Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Shahararrun ayoyin Littafi Mai Tsarki › Zabura 1

Ayar Littafi Mai Tsarki · SRK

Zabura 1

1Mai farin ciki ne mutumin da ba ya aiki da shawarar mugaye ko yă yi abin da masu zunubi suke yi ko yă zauna tare da masu yin ba’a.

2Amma yana jin daɗin bin dokar Ubangiji, kuma yana ta nazarinta dare da rana.

3Yana kama da itacen da aka shuka kusa da maɓulɓulan ruwa, wanda yake ba da amfani a daidai lokaci wanda kuma ganyensa ba sa bushewa. Duk abin da yake yi, yakan yi nasara.

4Ba haka yake da mugaye ba! Su kamar yayi ne da iska take kwashewa.

5Saboda haka mugaye ba za su iya tsayawa a shari’a ba, balle a sami masu zunubi a taron adalai.

6Gama Ubangiji yana lura da yadda adalai suke yin abubuwa, amma ayyukan mugaye za su kai su ga hallaka.

Karanta dukan babin: Zabura 1

Da Turanci

Berean Standard BiblePsalm 1Blessed is the man who does not walk in the counsel of the wicked, or set foot on the path of sinners, or sit in the seat of mockers. But his delight is in the Law of the LORD, and on His law he meditates day and night. He is like a tree planted by streams of water, yielding its fruit in season, whose leaf does not wither, and who prospers in all he does. Not so the wicked! For they are like chaff driven off by the wind. Therefore the wicked will not stand in the judgment, nor sinners in the assembly of the righteous. For the LORD guards the path of the righteous, but the way of the wicked will perish.

Nassoshi masu alaƙa

Sassan da masu karatu suka fi danganta wa da wannan.

Zab 26:4–5Ba na zama tare da masu ruɗu, ko in yi tarayya da masu riya; na ƙi jinin taron masu aikata mugunta na ƙi in zauna tare da mugaye.
K Mag 4:14–15Kada ka sa ƙafa a kan hanyar mugaye kada ka bi gurbin mugaye. Ka guji mugunta, kada ka yi tafiya a kanta; juya daga gare ta ka yi tafiyarka.
Irm 17:8Za su zama kamar itacen da aka dasa kusa da ruwa wanda ya miƙa saiwoyinsa zuwa cikin rafi. Ba ya jin tsoro sa’ad da zafi ya zo; ganyayensa kullum kore suke. Ba shi da damuwa a shekarar fări ba ya taɓa fasa ba da ’ya’ya.”
K Mag 13:20Shi da yake tafiya tare da masu hikima yakan ƙaru da hikima, amma abokin wawaye zai yi fama da lahani.
Zab 119:1–2Albarka ta tabbata ga waɗanda rayuwarsu ba ta da abin zargi, waɗanda suke tafiya bisa ga dokar Ubangiji. Albarka ta tabbata ga waɗanda suke kiyaye ƙa’idodinsa suke kuma nemansa da dukan zuciyarsu.
Irm 15:17Ban taɓa zauna a cikin ’yan tawaye ba, ban taɓa yi murna da su ba; na zauna ni kaɗai domin hannunka yana a kaina ka kuma sa na cika da haushi.
Mat 7:13–14“Ku shiga ta matsattsiyar ƙofa. Gama ƙofar zuwa hallaka faɗaɗɗiya ce mai sauƙin bi kuma, masu shiga ta cikinta kuwa suna da yawa. Amma ƙofar zuwa rai, ƙarama ce matsattsiya kuma, masu samunta kuwa kaɗan ne.
Luk 11:28Yesu ya amsa ya ce, “A maimakon, masu albarka ne waɗanda suke jin maganar Allah, suna kuma biyayya da ita.”

Tushe: OpenBible.info, CC BY 4.0 · Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi