Littafi Mai Tsarki › Zabura › 124
SRK · Babi 124 / 150
Zabura 124
1Waƙar haurawa. Ta Dawuda. Da ba don Ubangiji ya kasance a gefenmu ba, bari Isra’ila yă ce,
2da ba don Ubangiji ya kasance a gefenmu ba sa’ad da aka auka mana,
3sa’ad da fushinsu ya ƙuna a kanmu, ai, da sun haɗiye mu da rai;
4da rigyawa ta kwashe mu, da ambaliya ta rufe mu.
5Da ruwa mai hauka ya share mu ƙaf.
6Yabo ya tabbata ga Ubangiji, wanda bai bari aka yayyage mu da haƙoransu ba.
7Mun tsira kamar tsuntsu daga tarkon mai farauta; an tsinke tarko, muka kuwa tsira.
8Taimakonmu yana a sunan Ubangiji, Wanda ya yi sama da ƙasa.
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (SRK, 2020) · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. (ba a canja rubutu ba; an bar bayanan ƙasa da kanun labarai) · eBible.org