Littafi Mai Tsarki › Zabura › 63
SRK · Babi 63 / 150
Zabura 63
1Zabura ta Dawuda. Sa’ad da yake a hamadar Yahuda. Ya Allah, kai ne Allahna, da nacewa na neme ka; raina yana ƙishinka, jikina yana marmarinka, cikin busasshiyar ƙasar da ta zozaye inda babu ruwa.
2Na gan ka a wuri mai tsarki na kuma dubi ikonka da ɗaukakarka.
3Domin ƙaunarka ta fi rai kyau, leɓunana za su ɗaukaka ka.
4Zan yabe ka muddin raina, kuma a cikin sunanka zai ɗaga hannuwana.
5Raina zai ƙoshi kamar da abinci mafi kyau; da leɓunan rerawa bakina zai yabe ka.
6A gadona na tuna da kai; ina tunaninka dukan dare.
7Domin kai ne mai taimakona, ina rera a cikin inuwar fikafikanka.
8Raina ya manne maka; hannunka na dama yana riƙe da ni.
9Su da suke neman raina za su hallaka; za su gangara zuwa zurfafan duniya.
10Za a bayar da su ga takobi su kuma zama abincin karnukan jeji.
11Amma sarki zai yi farin ciki ga Allah; dukan waɗanda suke rantse da sunan Allah za su yabe shi, amma za a rufe bakunan maƙaryata.
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (SRK, 2020) · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. (ba a canja rubutu ba; an bar bayanan ƙasa da kanun labarai) · eBible.org