Bincika › Littattafan Bishara gefe da gefe › A Galili
Littattafan Bishara gefe da gefe · A Galili
Alamar Yunana
Mat 12:38–42 · Luk 11:29–32
Mat 12:38–4238Sa’an nan waɗansu Farisiyawa da malaman dokoki suka ce masa, “Malam, muna so mu ga wata alama mai banmamaki daga gare ka.”
39Sai ya amsa ya ce, “Mugaye da masu zinan zamanin nan suna neman wata alama mai banmamaki! Amma babu wadda za a nuna musu, sai dai alama ta annabi Yunana.
40Gama kamar yadda Yunana ya yi yini uku da kuma dare uku a cikin wani babban kifi, haka Ɗan Mutum zai yi yini uku da kuma dare uku a cikin ƙasa.
41Mutanen Ninebe za su tashi a ranar shari’a tare da wannan zamani, su kuwa hukunta shi; don sun tuba saboda wa’azin Yunana, yanzu kuwa ga wanda ya fi Yunana girma a nan.
42Sarauniyar Sheba za tă tashi a ranar shari’a tare da wannan zamani, tă kuwa hukunta shi; don ta zo daga ƙarshen duniya, ta saurari hikimar Solomon, yanzu kuwa ga wanda ya fi Solomon girma a nan.
Luk 11:29–3229Da taron mutane suka ƙaru, sai Yesu ya ce, “Wannan mugun zamani ne. Tana neman wani abin banmamaki, amma ba ko ɗaya da za a ba ta, sai dai ta Yunana.
30Kamar yadda Yunana ya zama alama ga mutanen Ninebe, haka ma Ɗan Mutum zai zama ga zamanin nan.
31A ranar shari’a, Sarauniyar Kudu za tă tashi tsaye tare da wannan zamani, ta yanke wa wannan zamani hukunci, domin ta zo daga ƙarshen duniya ta saurari hikimar Solomon, ga shi kuwa, shi wanda ya fi Solomon girma, na nan.
32A ranar shari’a, mutanen Ninebe za su tashi tsaye tare da wannan zamani, su yanke wa wannan zamani hukunci. Gama sun tuba sa’ad da Yunana ya yi musu wa’azi. Ga shi yanzu, shi wanda ya fi Yunana girma, na nan.
An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY