Bible Explorer

Littafi Mai Tsarki › Zabura › 61

SRK · Babi 61 / 150

Zabura 61

1Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi masu tsirkiya. Ta Dawuda. Ka ji kukata, ya Allah; ka saurari addu’ata.

2Daga iyakar duniya na yi kira gare ka, na yi kira yayinda zuciyata ta karai; ka bishe ni zuwa dutsen da ya fi ni tsayi.

3Gama kai ne mafakata, hasumiya mai ƙarfi gāba da maƙiyi.

4Ina marmari in zauna a tentinka har abada in sami mafaka a cikin inuwar fikafikanka. Sela

5Gama ka ji alkawarina, ya Allah; ka ba ni gādo na waɗanda suke tsoron sunanka.

6Ka ƙara kwanakin ran sarki, shekarunsa su kasance a zamanai masu yawa.

7Bari yă yi mulki a gaban Allah har abada; ka sa ƙaunarka da amincinka su tsare shi.

8Sa’an nan zan riƙa rera yabo ga sunanka in kuma cika alkawarina kowace rana.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (SRK, 2020) · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. (ba a canja rubutu ba; an bar bayanan ƙasa da kanun labarai) · eBible.org