin da rubutun ya ambataAsabbaci
Matan da suka zo tare da Yesu daga Galili suka huta bisa ga doka; aka sa masu gadi a kabarin.
Lahadin Ista · Ista
- 05:00–08:00lokacin da rubutun ya ambataTashin daga matattu
Da sassafe, da wayewar gari, matan suka je kabarin suka tarar babu kowa a ciki.
- 15:00–18:00lokacin da rubutun ya ambataHanyar Emmawus
Almajirai biyu suna tafiya zuwa Emmawus. Ubangiji da ya tashi daga matattu ya yi tafiya tare da su, da yamma kuma suka gane shi.
- 18:00–21:00lokacin da rubutun ya ambataYesu ya bayyana ga almajiransa
Da yammar wannan rana Yesu ya zo wurin almajiransa, ko da yake ƙofofi suna a kulle.
A zane-zane
Jibin ƘarsheUgolino da Siena · kusan 1325
Gicciyewa tare da Budurwa Maryamu, Waliyi Yohanna, Waliyi Jerome da Waliya Maryamu MagdalinPerugino · kusan 1482/1485
An Nuna Kiristi ga Jama’a (Ecce Homo)Sodoma · kusan 1540–49
Binne KiristiRubens · kusan 1612
Kiristi Ya Bayyana ga Maryamu Magdalin a Matsayin Mai Lambu (Noli me Tangere)Masu aiki na Rubens · kusan 1615–1618
Cin Amanar KiristiJacob Jordaens · 1655–1659
Shigar Kiristi UrushalimaDürer · kusan 1509/1510?
Kiristi Yana Wanke Ƙafafun AlmajiraiGarofalo · kusan 1520/1525
Kiristi Yana Ɗauke da GicciyeEl Greco · kusan 1577–87
Tashin KiristiBenvenuto di Giovanni · 1491?
Shigar UrushalimaGustave Doré · 1866
Jibin ƘarsheGustave Doré · 1866
Wasu bukukuwa
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi