Littafi Mai Tsarki › Zabura › 131
SRK · Babi 131 / 150
Zabura 131
1Waƙar haurawa. Ta Dawuda. Zuciyata ba mai girman kai ba ce, ya Ubangiji, idanuna ba sa fariya; ban dami kaina da manyan al’amura ba ko abubuwan da suka sha ƙarfina.
2Amma na haƙura na kuma kwantar da raina; kamar yaron da aka yaye tare da mahaifiyarsa, kamar yaron da aka yaye haka raina yake a cikina.
3Ya Isra’ila, sa zuciyarka ga Ubangiji yanzu da har abada kuma.
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (SRK, 2020) · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. (ba a canja rubutu ba; an bar bayanan ƙasa da kanun labarai) · eBible.org