Littafi Mai Tsarki › Zabura › 98
SRK · Babi 98 / 150
Zabura 98
1Zabura ce. Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji, gama ya yi abubuwa masu banmamaki; hannunsa na dama da hannunsa mai tsarki sun yi masa aikin ceto.
2Ubangiji ya sanar da cetonsa ya kuma bayyana adalcinsa ga al’ummai.
3Ya tuna da ƙaunarsa da kuma amincinsa ga gidan Isra’ila; dukan iyakar duniya sun ga ceton Allahnmu.
4Ku yi sowa don farin ciki ga Ubangiji, dukan duniya, ku ɓarke da waƙa ta murna tare da kiɗi;
5ku yi kiɗi ga Ubangiji da garaya, da garaya da ƙarar rerawa,
6tare da bushe-bushe da karar ƙahon rago, ku yi sowa don farin ciki a gaban Ubangiji, Sarki.
7Bari teku su yi ruri, da kuma kome da yake cikinsa, duniya da kuma kome da yake cikinta.
8Bari koguna su tafa hannuwansu, bari duwatsu su rera tare don farin ciki;
9bari su rera a gaban Ubangiji, gama yana zuwa domin yă hukunta duniya. Zai hukunta duniya da adalci mutane kuma cikin gaskiya.
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (SRK, 2020) · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. (ba a canja rubutu ba; an bar bayanan ƙasa da kanun labarai) · eBible.org