Littafi Mai Tsarki › Zabura › 87
SRK · Babi 87 / 150
Zabura 87
1Na ’ya’yan Kora maza. Zabura ce. Waƙa ce. Ya kafa harsashinsa a kan dutse mai tsarki.
2Ubangiji yana ƙaunar ƙofofin Sihiyona fiye da dukan wuraren zaman Yaƙub.
3Ana faɗin abubuwa masu ɗaukaka game da ke Ya birnin Allah, Sela
4“Zan lissafta Rahab a cikin waɗanda suka san ni, Filistiya ita ma, da Taya, tare da Kush, zan kuma ce, ‘An haifi wannan a Sihiyona.’ ”
5Tabbatacce, game da Sihiyona za a ce, “Wannan da wancan an haifa a cikinta, Mafi Ɗaukaka kansa zai kafa ta.”
6Ubangiji zai rubuta a littafin sunayen mutanensa, “An haifi wannan a Sihiyona.” Sela
7Yayinda suke kaɗe-kaɗe za su rera, “Dukan maɓulɓulaina suna cikinki.”
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (SRK, 2020) · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. (ba a canja rubutu ba; an bar bayanan ƙasa da kanun labarai) · eBible.org