Bible Explorer

Gida › Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce › Yabo da sujada

Bangaskiya

Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da Yabo da sujada

Ayoyin da masu karatu suka fi komawa gare su don wannan jigo (10), an ambace su gaba ɗaya daga Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa.

Ish 61:3in tanada wa waɗanda suke baƙin ciki a Sihiyona, in maido musu rawani mai kyau a maimako na toka, man murna a maimako na makoki, da kuma rigar yabo a maimako na ruhun fid da zuciya. Za a ce da su itatuwan oak na adalci, shukin Ubangiji don bayyana darajarsa.
Zab 150:6Bari kowane abu mai numfashi yă yabi Ubangiji. Yabi Ubangiji.
Ibr 13:15Saboda haka, ta wurin Yesu, bari mu ci gaba da miƙa hadaya ta yabo ga Allah, yabon leɓuna da yake shaidar sunansa.
Yoh 4:24Allah ruhu ne, masu yi masa sujada kuwa dole su yi masa sujada a ruhu, da gaskiya kuma.”
Zab 150:2Yabe shi saboda ayyukansa masu iko; yabe shi saboda mafificin girmansa.
Yoh 4:23Duk da haka, lokaci yana zuwa har ma ya riga ya yi, da masu sujada na gaskiya za su yi wa Uba sujada a Ruhu da kuma gaskiya, gama irin waɗannan masu sujada ne Uba yake nema.
Zab 106:1Yabi Ubangiji. Yi godiya ga Ubangiji, gama nagari ne shi; ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.
Zab 99:3Bari mu yabi girmanka da sunanka mai banrazana, shi mai tsarki ne.
Zab 71:8Bakina ya cika da yabonka, ina furta darajarka dukan yini.
Zab 109:30Da bakina zan ɗaukaka Ubangiji sosai; cikin babban taro zan yabe shi.

Waɗannan ayoyi ne da masu karatu suka fi komawa a wannan batu — ba koyarwa a kansa ba. Karanta kowanne a cikin surarsa.

Tushe

Ayoyin kowane jigo da tsarinsu: bayanan jigogi na OpenBible.info, bisa ƙuri’un masu karatu: OpenBible.info · CC BY 4.0

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.