Bincika › Littattafan Bishara gefe da gefe › Shan wahalar Yesu
Littattafan Bishara gefe da gefe · Shan wahalar Yesu
Makircin kashe Yesu
Mat 26:1–5 · Mar 14:1–2 · Luk 22:1–2
Mat 26:1–51Sa’ad da Yesu ya gama faɗin dukan waɗannan abubuwa, sai ya ce wa almajiransa,
2“Kamar yadda kuka sani, Bikin Ƙetarewa sauran kwana biyu, za a kuma ba da Ɗan Mutum don a gicciye shi.”
3Sai manyan firistoci da dattawan mutane, suka taru a fadan babban firist, mai suna Kayifas,
4suka ƙulla shawara su kama Yesu da makirci, su kuma kashe shi.
5Suka ce, “Amma ba a lokacin Biki ba, don kada mutane su tā da rikici.”
Mar 14:1–21To, saura kwana biyu ne kaɗai a yi Bikin Ƙetarewa da Bikin Burodi Marar Yisti, sai manyan firistoci da malaman dokoki, suka nemi wani dalili su kama Yesu a ɓoye, su kashe.
2Suka ce, “Ba a lokacin Biki ba, don kada mutane su yi tawaye.”
Luk 22:1–21Yanzu fa, Bikin Burodi Marar Yistin da ake kira Bikin Ƙetarewa ya yi kusa,
2manyan firistoci da malaman dokoki kuma suna neman yadda za su kashe Yesu a ɓoye, don suna tsoron mutane.
An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY