Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Shahararrun ayoyin Littafi Mai Tsarki › Zabura 119:105

Ayar Littafi Mai Tsarki · SRK

Zabura 119:105

Maganarka fitila ce ga ƙafafuna haske kuma a kan hanyata.

Karanta dukan babin: Zabura 119

A cikin mahallinsa

102Ban rabu da dokokinka ba, gama kai da kanka ne ka koya mini.

103Ɗanɗanon maganarka akwai zaki, sun ma fi zuma zaki a bakina!

104Na sami ganewa daga farillanka; saboda haka ina ƙin kowace hanyar da ba daidai ba.

105Maganarka fitila ce ga ƙafafuna haske kuma a kan hanyata.

106Na yi rantsuwa na kuma tabbatar da shi, cewa zan bi dokokinka masu adalci.

107Na sha wahala sosai; ka kiyaye raina, ya Ubangiji, bisa ga maganarka.

108Ka karɓi yabon bakina da nake yi da yardar rai, ya Ubangiji, ka kuwa koya mini dokokinka.

Zabura 119

Da Turanci

Berean Standard BiblePsalm 119:105Your word is a lamp to my feet and a light to my path.

Nassoshi masu alaƙa

Sassan da masu karatu suka fi danganta wa da wannan.

K Mag 6:23Gama waɗannan umarnai fitila ne, wannan koyarwa haske ne, kuma gyare-gyaren horo hanyar rayuwa ce,
Zab 43:3Ka aiko da haskenka da gaskiyarka, bari su bishe ni bari su kawo ni ga dutsenka mai tsarki, zuwa wurin da kake zama.
Zab 18:28Kai Ya Ubangiji, ka sa fitilata ta yi ta ci; Allahna ya mai da duhu ya zama haske.
2Bit 1:19Muna kuwa da maganar annabawa da aka ƙara tabbatar mana, zai fi kyau in kuka lura da ita, kamar hasken da yake haskakawa a wuri mai duhu, har yă zuwa wayewar gari da kuma haskakawar tauraron asubahi a zukatanku.
Ayu 29:3lokacin da fitilarsa take haske a kaina na yi tafiya cikin duhu tare da haskensa.
Zab 19:8Ƙa’idodin Ubangiji daidai ne, suna ba da farin ciki ga zuciya. Umarnan Ubangiji haske ne suna ba da haske ga idanu.
Afi 5:13Duk abin da aka kawo a gaban haske ana iya ganinsa, kuma duk abin da aka haskaka yakan zama haske.

Tushe: OpenBible.info, CC BY 4.0 · Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi