Littafi Mai Tsarki › Zabura › 120
SRK · Babi 120 / 150
Zabura 120
1Waƙar haurawa. Na yi kira ga Ubangiji cikin damuwata, ya kuwa amsa mini.
2Ka cece ni, ya Ubangiji, daga leɓuna masu ƙarya da kuma daga harsuna masu yaudara.
3Me zai yi maka, me kuma ya fi, ya kai harshe mai yaudara?
4Zai hukunta ku da kibiyoyi masu tsini na jarumi, tare da garwashin wuta na itacen tsintsiya.
5Kaitona da nake zama a Meshek, da nake zama a ciki tentunan Kedar!
6Da daɗewa na zauna a cikin waɗanda suke ƙin salama.
7Ni mutum ne mai salama; amma sa’ad da na yi magana, su sai su yi ta yaƙi.
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (SRK, 2020) · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. (ba a canja rubutu ba; an bar bayanan ƙasa da kanun labarai) · eBible.org