Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Shahararrun ayoyin Littafi Mai Tsarki › Zabura 34:17–20

Ayar Littafi Mai Tsarki · SRK

Zabura 34:17–20

17Adalai kan yi kuka, Ubangiji kuwa yakan ji su; yakan cece su daga dukan wahalarsu.

18Ubangiji yana kusa da waɗanda suka karai ya kuma cece waɗanda aka ragargaza a ruhu.

19Adali zai iya kasance da wahala da yawa, amma Ubangiji yakan cece shi daga dukansu;

20yakan tsare dukan ƙasusuwansa, ba ko ɗayansu da zai karye.

Karanta dukan babin: Zabura 34

A cikin mahallinsa

14Juyo daga mugunta ku yi alheri; nemi salama ku kuma yi ƙoƙarin samunta.

15Idanun Ubangiji suna a kan masu adalci kuma kunnuwansa suna sauraran kukansu;

16fuskar Ubangiji yana gāba da waɗanda suke aikata mugunta, don yă sa a manta da su a duniya.

17Adalai kan yi kuka, Ubangiji kuwa yakan ji su; yakan cece su daga dukan wahalarsu.

18Ubangiji yana kusa da waɗanda suka karai ya kuma cece waɗanda aka ragargaza a ruhu.

19Adali zai iya kasance da wahala da yawa, amma Ubangiji yakan cece shi daga dukansu;

20yakan tsare dukan ƙasusuwansa, ba ko ɗayansu da zai karye.

21Mugunta zai kashe mugu; za a hukunta abokan gāban adalai.

22Ubangiji yakan cece bayinsa; ba wanda yake neman mafaka a wurinsa da za a hukunta.

Zabura 34

Da Turanci

Berean Standard BiblePsalm 34:17–20The righteous cry out, and the LORD hears; He delivers them from all their troubles. The LORD is near to the brokenhearted; He saves the contrite in spirit. Many are the afflictions of the righteous, but the LORD delivers him from them all. He protects all his bones; not one of them will be broken.

An ambace shi a Sabon Alkawari

Yoh 19:36Waɗannan abubuwa sun faru don a cika Nassi ne cewa, “Ba ko ɗaya daga cikin ƙasusuwansa da za a karya,”

Nassoshi masu alaƙa

Sassan da masu karatu suka fi danganta wa da wannan.

Zab 147:3Ya warkar da masu raunanar zuciya ya ɗaɗɗaura miyakunsu.
Zab 145:18Ubangiji yana kusa da kowa da ya kira gare shi, ga duk wanda ya kira gare shi cikin gaskiya.
Ish 57:15Gama abin da Maɗaukaki da kuma Mai daraja ya faɗa wanda yake raye har abada, wanda sunansa mai tsarki ne, “Ina zama a bisa da kuma a tsattsarkan wuri, amma kuma tare da shi wanda yake mai halin tuba mai tawali’u a ruhu, don in farfaɗo da ruhu mai tawali’u in kuma farfaɗo da zuciyar mai halin tuba.
Ish 61:1Ruhun Ubangiji Mai Iko Duka yana a kaina, domin Ubangiji ya shafe ni domin in yi wa’azi labari mai daɗi ga matalauta. Ya aiko ni in warkar da waɗanda suka karai a zuci, don in yi shelar ’yanci don ɗaurarru in kuma kunce ’yan kurkuku daga duhu
Zab 51:17Hadayun Allah su ne karyayyen ruhu; karyayyiya da kuma zuciya mai tuba, Ya Allah, ba za ka ƙi ba.
1Bit 4:12–13Abokaina ƙaunatattu, kada ku yi mamakin gwaji mai tsananin da kuke sha, sai ka ce wani baƙon abu ne yake faruwa da ku. Sai dai ku yi murna cewa kuna tarayya cikin shan wahalolin Kiristi, domin ku kai ga farin ciki mai yawa sa’ad da aka bayyana ɗaukakarsa.
Ezk 36:26Zan ba ku sabuwa zuciya in kuma sa sabon ruhu a cikinku; zan fid da zuciyar dutse in kuma ba ku zuciyar nama.
Zab 34:6Wannan matalauci ya yi kira, Ubangiji kuwa ya ji shi; ya cece shi daga dukan wahalarsa.

Tushe: OpenBible.info, CC BY 4.0 · Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi