Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Shahararrun ayoyin Littafi Mai Tsarki › Zabura 37:4

Ayar Littafi Mai Tsarki · SRK

Zabura 37:4

Ka ji daɗinka a cikin Ubangiji zai kuwa biya bukatun zuciyarka.

Karanta dukan babin: Zabura 37

A cikin mahallinsa

1Ta Dawuda. Kada ka tsorata saboda mugayen mutane ko ka yi kishin waɗanda suka aikata mugunta;

2gama kamar ciyawa za su bushe, kamar ɗanyun ganyaye za su mutu.

3Ka dogara ga Ubangiji ka kuma aikata alheri; yi zama cikin ƙasar ka kuma more makiyaya mai lafiya.

4Ka ji daɗinka a cikin Ubangiji zai kuwa biya bukatun zuciyarka.

5Ka sa kanka a hanyar Ubangiji; ka kuma dogara gare shi zai kuwa yi wannan.

6Zai sa adalcinka yă haskaka kamar hasken safiya, gaskiyarka kuma kamar rana a tsaka.

7Ka natsu a gaban Ubangiji ka kuma jira da haƙuri gare shi; kada ka tsorata sa’ad da mutane ke nasara a hanyoyinsu, sa’ad da suke aikata mugayen shirye-shiryensu.

Zabura 37

Da Turanci

Berean Standard BiblePsalm 37:4Delight yourself in the LORD, and He will give you the desires of your heart.

Nassoshi masu alaƙa

Sassan da masu karatu suka fi danganta wa da wannan.

Yoh 15:7In kun kasance a cikina kalmomina kuma suka kasance a cikinku, ku roƙi kome da kuke so, za a kuwa ba ku.
Zab 145:19Yakan cika sha’awar waɗanda suke tsoronsa; yakan ji kukansu yă kuma cece su.
Yoh 15:16Ba ku kuka zaɓe ni ba, a’a, ni ne na zaɓe ku na kuma naɗa ku ku je ku ba da ’ya’ya-’ya’yan da za su dawwama. Uba kuwa zai ba ku duk abin da kuka roƙa cikin sunana.
Ish 58:14sa’an nan za ku yi farin ciki a cikin Ubangiji, zan kuma sa ku a kan maɗaukaka ƙasashe ku kuma yi biki a gādon mahaifinku Yaƙub.” Ni Ubangiji ne na faɗa.
1Yoh 5:14–15Wannan shi ne ƙarfin halin da muke da shi sa’ad da muke zuwa a gaban Allah, gama mun san cewa kome muka roƙa bisa ga nufinsa, yakan saurare mu. In kuwa muka san cewa yana sauraranmu, ko mene ne muka roƙa, mun sani, mun riga mun sami abin da muka roƙa daga gare shi ke nan.
Zab 21:1–2Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Ya Ubangiji, sarki yana farin ciki cikin ƙarfinka. Yana farin cikinsa ƙwarai cikin nasarorin da ka ba shi! Ka biya masa bukatar zuciyarsa ba ka kuwa hana masa roƙon da ya yi da leɓunansa ba. Sela
Ayu 22:26Ba shakka a lokacin ne za ka sami farin ciki daga wurin Maɗaukaki, ku kuma ɗaga idanunku ga Allah
1Bit 1:8Ko da yake ba ku taɓa ganinsa ba, kuna ƙaunarsa; kuma ko da yake ba kwa ganinsa yanzu, kun gaskata shi, kun kuma cika da farin ciki ƙwarai, wanda ya fi gaban faɗi,

Tushe: OpenBible.info, CC BY 4.0 · Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi