Bible Explorer

Gida › Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce › Yanke shawara

Rayuwa da aiki

Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da Yanke shawara

Ayoyin da masu karatu suka fi komawa gare su don wannan jigo (15), an ambace su gaba ɗaya daga Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa.

K Mag 3:5–6Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka kada kuma ka dangana ga ganewarka; cikin dukan hanyoyinka ka amince da shi, zai kuwa sa hanyoyinka su miƙe.
Yaƙ 1:5In waninku ya rasa hikima, ya kamata yă roƙi Allah, mai bayarwa hannu sake ga kowa ba tare da gori ba, za a kuwa ba shi.
K Mag 11:14Saboda rashin jagora al’umma takan fāɗi, amma masu ba da shawara da yawa kan tabbatar da nasara.
Fil 4:6–7Kada ku damu game da kome sai dai a cikin abu duka, ku gabatar da roƙe-roƙenku ga Allah ta wurin addu’a da roƙo, tare da godiya. Salamar Allah, wadda ta wuce dukan fahimta, za tă tsai da zukatanku da tunaninku cikin Kiristi Yesu.
K Mag 12:15Hanyar wawa daidai take a gare shi, amma mai hikima kan saurari shawara.
K Mag 15:22Shirye-shirye sukan lalace saboda rashin neman shawara, amma tare da mashawarta masu yawa za su yi nasara.
Ish 30:21Ko kun juye dama ko hagu, kunnuwanku za su ji murya a bayanku tana cewa, “Ga hanya; ku yi tafiya a kai.”
Zab 32:8Zan umarce ka in kuma koyar da kai a hanyar da za ka bi; Zan ba ka shawara in kuma lura da kai.
K Mag 18:15Zuciya mai la’akari kan nemi sani; kunnuwan mai hikima kan bincika don yă koya.
K Mag 16:9’Yan Adam sukan yi shirye-shiryensu a zukatansu, amma Ubangiji ne yake da ikon cika matakansa.
Rom 12:2Kada ku ci gaba da yin abin da duniya take yi, sai dai ku bar halinku ya sāke, ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah yake so yake, abu mai kyau, mai daɗi da kuma cikakke.
K Mag 2:6Gama Ubangiji yana ba da hikima, daga bakinsa kuma, sani da ganewa sukan fito.
1Sar 3:9Saboda haka ka ba bawanka zuciyar ganewa, don yă shugabanci mutanenka, yă kuma iya rarrabe tsakanin abin da yake daidai da abin da ba daidai ba. Gama wa zai iya shugabance wannan mutanenka masu girma haka?”
K Mag 16:3Ka miƙa wa Ubangiji dukan abin da kake yi, shirye-shiryenka kuwa za su yi nasara.
K Mag 1:5bari masu hikima su saurara, su kuma ƙara ga saninsu, bari masu tunani kuma su sami jagora,

Waɗannan ayoyi ne da masu karatu suka fi komawa a wannan batu — ba koyarwa a kansa ba. Karanta kowanne a cikin surarsa.

Tushe

Ayoyin kowane jigo da tsarinsu: bayanan jigogi na OpenBible.info, bisa ƙuri’un masu karatu: OpenBible.info · CC BY 4.0

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.