17A rana ta fari ta Bikin Burodi Marar Yisti, sai almajiran suka zo wurin Yesu suka yi tambaya suka ce, “Ina kake so mu je mu shirya maka wurin da za ka ci Bikin Ƙetarewa?”
18Ya amsa ya ce, “Ku shiga gari wurin wāne, ku ce masa, ‘Malam ya ce, lokacina ya yi kusa. Zan ci Bikin Ƙetarewa tare da almajiraina a gidanka.’ ”
19Saboda haka almajiran suka yi yadda Yesu ya umarce su, suka kuwa shirya Bikin Ƙetarewa.