Gida › Shahararrun ayoyin Littafi Mai Tsarki › 2 Tessalonikawa 3:10
Ayar Littafi Mai Tsarki · SRK
2 Tessalonikawa 3:10
Ko ma a sa’ad da muke tare da ku, mun ba ku wannan umarni cewa, “In mutum ya ƙi yin aiki, kada a ba shi abinci.”
Karanta dukan babin: 2 Tessalonikawa 3
A cikin mahallinsa
7Gama ku kanku kun san yadda ya kamata ku bi gurbinmu. Ba mu yi zaman banza sa’ad da muke tare da ku ba,
8ba mu kuwa ci abincin kowa ba tare da ba mu biya ba. A maimakon haka, mun yi aiki dare da rana, muna fama muna wahala kuma don kada mu nawaita wa waninku.
9Mun yi wannan, ba don ba mu da ’yancin karɓar irin taimakon nan ba ne, sai dai domin mu zama gurbin da za ku bi.
10Ko ma a sa’ad da muke tare da ku, mun ba ku wannan umarni cewa, “In mutum ya ƙi yin aiki, kada a ba shi abinci.”
11Mun ji cewa waɗansunku suna zaman banza. Ba sa aikin kome; sai shisshigi kurum.
12Irin waɗannan mutane muna ba da umarni muna kuma gargaɗe su cikin Ubangiji Yesu Kiristi su natsu su kuma nemi abincin da suke ci.
13Game da ku kuma ’yan’uwa, kada ku gaji da yin abin da yake daidai.
Da Turanci
For even while we were with you, we gave you this command: “If anyone is unwilling to work, he shall not eat.”Nassoshi masu alaƙa
Sassan da masu karatu suka fi danganta wa da wannan.
Da zuffan goshinka za ka ci abincinka har ka koma ga ƙasa, da yake daga cikinta aka yi ka. Gama kai turɓaya ne, kuma ga turɓaya za ka koma.”Ku mai da wannan burinku na yi natsattsiyar rayuwa, kuna mai da hankali ga sha’anin da yake gabanku, kuna kuma yin aiki da hannuwanku, kamar dai yadda muka gaya muku,Rago ya ƙosa ya sami wani abu ainun amma ba ya samun kome, amma sha’awar mai aiki tuƙuru yakan ƙoshi sosai.Rago ba ya noma a lokacin noma; saboda haka a lokacin girbi ba ya bukata samun kome.Marmarin rago zai zama mutuwarsa, domin hannuwansa sun ƙi su yi aiki.Na wuce cikin gonar rago, na wuce cikin gonar inabin mutumin da ba shi da azanci; ƙayayyuwa sun yi girma ko’ina, ciyayi sun rufe ƙasar, katangar duwatsu duk ta rushe. Na yi tunani a zuciyata na kuwa koyi darasi daga abin da na gani. Ɗan barci, ɗan gyangyaɗi, ɗan naɗin hannuwa don a huta, sai talauci ya shigo maka kamar ’yan fashi rashi kuma ya zo maka kamar mai hari.Tushe: OpenBible.info, CC BY 4.0 · Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi