Bible Explorer

Littafi Mai Tsarki › Zabura › 82

SRK · Babi 82 / 150

Zabura 82

1Zabura ta Asaf. Allah yana shugabanta cikin babban taro; yakan zartar da hukunci a cikin “alloli”.

2“Har yaushe za ku kāre marasa adalci ku kuma goyi bayan mugaye? Sela

3Ku tsare mutuncin marasa ƙarfi da marayu; ku kāre hakkin matalauta da waɗanda ake danniya.

4Ku ceci marasa ƙarfi da masu bukata; ku kuɓutar da su daga hannun mugaye.

5“Ba su san kome ba, ba su fahimci kome ba. Suna yawo cikin duhu; an girgiza dukan tussan duniya.

6“Na ce, ‘Ku “alloli” ne; dukanku ’ya’yan Mafi Ɗaukaka’ ne.

7Amma za ku mutu kamar mutum kurum; za ku fāɗi kamar duk wani mai mulki.”

8Ka tashi, ya Allah, ka shari’anta duniya, gama dukan al’ummai gādonka ne.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (SRK, 2020) · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. (ba a canja rubutu ba; an bar bayanan ƙasa da kanun labarai) · eBible.org