Bible Explorer

Bincika › Littattafan Bishara gefe da gefe › A Urushalima

Littattafan Bishara gefe da gefe · A Urushalima

Darasi daga itacen ɓaure

Mat 24:32–35 · Mar 13:28–31 · Luk 21:29–33

Mattiyu

Mat 24:32–35

32“Yanzu fa, sai ku koyi wannan darasi daga itacen ɓaure. Da zarar rassansa suka yi taushi ganyayensa kuma suka toho, kun san damina ta kusa.

33Haka kuma, sa’ad da kun ga dukan waɗannan abubuwa, ku sani ya yi kusan zuwa, yana ma dab da bakin ƙofa.

34Gaskiya nake gaya muku, wannan zamani ba zai shuɗe ba sai dukan abubuwan nan sun faru.

35Sama da ƙasa za su shuɗe, amma maganata ba za tă taɓa shuɗe ba.

Markus

Mar 13:28–31

28“To, sai ku yi koyi da itacen ɓaure. Da zarar rassansa suka yi taushi, ganyayensa kuma suka toho, kun san cewa damina ta yi kusa ke nan.

29Haka ma, in kuka ga waɗannan abubuwa suna faruwa, ku san cewa ya yi kusan zuwa, yana ma dab da bakin ƙofa.

30Gaskiya nake gaya muku, zamanin nan ba zai shuɗe ba sai duk abubuwan nan sun faru.

31Sama da ƙasa za su shuɗe, amma kalmomina ba za su taɓa shuɗewa ba.

Luka

Luk 21:29–33

29Sai ya gaya musu wannan misali ya ce, “Ku dubi itacen ɓaure da dukan itatuwa.

30A duk lokacin da sun fara fitar da ganye, za ku gani da kanku, ku san cewa, damina ta yi kusa.

31Haka ma, in kuka ga waɗannan abubuwa suna faruwa, ku sani mulkin Allah ya yi kusa.

32“Gaskiya nake gaya muku, ba shakka, wannan zamani ba zai shuɗe ba, sai dukan waɗannan abubuwa sun cika.

33Sama da ƙasa za su shuɗe, amma kalmomina ba za su taɓa shuɗewa ba.

An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY