Bible Explorer

Bincika › Littattafan Bishara gefe da gefe › A Urushalima

Littattafan Bishara gefe da gefe · A Urushalima

Zuwan Ɗan Mutum

Mat 24:29–31 · Mar 13:24–27 · Luk 21:25–28

Mattiyu

Mat 24:29–31

29“Nan da nan bayan tsabar wahalan nan “ ‘sai a duhunta rana, wata kuma ba zai ba da haskensa ba; taurari kuma za su fāffāɗi daga sararin sama, za a kuma girgiza abubuwan sararin sama.’

30“A sa’an nan ne alamar dawowar Ɗan Mutum zai bayyana a sararin sama, dukan al’umman duniya kuwa za su yi kuka. Za su ga Ɗan Mutum yana zuwa kan gizagizan sararin sama, da iko da kuma ɗaukaka mai girma.

31Zai kuwa aiki mala’ikunsa su busa ƙaho mai ƙara sosai, za su kuwa tattaro zaɓaɓɓunsa daga kusurwoyi huɗun nan, daga wannan bangon duniya zuwa wancan.

Markus

Mar 13:24–27

24“Amma waɗancan kwanaki, bayan baƙin azaban nan, “ ‘rana za tă yi duhu, wata kuma ba zai ba da haskensa ba;

25taurari za su fāffāɗo daga sararin sama. Za a kuma girgiza manyan abubuwan da suke a sararin sama.’

26“Sa’an nan, mutane za su ga Ɗan Mutum yana zuwa cikin gizagizai da iko, da ɗaukaka mai girma.

27Zai kuma aiko mala’ikunsa su tattaro zaɓaɓɓunsa daga kusurwoyi huɗun nan, daga iyakar duniya har yă zuwa iyakar sama.

Luka

Luk 21:25–28

25“Za a yi alamu a cikin rana, da cikin wata, da cikin taurari. A duniya, al’ummai za su yi baƙin ciki, su kuma rikice don tsoro, saboda ruri da kuma tafasar teku.

26Mutane za su suma don tsoro, za su kuma yi fargaba, a kan abin da yake zuwa a bisan duniya, gama za a girgiza duniyar taurarin sararin sama.

27A lokacin ne za su ga Ɗan Mutum yana zuwa cikin girgije, da iko, da ɗaukaka mai girma.

28Sa’ad da waɗannan abubuwa sun fara faruwa, ku tashi tsaye, ku ɗaga kawunanku, domin fansarku yana matsowa kusa.”

An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY