Gida › Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce › Hikima
Rayuwa da aiki
Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da Hikima
Ayoyin da masu karatu suka fi komawa gare su don wannan jigo (10), an ambace su gaba ɗaya daga Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa.
Yaƙ 1:5
In waninku ya rasa hikima, ya kamata yă roƙi Allah, mai bayarwa hannu sake ga kowa ba tare da gori ba, za a kuwa ba shi.K Mag 1:7
Tsoron Ubangiji shi ne masomin ilimi, amma wawaye sun rena hikima da horo.Yaƙ 3:17
Amma hikimar da ta zo daga sama da fari tana da tsabta gaba ɗaya; sa’an nan mai ƙaunar salama ce, mai sanin ya kamata, mai biyayya, cike da jinƙai da aiki mai kyau, marar nuna bambanci, sahihiya kuma.Afi 5:15
Sai ku yi hankali sosai da yadda kuke rayuwa, kada ku zama kamar marasa hikima, sai dai kamar masu hikima.K Mag 2:6
Gama Ubangiji yana ba da hikima, daga bakinsa kuma, sani da ganewa sukan fito.Mat 10:16
“Ina aikan ku kamar tumaki a cikin kyarketai. Saboda haka ku zama masu wayo kamar macizai, kuma marasa ɓarna kamar kurciyoyi.Yaƙ 3:13–14
Wane ne mai hikima da fahimta a cikinku? Bari yă nuna ta ta wurin rayuwarsa mai kyau, ta wurin ayyukan da aka yi cikin tawali’un da suke fitowa daga hikima. Amma in kuna cike da mugun kishi da kuma sonkai a cikin zukatanku, kada ku yi taƙama game da wannan, ko ku danne gaskiya.Zab 111:10
Tsoron Ubangiji ne mafarin hikima; dukan waɗanda suke bin farillansa suna da ganewa mai kyau. Gare shi ne madawwamin yabo.M Had 7:12
Hikima mafaka ce takan kāre mutum kamar yadda kuɗi suke yi. Kiyayewar da hikima takan yi wa mai ita ita ce amfanin ilimi.K Mag 19:20
Ka kasa kunne ga shawara ka kuma yarda da umarni, a ƙarshe kuwa za ka yi hikima.Waɗannan ayoyi ne da masu karatu suka fi komawa a wannan batu — ba koyarwa a kansa ba. Karanta kowanne a cikin surarsa.
Tushe
Ayoyin kowane jigo da tsarinsu: bayanan jigogi na OpenBible.info, bisa ƙuri’un masu karatu: OpenBible.info · CC BY 4.0
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.