Bible Explorer

Littafi Mai Tsarki › Zabura › 122

SRK · Babi 122 / 150

Zabura 122

1Waƙar haurawa. Ta Dawuda. Na yi farin ciki tare da waɗanda suka ce da ni, “Bari mu tafi gidan Ubangiji.”

2Ƙafafunmu suna tsaye a ƙofofinki, ya Urushalima.

3An gina Urushalima kamar birnin da aka yi a harhaɗe wuri guda.

4A can ne kabilu suke haurawa, kabilan Ubangiji, don su yabi sunan Ubangiji bisa ga farillan da aka ba wa Isra’ila.

5A can kursiyoyin shari’a yake tsaye, kursiyoyin gidan Dawuda.

6Ku yi addu’a don salamar Urushalima, “Bari waɗanda suke ƙaunarki su zauna lafiya.

7Bari salama ta kasance a katangarki zaman lafiya kuma a fadodinki.”

8Saboda ’yan’uwana da kuma abokaina, zan ce, “Salama tă kasance tare da ke.”

9Saboda gidan Ubangiji Allahnmu, zan nemi wadatarki.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (SRK, 2020) · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. (ba a canja rubutu ba; an bar bayanan ƙasa da kanun labarai) · eBible.org