Gida › Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce › Tsufa
Rayuwa da aiki
Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da Tsufa
Ayoyin da masu karatu suka fi komawa gare su don wannan jigo (10), an ambace su gaba ɗaya daga Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa.
K Mag 16:31
Furfura rawani ne mai daraja; akan same ta ta wurin yin rayuwa ta adalci.Ish 46:4
Har lokacin da kuka tsufa kuka yi furfura ni ne shi, ni ne shi wanda zai lura da ku. Na yi ku zan kuma riƙe ku; zan lura da ku in kuma kuɓutar da ku.K Mag 20:29
Ɗaukakar matasa maza ita ce ƙarfinsu, furfura ita ce darajar tsofaffi.Fir 19:32
“ ‘Ku miƙe tsaye a gaban tsofaffi, ku nuna bangirma ga waɗanda suka tsufa, ku kuma girmama Allahnku. Ni ne Ubangiji.2Kor 4:16
Saboda haka, ba mu fid da zuciya ba. Ko da yake a waje, jikinmu mai mutuwa yana lalacewa, amma can ciki, ana sabunta mu kowace rana.Ayu 12:12
Ko ba a wurin tsofaffi ake samun hikima ba? Ba tsawon rai yana kawo ganewa ba?Zab 71:18
Ko sa’ad da na tsufa da furfura, kada ka yashe ni, ya Allah, sai na furta ikonka ga tsara mai zuwa, ƙarfinka ga dukan waɗanda suke zuwa.Zab 71:9
Kada ka yar da ni sa’ad da na tsufa; kada ka yashe ni sa’ad da ƙarfina ya ƙare.Zab 92:14
Za su ci gaba da ba da ’ya’ya a tsufansu, za su kasance ɗanye kuma kore shar,K Mag 17:6
Jikoki rawanin tsofaffi ne, kuma iyaye su ne abin taƙamar ’ya’yansu.Waɗannan ayoyi ne da masu karatu suka fi komawa a wannan batu — ba koyarwa a kansa ba. Karanta kowanne a cikin surarsa.
Tushe
Ayoyin kowane jigo da tsarinsu: bayanan jigogi na OpenBible.info, bisa ƙuri’un masu karatu: OpenBible.info · CC BY 4.0
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.