Bible Explorer

Bincika › Littattafan Bishara gefe da gefe › Shan wahalar Yesu

Littattafan Bishara gefe da gefe · Shan wahalar Yesu

Ɗayanku zai bashe ni

Mat 26:20–25 · Mar 14:17–21 · Luk 22:21–23 · Yoh 13:21–30

Mattiyu

Mat 26:20–25

20Da yamma ta yi, sai Yesu ya zauna don cin abinci tare da Sha Biyun.

21Yayinda suke cin abinci, sai ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, ɗayanku zai bashe ni.”

22Suka yi baƙin ciki ƙwarai, suka fara ce masa da ɗaya-ɗaya, “Gaskiya nake gaya muku, ɗayanku zai bashe ni.”

23Yesu ya amsa ya ce, “Wanda ya sa hannunsa a kwano tare da ni ne, zai bashe ni.

24Ɗan Mutum zai tafi kamar yadda aka rubuta game da shi. Amma kaiton mutumin da zai bashe Ɗan Mutum! Da ma ba a haifi mutumin nan ba, da ya fi masa.”

25Sa’an nan Yahuda, wanda zai bashe shi ya ce, “Tabbatacce ba ni ba ne, ko, Rabbi?” Yesu ya amsa ya ce, “I, kai ma ka fada.”

Markus

Mar 14:17–21

17Da yamma ta yi, sai Yesu ya zo tare da Sha Biyun.

18Yayinda suke cin abinci a tebur, sai ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, ɗaya daga cikinku zai bashe ni, wani wanda yake ci tare da ni.”

19Suka cika da baƙin ciki, da ɗaya-ɗaya suka ce masa, “Tabbatacce, ba ni ba ne, ko?”

20Ya ce, “Ɗaya daga cikin Sha Biyun ne, wanda yake ci tare da ni a kwano.

21Ɗan Mutum zai tafi kamar yadda yake a rubuce game da shi, amma kaiton mutumin da ya bashe Ɗan Mutum! Zai fi masa, da ba a haife shi ba.”

Luka

Luk 22:21–23

21Amma hannun wanda zai ci amanata, yana cin abincin tare da ni.

22Ɗan Mutum zai mutu kamar yadda aka ƙaddara, amma kaiton mutumin da zai bashe shi.”

23Sai suka fara tambayar junansu, ko wane ne a cikinsu zai yi wannan.

Yohanna

Yoh 13:21–30

21Bayan Yesu ya faɗi haka, sai ya yi juyayi a ruhu, ya kuma furta cewa, “Gaskiya nake gaya muku, ɗayanku zai bashe ni.”

22Almajiransa suka dubi juna, suka rasa ko da wa yake.

23Ɗaya daga cikin almajiran Yesu wanda yake ƙauna kuwa, yana zaune kusa da shi.

24Sai Siman Bitrus ya taɓa wannan almajirin ya ce, “Tambaye shi, wa yake nufi?”

25Shi kuwa da yake jingine kusa da Yesu, ya ce, “Ubangiji, wane ne?”

26Yesu ya amsa ya ce, “Shi ne wanda zan ba shi gutsurin burodin nan sa’ad da na tsoma cikin kwanon.” Da ya tsoma gutsurin burodin, sai ya ba wa Yahuda Iskariyot, ɗan Siman.

27Nan take bayan Yahuda ya karɓi burodin, sai Shaiɗan ya shige shi. Sai Yesu ya ce masa, “Abin nan da kake niyyar yi, ka yi shi maza.”

28Amma ba wani a wurin cin abincin da ya fahimci dalilin da ya sa Yesu ya faɗa masa haka.

29Da yake Yahuda ne ma’aji, waɗansunsu suka ɗauka Yesu yana ce masa yă sayi abin da ake bukata don Bikin ne, ko kuwa yă ba wa matalauta wani abu.

30Nan da nan da Yahuda ya karɓi burodin, sai ya fita. A lokacin kuwa dare ya yi.

An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY