Bincika › Littattafan Bishara gefe da gefe › Mafari
Littattafan Bishara gefe da gefe · Mafari
Yesu ya fara wa’azi a Galili
Mat 4:12–17 · Mar 1:14–15 · Luk 4:14–15
Mat 4:12–1712Da Yesu ya ji labari cewa an kulle Yohanna a kurkuku, sai ya koma zuwa Galili.
13Ya bar Nazaret, ya je ya zauna a Kafarnahum, wadda take a bakin tafki wajen Zebulun da Naftali
14don a cika abin da aka faɗa ta bakin annabi Ishaya cewa,
15“Ƙasar Zebulun da ƙasar Naftali, da kuke a hanyar zuwa tekun Galili, a ƙetaren Urdun, wannan yankin Galili ta Al’ummai,
16mutanen da suke zama cikin duhu sun ga babban haske; haske kuma ya haskaka a kan waɗanda suke zama a inuwar mutuwa.”
17Tun daga wannan lokaci, Yesu ya fara wa’azi yana cewa, “Ku tuba, gama mulkin sama ya yi kusa.”
Mar 1:14–1514Bayan da aka sa Yohanna a kurkuku, sai Yesu ya shigo cikin Galili, yana shelar bisharar Allah.
15Yana cewa, “Lokaci ya yi. Mulkin Allah ya yi kusa. Ku tuba, ku gaskata bishara!”
Luk 4:14–1514Yesu ya koma Galili cikin ikon Ruhu. Labarinsa kuwa ya bazu ko’ina a ƙauyuka.
15Ya yi ta koyarwa a majami’unsu, kowa kuwa ya yabe shi.
An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY