Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Shahararrun ayoyin Littafi Mai Tsarki › Zabura 139:13–16

Ayar Littafi Mai Tsarki · SRK

Zabura 139:13–16

13Gama ka halicci ciki-cikina; ka gina ni gaba ɗaya a cikin mahaifar mahaifiyata.

14Ina yabonka domin yadda ka yi ni abin tsoro ne da kuma abin mamaki; ayyukanka suna da banmamaki, na san da haka sosai.

15Ƙasusuwana ba a ɓoye suke a gare ka ba sa’ad da aka yi ni asirce. Sa’ad da saƙa ni gaba ɗaya a zurfafan duniya.

16Idanunka sun ga jikina marar fasali; dukan kwanakin da aka tsara mini a rubuce suke a littafinka kafin ɗayansu yă kasance.

Karanta dukan babin: Zabura 139

A cikin mahallinsa

10can ma hannunka zai bishe ni, hannunka na dama zai riƙe ni gam.

11In na ce, “Tabbatacce duhu zai ɓoye ni haske kuma zai zama dare kewaye da ni,”

12duhu ma ba zai zama duhu gare ka ba; dare zai haskaka kamar rana, gama duhu ya yi kamar haske gare ka.

13Gama ka halicci ciki-cikina; ka gina ni gaba ɗaya a cikin mahaifar mahaifiyata.

14Ina yabonka domin yadda ka yi ni abin tsoro ne da kuma abin mamaki; ayyukanka suna da banmamaki, na san da haka sosai.

15Ƙasusuwana ba a ɓoye suke a gare ka ba sa’ad da aka yi ni asirce. Sa’ad da saƙa ni gaba ɗaya a zurfafan duniya.

16Idanunka sun ga jikina marar fasali; dukan kwanakin da aka tsara mini a rubuce suke a littafinka kafin ɗayansu yă kasance.

17Tunaninka suna da daraja gare ni, ya Allah! Yawansu ba su da iyaka!

18A ce zan iya ƙirgansu, za su fi yashin teku yawa. Sa’ad da na farka, ina nan tare da kai har yanzu.

19Da kawai za ka kashe mugaye, ya Allah! Ku rabu da ni, ku masu kisankai!

Zabura 139

Da Turanci

Berean Standard BiblePsalm 139:13–16For You formed my inmost being; You knit me together in my mother’s womb. I praise You, for I am fearfully and wonderfully made. Marvelous are Your works, and I know this very well. My frame was not hidden from You when I was made in secret, when I was woven together in the depths of the earth. Your eyes saw my unformed body; all my days were written in Your book and ordained for me before one of them came to be.

Nassoshi masu alaƙa

Sassan da masu karatu suka fi danganta wa da wannan.

Far 1:26–27Sa’an nan Allah ya ce, “Bari mu yi mutum cikin siffarmu, cikin kamanninmu, bari kuma su yi mulki a bisa kifin teku, tsuntsayen sama, da kuma dabbobi, su yi mulki a bisa dukan duniya, da kuma a bisa dukan halittu, da masu rarrafe a ƙasa.” Saboda haka Allah ya halicci mutum cikin siffarsa. Cikin kamannin Allah, Allah ya halicci mutum. Miji da mace ya halicce su.
Irm 1:5“Kafin in siffanta ka a cikin ciki na san ka, kafin a haife ka, na keɓe ka; na naɗa ka ka zama annabi ga al’ummai.”
Zab 111:2Ayyukan Ubangiji da girma suke; dukan waɗanda suke farin ciki da su suna tunaninsu.
Zab 104:24Ina misalin yawan aikinka, ya Ubangiji! Cikin hikima ka yi su duka; duniya ta cika da halittunka.
Zab 119:73Hannuwanka ne suka yi suka kuma siffanta ni; ka ba ni ganewa don in koyi umarnanka.
Ish 44:2Ga abin da Ubangiji yana cewa, shi wanda ya yi ka, wanda ya siffanta ka a cikin mahaifa, wanda kuma zai taimake ka. Kada ka ji tsoro, ya Yaƙub, bawana, Yeshurun, wanda na zaɓa.
Zab 92:4–5Gama ka sa na yi murna ta wurin ayyukanka, ya Ubangiji; na rera don farin ciki saboda ayyukan hannuwanka. Ina misalin ayyukanka, ya Ubangiji, tunaninka da zurfi suke ƙwarai!
Ayu 31:15Shi wanda ya yi ni a cikin uwata ba shi ne ya yi su ba? Ba shi ne ya yi mu a cikin uwayenmu ba?

Tushe: OpenBible.info, CC BY 4.0 · Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi