Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Shahararrun ayoyin Littafi Mai Tsarki › Zabura 150

Ayar Littafi Mai Tsarki · SRK

Zabura 150

1Yabi Ubangiji. Yabi Allah a cikin wurinsa mai tsarki; yabe shi a cikin sammai na ikonsa.

2Yabe shi saboda ayyukansa masu iko; yabe shi saboda mafificin girmansa.

3Yabe shi da ƙarar kakaki, yabe shi da garaya da molo,

4yabe shi da ganga kuna taka rawa, yabe shi da kayan kiɗi na tsirkiya kuna kuma busa,

5yabe shi da kuge mai ƙara, yabe shi da kuge masu ƙara sosai.

6Bari kowane abu mai numfashi yă yabi Ubangiji. Yabi Ubangiji.

Karanta dukan babin: Zabura 150

Da Turanci

Berean Standard BiblePsalm 150Hallelujah! Praise God in His sanctuary. Praise Him in His mighty heavens. Praise Him for His mighty acts; praise Him for His excellent greatness. Praise Him with the sound of the horn; praise Him with the harp and lyre. Praise Him with tambourine and dancing; praise Him with strings and flute. Praise Him with clashing cymbals; praise Him with resounding cymbals. Let everything that has breath praise the LORD! Hallelujah!

Nassoshi masu alaƙa

Sassan da masu karatu suka fi danganta wa da wannan.

Zab 145:21Bakina zai yi magana cikin yabon Ubangiji. Bari kowace halitta ta yabi sunansa mai tsarki har abada abadin.
R Yoh 5:13Sa’an nan na ji kowace halitta a sama da ƙasa da ƙarƙashin ƙasa da kuma bisan teku, da kome da yake cikinsu yana rerawa, “Gare shi mai zama a kan kursiyin da kuma ga Ɗan Ragon yabo da girma da ɗaukaka da iko, sun tabbata har abada abadin!”
Zab 103:22Yabi Ubangiji, dukanku ayyukansa ko’ina a mulkinsa. Yabi Ubangiji, ya raina.
Zab 145:10Dukan abubuwan da ka yi za su yabe ka, ya Ubangiji; tsarkakanka za su ɗaukaka ka.
Zab 148:7–11Yabi Ubangiji daga duniya, ku manyan halittun teku da kuma dukan zurfafan teku, walƙiya da ƙanƙara, dusar ƙanƙara da gizagizai, hadirin iskar da suke biyayya da umarnansa, ku duwatsu da dukan tuddai, itatuwa masu ’ya’ya da dukan al’ul, namun jeji da dukan dabbobin gida, ƙanana halittu da tsuntsaye masu firiya, sarakunan duniya da dukan al’ummai, ku sarakuna da dukan masu mulkin duniya,
Zab 149:1Yabi Ubangiji. Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji, yabonsa a cikin taron tsarkaka.
Zab 134:2Ku tā da hannuwanku a cikin wurinsa mai tsarki ku kuma yabi Ubangiji.
M Sh 3:24“Ya Ubangiji Mai Iko Duka, ka fara nuna wa bawanka ɗaukakarka da ikonka. Akwai wani allah a sama ko a duniya, wanda zai aikata waɗannan manyan ayyukan kamar ka?

Tushe: OpenBible.info, CC BY 4.0 · Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi