Littafi Mai Tsarki › Zabura › 14
SRK · Babi 14 / 150
Zabura 14
1Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda. Wawaye sukan ce a ransu, “Ba Allah.” Sun lalace, ayyukansu kuwa mugaye ne; babu wani da yake yi abu mai kyau.
2Ubangiji ya duba daga sama a kan ’yan adam don yă ga ko akwai wani da ya gane, wani wanda yake neman Allah.
3Duka sun kauce, duka gaba ɗaya sun zama lalatattu; babu ɗaya wanda yake yin abu mai kyau, ba ko ɗaya.
4Masu aikata mugunta za su taɓa koyo. Suna cin mutane yadda mutane ke cin gurasa kuma waɗanda ba sa kira bisa Ubangiji?
5Ga su, tsoro ya sha kansu, gama Allah yana cikin ƙungiyar adalai.
6Ku masu mugunta kuna sa ƙoƙarin matalauta yă zama banza, amma Ubangiji ne mafakansu.
7Kash, da ceton Isra’ila zai fito daga Sihiyona mana! Sa’ad da Ubangiji zai maido da sa’ar mutanensa, bari Yaƙub yă yi farin ciki Isra’ila kuma yă yi murna!
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (SRK, 2020) · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. (ba a canja rubutu ba; an bar bayanan ƙasa da kanun labarai) · eBible.org