Bible Explorer

Bincika › Littattafan Bishara gefe da gefe › A Galili

Littattafan Bishara gefe da gefe · A Galili

Mutum mai mugun ruhu a majami’a a Kafarnahum

Mar 1:21–28 · Luk 4:31–37

Markus

Mar 1:21–28

21Suka tafi Kafarnahum. Da ranar Asabbaci ta kewayo, sai Yesu ya shiga majami’a ya fara koyarwa.

22Mutane suka yi mamakin koyarwarsa, domin ya koyar da su kamar wanda yake da iko, ba kamar malaman dokoki ba.

23Nan take, sai wani mutum mai mugun ruhu a majami’arsu, ya ɗaga murya ya ce,

24“Ina ruwanka da mu, Yesu Banazare? Ka zo ne don ka hallaka mu? Na san wane ne kai, Mai Tsarki nan na Allah!”

25Yesu ya tsawata masa ya ce, “Yi shiru! Fita daga cikinsa!”

26Sai mugun ruhun ya jijjiga mutumin da ƙarfi, ya fita daga jikinsa da ihu.

27Dukan mutane suka yi mamaki, suna tambayar juna suna cewa, “Mene ne haka? Tabɗi! Yau ga sabuwar koyarwa kuma da iko! Yana ma ba wa mugayen ruhohi umarni, suna kuma yin masa biyayya.”

28Labari game da shi ya bazu nan da nan ko’ina a dukan yankin Galili.

Luka

Luk 4:31–37

31Sai ya tafi Kafarnahum, wani gari a Galili, a ranar Asabbaci kuma, ya fara koya wa mutane.

32Suka yi ta mamakin koyarwarsa, domin saƙonsa yana da iko.

33A cikin majami’ar, akwai wani mutum mai aljani, wani mugun ruhu. Mutumin ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce,

34“Wayyo! Ina ruwanka da mu, Yesu Banazare? Ka zo ne don ka hallaka mu? Na san wane ne kai, Mai Tsarki na Allah!”

35Yesu ya tsawata masa da ƙarfin cewa, “Yi shiru! Ka fita daga cikinsa!” Sai aljanin ya fyaɗa mutumin da ƙasa a gabansu duka, sa’an nan ya fita, ya bar shi ba wani rauni.

36Dukan mutanen suka yi mamaki, suka ce wa junansu, “Wace irin koyarwa ce haka? Da ƙarfi da iko, yana ba wa mugayen ruhohin umarni suna kuma fita!”

37Labarinsa kuwa ya bazu ko’ina a cikin ƙasar.

An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY