Bincika › Littattafan Bishara gefe da gefe › A Galili
Littattafan Bishara gefe da gefe · A Galili
Mahaifiyar Yesu da ’yan’uwansa
Mat 12:46–50 · Mar 3:31–35 · Luk 8:19–21
Mat 12:46–5046Yayinda Yesu yake cikin magana da taron, sai ga mahaifiyarsa da ’yan’uwansa tsaye a waje, suna so su yi magana da shi.
47Wani ya ce masa, “Mahaifiyarka da ’yan’uwanka suna tsaye a waje, suna so su yi magana da kai.”
48Ya amsa masa ya ce, “Wace ce mahaifiyata, su wane ne kuma ’yan’uwana?”
49Sai ya miƙa hannu wajen almajiransa ya ce, “Ga mahaifiyata da kuma ’yan’uwana.
50Ai, duk wanda yake aikata nufin Ubana wanda yake cikin sama, shi ne ɗan’uwana da ’yar’uwata da kuma mahaifiyata.”
Mar 3:31–3531Sai mahaifiyar Yesu tare da ’yan’uwansa suka iso. Suna tsaye a waje, sai suka aiki wani ciki yă kira shi.
32Taron yana zaune kewaye da shi, sai suka ce masa, “Mahaifiyarka da ’yan’uwanka suna waje, suna nemanka.”
33Ya yi tambaya ya ce, “Su wane ne mahaifiyata, da ’yan’uwana?”
34Sai ya dubi waɗanda suke zaune kewaye da shi ya ce, “Ga mahaifiyata da ’yan’uwana!
35Duk wanda yake aikata nufin Allah, shi ne ɗan’uwana, da ’yar’uwata, da kuma mahaifiyata.”
Luk 8:19–2119Sai uwar Yesu da ’yan’uwansa suka zo, domin su gan shi, amma ba su iya zuwa kusa da shi ba, saboda taron.
20Sai wani ya faɗa masa cewa, “Ga uwarka da ’yan’uwanka suna tsaye a waje suna so su gan ka.”
21Ya amsa ya ce, “Mahaifiyata da ’yan’uwana, su ne waɗanda suke jin maganar Allah, suna kuma aikata ta.”
An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY