Bible Explorer

Bincika › Littattafan Bishara gefe da gefe › Mafari

Littattafan Bishara gefe da gefe · Mafari

Gwajin Yesu a hamada

Mat 4:1–11 · Mar 1:12–13 · Luk 4:1–13

Mattiyu

Mat 4:1–11

1Sa’an nan Ruhu ya kai Yesu cikin hamada don Iblis yă gwada shi.

2Bayan ya yi azumi yini arba’in da kuma dare arba’in, sai ya ji yunwa.

3Sai mai gwajin ya zo wurinsa ya ce, “In kai Ɗan Allah ne, ka ce wa duwatsun nan su zama burodi.”

4Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake cewa, ‘Ba da abinci kaɗai mutum yake rayuwa ba, sai dai da kowace kalmar da take fitowa daga bakin Allah.’ ”

5Sai Iblis ya kai shi birni mai tsarki, ya kai shi can wuri mafi tsayi duka na haikali.

6Ya ce, “In kai Ɗan Allah ne, yi tsalle ka sauka ƙasa. Gama a rubuce yake, “ ‘Zai umarci mala’ikunsa game da kai, za su tallafe ka da hannuwansu, don kada ka buga ƙafarka a kan dutse.’”

7Yesu ya amsa masa ya ce, “A rubuce yake kuma cewa, ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’ ”

8Har wa yau, Iblis ya kai shi bisa wani dutse mai tsawo sosai, ya nunnuna masa dukan mulkokin duniya da darajarsu.

9Ya ce, “Zan ba ka dukan wannan, in za ka durƙusa ka yi mini sujada.”

10Sai Yesu ya ce masa, “Rabu da ni, Shaiɗan! Gama a rubuce yake, ‘Yi wa Ubangiji Allahnka sujada, shi kaɗai kuma za ka bauta wa.’ ”

11Sa’an nan Iblis ya bar shi, mala’iku kuwa suka zo suka yi masa hidima.

Markus

Mar 1:12–13

12Nan da nan, sai Ruhu ya kai shi cikin hamada,

13ya kuma kasance a hamada kwana arba’in, Shaiɗan yana gwada shi. Yana tare da namomin jeji, mala’iku kuma suka yi masa hidima.

Luka

Luk 4:1–13

1Yesu kuwa cike da Ruhu Mai Tsarki, ya dawo daga Urdun, Ruhu kuma ya kai shi cikin hamada,

2inda kwana arba’in, Iblis ya gwada shi. Bai ci kome ba a cikin kwanakin nan, a ƙarshensu kuwa ya ji yunwa.

3Iblis ya ce masa, “In kai Ɗan Allah ne, ka faɗa wa wannan dutse yă zama burodi.”

4Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake, ‘Ba da abinci kaɗai mutum zai rayu ba.’ ”

5Iblis ya kai shi can kan wani wuri mai tsawo, ya nunnuna masa a ƙyiftawar ido dukan mulkokin duniya.

6Ya ce masa, “Zan ba ka dukan ikonsu da darajarsu, gama ni aka danƙa wa, kuma zan bai wa duk wanda na ga dama.

7Saboda haka in ka yi mini sujada, dukan wannan zai zama naka.”

8Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake, ‘Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, kuma shi kaɗai za ka bauta wa.’ ”

9Sai Iblis, ya kai shi Urushalima ya sa ya tsaya a kan wuri mafi tsayi na haikali ya ce, “In kai Ɗan Allah ne, ka yi tsalle daga nan zuwa ƙasa.

10Gama a rubuce yake, “ ‘Zai umarci mala’ikunsa game da kai, su kiyaye ka da kyau;

11za su tallafe ka da hannuwansu, don kada ka buga ƙafarka a kan dutse.’”

12Yesu ya amsa ya ce, “An ce, ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’ ”

13Da Iblis ya gama dukan wannan gwajin, ya bar shi sai lokacin da wata dama ta samu.

An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY