Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Shahararrun ayoyin Littafi Mai Tsarki › Zabura 147:3

Ayar Littafi Mai Tsarki · SRK

Zabura 147:3

Ya warkar da masu raunanar zuciya ya ɗaɗɗaura miyakunsu.

Karanta dukan babin: Zabura 147

A cikin mahallinsa

1Yabi Ubangiji. Yana da kyau a rera yabai ga Allahnmu, abu mai daɗi ne daidai ne kuma a yabe shi!

2Ubangiji ya gina Urushalima; ya tattara kamammu na Isra’ilan da aka kai bauta.

3Ya warkar da masu raunanar zuciya ya ɗaɗɗaura miyakunsu.

4Ya lissafta yawan taurari ya kuma kira kowannensu da suna.

5Shugabanmu mai girma ne mai iko duka; ganewarsa ba shi da iyaka.

6Ubangiji yana kula da masu sauƙinkai yakan yar da mugaye a ƙasa.

Zabura 147

Da Turanci

Berean Standard BiblePsalm 147:3He heals the brokenhearted and binds up their wounds.

Nassoshi masu alaƙa

Sassan da masu karatu suka fi danganta wa da wannan.

Zab 34:18Ubangiji yana kusa da waɗanda suka karai ya kuma cece waɗanda aka ragargaza a ruhu.
Ayu 5:18Ko da yake yana sa ciwo, shi ne kuma yake warkar da ciwon; ciwon da ya ji maka, shi da kansa zai warkar da shi.
Irm 33:6“ ‘Duk da haka, zan kawo lafiya da warkarwa gare ta; zan warkar da mutanena in kuma wadata su da salama da zama lafiya.
Ish 61:1Ruhun Ubangiji Mai Iko Duka yana a kaina, domin Ubangiji ya shafe ni domin in yi wa’azi labari mai daɗi ga matalauta. Ya aiko ni in warkar da waɗanda suka karai a zuci, don in yi shelar ’yanci don ɗaurarru in kuma kunce ’yan kurkuku daga duhu
Luk 4:18“Ruhun Ubangiji yana kaina, domin ya shafe ni, in yi wa matalauta wa’azin bishara. Ya aiko ni in yi shelar ’yanci ga ’yan kurkuku, in kuma buɗe idanun makafi, in ba da ’yanci ga waɗanda aka danne.
Hos 6:1–2“Ku zo, mu koma ga Ubangiji. Ya yayyage mu kucu-kucu amma zai warkar da mu; ya ji mana ciwo amma zai daure mana miyakunmu. Bayan kwana biyu zai rayar da mu, a rana ta uku zai tashe mu, don mu rayu a gabansa.
Zab 51:17Hadayun Allah su ne karyayyen ruhu; karyayyiya da kuma zuciya mai tuba, Ya Allah, ba za ka ƙi ba.
Ish 57:15Gama abin da Maɗaukaki da kuma Mai daraja ya faɗa wanda yake raye har abada, wanda sunansa mai tsarki ne, “Ina zama a bisa da kuma a tsattsarkan wuri, amma kuma tare da shi wanda yake mai halin tuba mai tawali’u a ruhu, don in farfaɗo da ruhu mai tawali’u in kuma farfaɗo da zuciyar mai halin tuba.

Tushe: OpenBible.info, CC BY 4.0 · Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi