Littafi Mai Tsarki › Zabura › 12
SRK · Babi 12 / 150
Zabura 12
1Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi. Bisa ga sheminit. Zabura ta Dawuda. Ka taimaka, Ubangiji, gama masu tsoron Allah ba sa nan kuma; masu aminci sun ɓace daga cikin mutane.
2Kowa yana yi wa maƙwabcinsa ƙarya; zaƙin bakinsu maganar ƙarya ce suna cike da ruɗu a zukatansu.
3Bari Ubangiji yă yanke dukan zaƙin bakinsu da kuma kowane harshe mai fariya,
4masu cewa, “Da harsunanmu za mu yi nasara; leɓunanmu za su kāre mu, wane ne maigidanmu?”
5“Saboda danniyar marasa ƙarfi da kuma nishin masu bukata, zan tashi yanzu,” in ji Ubangiji. “Zan kāre su daga masu yin musu sharri.”
6Kalmomin Ubangiji kuwa ba su da kuskure, kamar azurfan da aka tace cikin matoyan yumɓu, aka tsabtacce sau bakwai.
7Ya Ubangiji, za ka kiyaye mu lafiya ka tsare mu daga irin mutanen nan har abada.
8Mugaye suna yawo a sake sa’ad da ake girmama abin da ba shi da kyau a cikin mutane.
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (SRK, 2020) · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. (ba a canja rubutu ba; an bar bayanan ƙasa da kanun labarai) · eBible.org